← Book details Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 105

Sashe 94

Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

EDD din Amina har ya tsallake da wajen Sati uku Bata haihu ba Sannan Cikinta ya fita wata na Tara har ya shiga goma sai kuma hankula suka fara tashi ita kanta Aminar ta kosa ta Haihu Cikin ya mata girma ya koma yana Rinjayanta.
Danmallam duk ya Damu ya koma yana matukar jin Tsausayinta Hajiya ta bada Shawaran su koma asibiti haka kuwa akayi da ita suka koma wajen Dr.ghali da Amina shi kanshi yanayin Daya ganta yasa yace zai sanya mata ruwan naguda ya gani.
Allah Sarki Duk mai imani sai ya Tsausayama Amina an saka mata Ruwan Naguda ta fara asa asa kamar abun zai yuyu sai kuma shiru sau Biyu ana saka mata sai nagudan ta Fara ta Tsaya anan asibitin ta kwana Tare da Hajiya da Yakaka Danmallam kuma duk hankalinsa a tashe yake washegari asibitin ta cika da su Anty Hadiza da su Aba har da ya Jafar da matansu..
Mallam ma yazo ganin yadda Amina ke kukan azaba tana fadin acire mata Ckkin jikinta zata mutu yasa yace bari ya koma gida ya yi mata addu"a a ruwan Zamzam ya kawo mata tasha tagani shi ya hana asake mata alluran nagudan ganin yadda take wahala kamar zata mutu kuka reras haka Danmallam ke yi saboda ganin Halin da Amina ke ciki hatta Sarood da tazo asibitin sai da ta tsausayama Amina da kuma kanta Tunda itama ai cikin gareta
Tafiyar mallam ba Dadewa sai gashi ya aiko Hajiya Nasara da ruwan zam zam din da yayi ma Amina addu"a shi kuma yana gida yana cigaba da taya Amina addu"an Allah ya sauketa Lafiya Hankula duk sun tashi.
Kamar an kara ma Amina azaba tana sha ruwan zam zam din nan abubuwa suka taso mata haikan tana kamkame jikin Hajiya hannayenta cikin na Danmallam tana kuka tana Fadin su yafe mata mutuwa zatayi Aba duk Dauriyansa bayan rasuwar yaya da abunda Balaraba tayi mishi wannan ne karo na uku Daya ji ya raunana Waje ya fita chan haraban asibitin yana kuka tare da Fatan Allah ya Sauke Amina lafiya..
Anty Hadiza ma har da kwallarta Kowa fa jiki yayi sanyi ganin Haka yasa Danmallam yace ma Dr.Ghali a yi ma Amina aiki a ciro mata abunda ke Cikinta.
Nan da nan kuwa aka fara shirin yima Amina C.S,Bayan Danmallam ya saka Hannu kudin aikin ma su jafar sukayi ta Zirgan Zirgan Biya Hajiya ta amince da hakan saboda Amina ta Wahala har mallam data kirasa ta Fadamai ya amince yace indai za"a samu mafita ayi din yafi Alheri.
Koda aka shiga da ita Dakin Tiyata Amina ta fita Daga Hayyacinta Danmallan ko addu"a ya kasa yi ya Fara Hango kansa Rayuwarsa ta lalace in ya rasa Amina sai da Yakaka ta yi bashi baki sannan ya iya fita hataban asibitin ko Sallar da yaso yayi ya kasa Cikin Mota ya koma ya Dafe kansa kawai yana kiran sunan Allah hatta Hajiya ta kasa mgana Saboda itama ta Shiga Dimuwa..!
