← Book details Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 105

Sashe 34

Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Amina suna cigaba da zuwa makarantar su,Sannan tafi zama bangaren Hajiya har Hamida ma tare suke sai suyi sati basu kwana agidan Aba ba suna Shashen Hajiya saboda Hanne sannan ita kanta Mamanmu bata wani Damu ba Amina ba yanzu Duniya ta samu,Daga ita sai Aba ko Jawaad wani Lokacin Wajen su Amina yake kwana ashashen Hajiya Duniya ta samu yanzu Aba bai mata gaddama ko Hajiya da mallam tasha gabansu sai su gama mgana dasu yazo mamanmu na tambayansa zai kwashe ya Fadamata shawara kuma akomai da ita yake sai abunda tace shi yake yi ta kankane komai tana baza buraubanta yadda ta gama Dama shiyasa har Hamidan ba Damuwa da take yi da ita ba yanzu tasan dai lokacin auran su nayi za"a aurar dasu Amina kuma Daman sunan auranta gantali
Ita kanta Aminar tasan Mamanmu ta Rage kula da ita kamar baya sai ta Danganta hakan da yanzu ba Yaya ba su ya Zeenatu Hidima tayi ma mamammu yawa tayi mata uzuri sosai,Su Hajiya kuma basu wani Lura ba saboda basu fiya saka ido ba ko da yaya nada rai Amina da Hamida yan Shashenta ne kowa ya sani shiyasa ko yanzu da suka Tare anan bama wanda ya Damu.
Sannan in Allah zai ikonsa kan wani abu da karesa da kansa sai ya kaudar da Tunanin mutane akan hassashen wani abu to kamar hakane ya Faru da Amina cikin Lokaci kadan gabobinta suka fara girma kirjinta ya fara Cika har yazo ma yafi na Hanne yana neman fin na Hamida sannan Daga kasanta Hips dinta ya Bude ta fara Fashewa kibanta Daga sama ya Fara sai kuma ta Bude ta kasa sannan Fuskarta ta Ciko sosai yawancin kayanta ma sun mata kadan riguna sai da Hajiya ta saka aka kai aka Buda mata itama taga kiban da Amina tayi sai bata kawo komai ba azaton Cin abincin da Amina ke yi saboda cin abincinta ya ninka na baya har Cikin Dare ci take sannan ga shan Tea madara bata sati take karewa Amina hakanan take hambalamta har sata take yi tatafi da ita makaranta.
Har su Hamida sai da suka ce Amina tayi kiba yanzu ko Hamida albarka.
Ita kanta Aminar tana jin Canji Ajikinta ammh bata Damu ba Sai itama take Tunanin cin abincin datake yi shiyasa da kuma kila girman da batayi bane abaya sai yanzu take yi.
Ranar ma suna shiri zasu makaranta da Safe Dakyar Amina ta iya saka Rigarta ta matseta duk da an kara Budeta.
Ta saka tana Nishi kafin tace"ni dai girman nawa bai zo min da Dadi ba..Ku kalle har Tumbi fa na fara..!
Suka bi Cikin nata da kallo kafin su saka Dariya Hamida tace"Kirjinki wlh sun fi nawa..Tumbi kuma wlh gashi nan Hanne..!
Tafada tana Taba cikin Amina Daya Fara tasawaa taji Tauri ta cire Hannunta Tanacfadin"Sai Taurin bala"i..!
Hanne tace"Ke kuwa wannan Abincin Datake narka ai ba Lafiya bane..Dole ta Ijiye Timbi taurinsa kuma Uban Madaran Dake sha ne wlh in baki Daina ba kikayi Kiba Ya Danmallam bazai je dake madina ba domin in kika Hau seleken awon Nauyi aka ga kin yi kiba bamai zuwa Dake..!
Amina ta balla mata Harara tana Fadin"Dama wake son zuwa..?
Dariya suke mata ita kuma tana masifan ita ba inda zata je Daganan suka shashantar da mganar.
Aranar da sukaje gaida mallam kan su tafi makaranta da suka fita yana Tare da Hajiya ne sai da yayi mata mganar Kibar da Amina tayi hajiya tace kila gabobin girman nata basu bayyana ba sai yanzu Shima sai ya yarda da Haka.
Duk wanda ya ganta bai kawo ma kansa wani Tunani sai Tunanin gobobin girma ne suka bayyanan mata Mamanmu kuma bata bi ta kan Amina ballatana ta iya ankarewa da wani abu na Faruwa Anty Amarya kuma sai tayi sati ma bata ga Amina ba in ma ba ta ganta ba, bata ma Tsayawa kare mata kallo balle ta zargi wani abi zai faru.
Ana cikin haka aka fara Biyan kudin jarabawar fita ta su Akilu Hajiya tace a biyama Amina sai maallam yace da Aminar da sa"adatu da Hannatu da Hamida duk a Biya musu su zana a SS2 dinsu da hajiya ta nemi jin Dalili sai ya sanar da ita cewa in Umaru yazo ya tafi da Amina madina su hanne kewa zai musu yawa sannan sun ma isa auran suma da su zauna suna Damuwa da rashin Amina suma zai aurar dasu nan da wattani kadan zasu cigaba da zuwa hadda da islamiya kafin Mazajen nasu su bayyana Hajiya bata yi gaddama ba Tunda daman Jafar da Nasir sun fadamata cewa Karatun SS3 din duk maimaici ne da Reviosion shiyasa sai tayi na"am da mganarsa acikin Satin akaje aka biya musu su shida har da Akilu da Zubairu.
Amina da taji murna kamar me baza"a rabata dasu hanne ba Sa"adatu ne bata so ba,tayi ta kuka Anty Amarya ko ta kanta bata bi ba, abunda ke gabanta yafi karfi wannan iskancin na Sa"adatu.
Allah shi ke batar da Tunaninmu wani Lokaci ga abu a kusa damu sai mu Dade bamu Fahimcesa ba..!

