Sashe 11
Tafita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Achan Falon mallam kuwa bayan Fitan Anty Amarya itama Hj.nasara tayi musu sallama ta koma Shashenta ya Rage daga hajiya sai mallam Sai Haj.uwani Dake zaune gefen Hajiya Bisa kujera mai zaman mutum biyu Cikin kissarta data shiga Jikinsu gabadaya domin Hajiya ta yarda da ita Dari Bisa dari hakama mallam.
Sai da ta kalli Hajiya kafin tace"Oh Hajiya wai bawanda zai koma ya Dubomana Amina..?Tunda Suka tafi fa ba wanda yabi bayansu..!
Hajiya batayi yunkurin mgana ba Mallanlm ne ya Murmusa kafin yace"Kamar wasu yara kanana Uwani..?
In ita Amina yarinya ce ai Shi Umaru yana da Hankali na tabbata kuma zai kula da ita..Sannan ai ba ita kadai bace Sakina na tare da ita sannan ko Dazu nan mukayi sallar isha"i dashi kinga kuwa suna nan lafiya..!
Kafin tace wani abu Hajiya ta amshe mganar da cewa"Daman ina da niyyar su hanne su je mata..Na bari ne tayi ko Sati ne ta saba da chan kada su je yanzu ta fara koke koken suma ba Tunani ne dasu ba haka zasu hadu su kara Tada mata hankali..!
Haj.uwani tayi mirmishi kafin tace"Hakane kuma hajiya..ni daman nace ne ko zamu lekata Amina wlh da ita nake kwana araina Tsausayi ta bani Ranar da zasu tafi..!
Mallam yace"Da haka kowa ya saba..kema ai haka kika yi ta kuka ranar da zan taho dake daga Tsafe .!
Har Hajiya gatanan tayi wannan koke kokem ko ba haka ba Hajiya. ?
Hararan wasa hajiya ta sakar mai batayi mgana sukayi Dariya Dukkansu mallam ya cigaba da fadin"Zai koma ma jibin nan..in ya tafi su je su ganta su wunin mata sai taji Dadi..!
Hajiya tace"Eh har kwana ma sai suyi mata..Uwani ai mun girma da zuwa gidan yranmu yanzu sai dai in wani abu ya taso wanda ba"a Fata..!
Haj.uwani ta rausayar dakai kafin tace"Ammh in ya koma nan zai barmana ita ko..?
Hajiya tace"Eh nan zai barta ita da Sakina zasu zauna agidan su..!
Haj.uwani tayi mirmishin jin Dadi kafin tace"to Allah ya zaunar dasu lafiya..!
Gabadaya suka amsa da Ameen basu wani jima ba sukayi mai sallama suka fita,Hj.uwani bata koma Shashenta ba ,shashen Hajiya suka yada Zango suna hira sai hillatan Hajiya take yi tana jin wasu sirrikan saboda ko Mallam bai Fada maata abu ba zata jisa abakin Hajiya harta matakin da Hajiya ta Daukan kan tafiyar Amina madina sai da ta fada mata Hj.uwani tace"Wlh gwara haka hajiya..Yazo ya tafi da matarsa..Ni fa marliya ban yarda da ita ba..so suke su mallake Umar din shi kadai to ta Allah bata su ba..!
Hajiya tace"Ameen da yardan Allah Amina da Danmallam mutu ka raba. !
Aran Haj.uwani sai da tace ba Ameen ba afili kuma ta amsa da Ameen kafin tayi ma Hajiya sallama ta koma Shashenta Cikin Farincikin da sai da ya Bayyana akan Fuskarta
Umaima ta leka ta isketa tayi barci gyara mata Bargo tayi ta fice ta koma Dakinta,Tana shiga tayi wani Shewa lokaci Daya tana Fadin"Cikin ruwan sanyi..Burina zai cika..!
Wayarta ta Dauka Dake saman Mirror ta Kira Batula kanwata tana Dauka ta Sakin mata Shewa tana fadin"Batula albishirinki..!
Dagachan bangaran Batula tace"Goro Uwani Sikari baki farin banza..!
Dariyar Nishadi ta saki kafin tace"Tsarin da muka dora yarinyar nan su Hajiya sun taimaka mana ya tafi Daidai batula..!
Batula tace"kai don Allah..?,Bani na sha..!
Nan uwani ta warware mata komai ta Karishe da fadin"Kinga jibi zai koma kuma sai ya Dau Lokaci kafin ya Dawo..Zuwa kafin ya dawon na riga na Dorata kan Tsarin koda ma zai kulatan watarana kamar Sakinar ce haka ko ta samu zai bi Rariya..!
Batula tace"Dakyau..Hakan yayi kyau sai dai kada ki yi sakaci har adauki wani Lokaci bata hau Tsarin ba kinsan yadda zaki yi ko ta Halin kakane ...Cikin kwanakin nan Namiji fa baka shedarsa..!
Haj.Uwani tace"Naso haka sai dai tunda suka tafi batazo ba..Sannan naso na sakama Hajiya Tunanin muje mu Dubata taki bada Dama..ammh nasan zata zo jibi fa zai tafi Batula wlh ina da Tabbacin Mai mata kamar Sakina da balarabiya bazai kula Amina ba kinganta ne..?
Kwaila ce fa ga kazanta ga rashin Natsuwa ina da tabbacin bazai taba kulata ba..!
Batula tace"Shikenan tunda kina da yakinin haka..Sai dai ina tsoron kada su shammacemu..!