Allah mai hikima ana shiga da Amina Dakin Tiyata Nagudan gaske tataso mata Sai dai su Hajiya suka ga Nurses suna kai da kawo da gudu suka zo suka karbi akwatin kayan Haihuwa suka shiga dashi Dr.ghali yayi matukar mamakin Lokacin Daya Duba Cm din Amina yaga Saura 2cm sannan kan yaro na kokarin fitowa Kananun shekarunta yake kallo yana Tunanin Haihuwa da kanta zai ja mata Tsinkau  Tsinkau ko yoyon Fitsari sai gashi Cikin Hikimarsa Amina ta fara kokarin Haihuwa da kanta Nishi kawai take yi da kakari da Taimakon Dr Ghali da Nurses dinsa Amina ta Sintalo manyan ya"yanta guda Biyu abun mamaki Kusan atare Jariran guda biyu suka Sulmiyo Daya na Fitowa Dayan ya Biyosa sai kuma Amina ta koma ta yi yaraf kamar bata da rai Dr.Ghali ya taimaka mata Uwar ta fito Nurses suka fara aikin gyara wajen Wasu kuma suna faman goge yaran bayan sun yanke musu Cibi Amina kuma Dr.Ghali ya samu natsuwa ganin tana Da rai allurai ya Hada yayi mata sannan ya fara kokarin gyara mata jikinta bai cika Tsayawa Irin haka ba da zarar mace ta Haihu ya gama mata abunda ya dace yake barin ma Nurse sauran ammh Amina ta Dabamce Matar Bazanga ce..!
Yaran duka maza ne sannan sun fito a wahale yasa basu yi kuka ba sai da Nurses din suka Daga su sama suka Daki bayansu sannan atare suka Callara kuka Gabadayansu sai suka washe Baki Dr.ghali na mirmishin jin Dadi yace"Alhamdulillah..!

Su Hajiya kuwa kamar amafarki sukaji kukan jarirai daga Dakin Tiyata sai suka fara Tunanin aikin ko yayi Sauri yanzu fa aka shiga da ita Hajiya tayi Hamdala acikin ranta suna nan dai Zaune suna jiran tssmmani.
Rabin Sa"a kafin Nurses guda Biyo su fito da Jarirai guda Biyu Cikin kayan Sanyi Farare masu kyau Hajiya ta kasa gasgaata abunda ta gani Amina ta Haifi yara Biyu duka maza..?
Allah mai iko Annabi mai Dubun Daraja.
Hajiya Nasara ta karbi ya"yan tana Hamdala daga ita sai su Nasir da Aba da Anty Hadiza da matan su ya Nasir Baki yaki Rufuwa Hajiya kuma Hannu ta Daga sama tace"Alhamdulilah..Godiyata tabbata ga Allah Shugaban Duniya..!
Sai hawaye tana sharewa sai ga Dr Ghali ya Fito Hajiya na ganinsa ta karisa tana Fadin"Sannu likita mungode fa..Ina Aminar ina fata Lafiya take..?
Dr Ghali yace"Lafiyanta kalau mama..Na mata alluran hutu ne sannan ga karin albishir ma Amina da kanta ta Haihu bamu riga ma mun yi aikin ba..!
Hajiya bakinta Har kunne take fadin"Alhamdulillah..Allah mun gode maka..Ashe yan Biyu ne acikin Amina bamu taba sani ba..?
Nidai nace cikin nan yayima Yarinyar nan girma ashe ashe..!
Dr Ghali yace"Hakan na faruwa Mama..ammh ni sanda suka zo na mata Scan na gani.Sai dai ban Fada musu bane ina Tunanin sun sani..!
Hajiya tace"To mudai bamu sani ba.kila dai Aishan ta sani Dayake chan wajenta ta zauna har cikin girma...!
Mungode Likita..!
Ya amsa mata kafin ya karisa su gaisa da Aba da ya Jafar sai.Nasir sannan ya koma Office dinsa ba Dadewa aka Gunguro Amina kamar gawa sai numfashi zuwa Dakin da zata Huta.
Hajiya Bakinta har kunne ta kira mallam tace mai tayi mazaje Shima Hamdalan yake yi Danmallam kusam shine na karshen sani Sai da Jafar ya Kirasa a waya ya Dawo Cikin asibitin.