********

Danmaallam achan madina Ko Sarood sai da ta Tausayamai yadda ya kwallafa rai akan cikin Sakina sannan yazo kuma ya tafi Ranar da Mallam ya kirasa ya fadamai da Zazzabi ya kwana,kwanansa biyu agida baya Fita Tana kula dashi,Ita kanta ta Damu sosai sai ta sakamai kuka ganin ya Daina Cin abinci sosai ballatana yawan mgana,da taimakon Mallam da Hajiya da Aliyu ya Dawo daidai da kuma Sarood itama tayi kokarin matuka wajen kula da shi Sosai take basa Tausayi tana da sanyin Hali kamarsa da kuma Hakuri shi kanshi yanzu ya Fara Tunanin mafitan da Aliyu yaso ya Nema tun farko yaki yarda da mganarsa ammh a yanzu yafi Sarood Damuwa Tsausayi take basa ita macece mai Rauni sannan kuma yaji yana Fatan in bai samu Haihuwa ta bangaran Sakina ba,me zai hana ya roki Allah ya basa ta bangaron Sarood Amina dai bai ma saka ta a Lissafinsa ba bai Taba kawo mata Daukan cikinsa nan kusa ba..!..abunda bai sani ba Daman Sau tari Allah yafi bamu abun da muke nema a inda bamu taba Zato ko Tsammani ba..!
Washegari yana cikin makaranta ya kira Aliyu da niyar ya Tuntubesa da mganar sai gashi shima ya fara mai mganar bayan sun gaisa Aliyu ke tambayansa matsalansa da Sarood ya ake ciki..? Yace mai har yanzu ba Sauki domin ko ya jaraba jiya iyau ne.

Aliyu ya kada baki yace"Shehi ni dai kaki jin Shawarata ne..Naso ka kira mallam ka sanar dashi matsalanka kila ya samo maka waraka Tunda yafimu sanin abubuwan da suka Shafi addini da irin wannan banace ka yarda wani yayi maka ba kasa aranka bamai yi sai Allah kuma wajensa kake neman waraka..!
Chapter 34 · 0% Book details