Haj.Uwani tace"Na yarda da aikin Mama..Ba wanda ya isa ya shammaceni Batula sai dai ni na shammacesu kamar yadda na saba..!
Dariya suka saka gabadayanau kafin su cigaba da mganarsu sun manta cewa Allah ne ke zana kaddaran bawa ba Mutum ba,abunda basu sani ba shine Komai da zai faru nan gaba Allah ya riga ya Tsara faruwar hakan Lokacin kawai ake jira.
Tabbas Uwani zata Tsammanci abunda batayi tsammani ba.
Bama ita kadai ba iri irenta ma zasu tsammanci abunda basu taba Tsammani ba..!
Anty Amarya sai da ta chanchara kwalliya,ta fesa turaruka sannan ta koma Shashen mallam cikin gayunta,Mallam bashi a falo yana cikin Bedroom dinsa chan ta Bisa ta iske ya fito wanka kenan ya sauya kaya zuwa saukakkiyar Jallabiya mai ruwan madara furfuran kansa duk yana Waje ne tana shigowa da sallama ya amsa mata yana Binta da kallo Lokaci daya da Mirmishi
Gefen gado ta nemi waje ta zauna tana kallonsa kafin tace"Mallam kayi wanka baka jira ni nazo na tayaka ba..!
Mirmishi yayi mata kafin yace"Na Hutassheki ne marliya..!
Mikewa tayi ta isa garesa ta amshi Man dayake shafawa a Hannunsa ta Lakuto tana tayasa shafawa Lokaci Daya tana fadin"Aikina ne fa..Kada kamin Rowan lada mana mallan..!
Yana kallonta yace"Mun girma marliya wannan aikin duk na Dauke muku yanzu..!
Marairaice masa tayi tana fadin"A"a nidai ban yarda mungirma ba....!
Yana yar dariya yace"Baki yarda mun girma ba..?,To in ke kina da yarintarki ai yunusa kan ya Tsufa..!
Tura bakinta tayi kafin tace"Ni dai wlh Mijina bai Tsufa ba..Yaro ne Danye Sharaf..!
Dukkansu yadda ta fadi mganar yasa sukayi Dariya atare ita ta karishe Shafa mai man suka koma saman gado suka zauna mallam ya mike kafarsa tana shafamai man zafi Saboda sun faramai Tauna kuma aki"da ne duk Dare sai ya shafa yake kwanciya
Tana shafamai suna Hiransu samasama sai da ta gama hillatansa sannan ta kallesa kafin tace"Ni ko mallam yaushe Danmallam zai koma ne..?
Kai tsaye yace mata"Jibi in Allah ya yarda yacemin jiya..!
Kai ta Rausayar kafin tace"Ya sanar dakai nan zai bar Sakina..?
Mallam yayi shuru kafin yace"A"a bai sanar dani ba..!
Anty Amarya ta gyara zama tana fadin"To ni dai baisan me ya faru Tsakaninsu ba..kasan yaran nan su yi ta shirme basa neman shawara ashe sanda zasu taho Bikin su Abida yace ta Zauna achan ta matsa sai tazo Shine fa yace bazai koma da ita ba yanzu..!
Mallam ya yi shuru yana kallonta kafin yace"Haka akayi .?
Anty amarya tace"Eh mallam ita kuma Sakinar ta damu tana ta kirana tan kukan wai na rokesa ya koma da ita bazata iya zama ita kadai ba nidai Fada nayi mata nace Laifinta ne da nace bazan saka Baki bane tace nayi maka mgana don Allah ka Rokesa ya tafi da ita..!
Har ta gama mgama yana Nazarinta Kafin ya sauke ajiyar rai yace"Naji batunki marliya kinsan Allah ni bansan ma duka anyi haka ba..Umaru da na ne ammh bana hirar iyalansa Dashi..Tsakani na dashi Hirar duniya sai kuma ta aiki in ta kama sai kuma ta Rayuwa haka ammh ni bana shiga Sha"anin ya"yana da matansu kinsani marliya..Umaru mijin Sakina ne sannan bansn meya faru Tsakaninsu ba domin ina Mahaifinsa ya gama tsara abunsa sai na kirasa nace masa ya Sauya..kina ganin hakan ba rashin girma bane..? sannan kuma shiga Hurumin da ba nawa bane tunda dai bai Tuntubeni da mganar ba..!
Ya karishe fada yana kallonta itama shi take kallo jikinta yayi sanyi domin taga ba Nasara,girgiza kai tayi cikin sanyin jiki kafin mallam ya cigaba da fadin"To kin gani bai kamata nayi mai mgana ba..Sannan ai ba ita kadai zata Zauna ba ga mamana nan itama nan zai barta sai ya sake dawo wa ki bata Hakuri ta zauna inda mijinta ya ijiyeta..!
Anty Amarya sai ta kasa mgana Shuru kawai tayi,Ganin kamar yanayinta ya Sauya ne yasa Mallam yace"Kiyi hakuri marliya..kema kada ki saka baki wannan ba Hurumin mu bane..!
Da Toh ta amsa mai tana kokarin nuna komai ba komai bane kada mallam ya Fahimci yanayinta..
Washegari ta kira sakina ta lallasheta akan tayi Hakuri da mganar Binsa ta bari in ya koma mallam ya tabbatar mata zai dawo domin ya koma da ita Tunda Sarood bata da wani amfani kamar Hoto take.
Sakina ta yarda ta Hakura ammh tace yana tafiya itama Dutse zata je tayi Sati Daya ta huce daga Bakincikin yadda zata fara zama da Amina agida Daya Matsayin Mijin su daya.
**********