Ya kasa yarda Amina ta Haifamai yan Biyu Duka maza bai karbi Yaran ba sai da ya yi sudujul shukur Yayi ma Allah Godiya sannan ya Dago ya karbesu hannun Aba yaran kamar yayi kaki Sai dai sun Dauko Fuskar Amina kadan da idanuwanta sannan Kuma Indentical ne bamai iya bambamcesu
Kadan ya gansu ya mikama Sarood su da Bakinta yaki Rufuwa Ya shiga Dakin da aka kai Amina ya ganta Hankalinsa ya kwanta ganin tana Numfashi haka ya Rumgumeta yana kwarara mata addu"a tasha albarka kamar me ya Tsausaya mata domin Hajiya ta fadamai da kanta ta Haihu bai Taba zaton Amina zata iya Haifan Daya da kanta bama biyu ba.sai gashi Allah yayi ikonsa..!
Danmallam Aliyu ne mutum na Farko Daya fara Kira ya fadamai karuwar Daya samu Aliyu ya tayasa murna Bakinsa har kunne yana Fara"Barkallahu Fika Ya shehi..Amina kwaila yanzu ta zama giwar mata..!
Umar yace"Kai fa banza ne meye kuma na Tuna baya..?
Aliyu nayi ta mai Dariya shima bakinsa har kunne yace"Hakane fa..To Allah ya raya Allah yayi musu albarka Sai mun zo barka..!
Da haka suka yanke kiran Kowa cikin Farinciki Aliya shi ya koma gida ya Fadama Aliya sai ta kara jin Imani ya Shigeta ta kuma kara yarda Duk abunda yaso Faruwarsa sai ya Faru..!
Sakina take tsausayi domin suna waya tasan Halin Data ke ciki har Cire mata Mahaifan da akayi yau wagari ya waya..?
Duk wanda ya bari Duniya ta Rudesa ya gama yawo haka zai zo ya kare a Duniyan ba riba Lahiran ma haka.
Kafin yammah Labarin Haihuwan Amina ta Zagaye Dangi kaf yan"uwanta ba wanda bai ji wannan Haihuwar ba ya Aisha ce duk ta Kira ta Fada musu Hanne da Hamida sai Tsallen murna suna Tunanin Waya ga Amina da ya'ya har Biyu..?
Ya Aisha har ya Sadiya ta kira ta Shaida mawa ita kuma ta kira Sa"adatu Fatan Allah ya raya sukayi Saboda Duniya ta koya musu hankali Sannan dukkansu sukace bazasu gayama Sakina ba kada Hankalinta ya tashi susan Halin Datake ciki..!
Har Jordan Labarin Haihuwan Amina yakai da Gusai suna ji da gayyar aka Dinga Fada a tsakar gida har Mamanmu daje wani karamim Daki tana jinya taji,Domin tana jin mgana sai dai bata iya mayarwa ne sannan kuma bata gani yanzu idon ya koma sai Lalube.
Taji Haihuwan Amina sai kukan zucci Lalle ta yarda Zakaran da Allah ya Nufa da chara..!
Sakina ma ta ji Domin Aliya ta kirata ta Fada mata Kuka take yi reras dataji Labari shikenan Burinta bazai taba Cika ba har Abada bazata ga k'wanta aduniya ba..Tayi kuka ranar kamar ranta zai fita ita kanta Anty A"i ta kasa lallashinta Domin tana tausayama Sakina  gashi har yanzu basu kara ji Daga Bakin Danmallam ba ballatana makomar auran nasu sannan Sakina tace bazata kirasa ba Domin bata san da wani ido xata kallesa ba Anty A"in ne ma ta kirashi da wayar sakinar bai Dauka ba..!
Haka Allah ke tsara lamarinsa Sau Tari wasu Burukan namu mattatu ne har mu koma ga Allah bazasu taba Cika ba..!
Amina haka ta farka ta ga Kyautar da Allah yayi mata tayi kuka ta share Hawayenta ta Rumgume ya"yanta wani son su na kara kamata Ya Danmallam Yahadasu duka ya Rumgume lokaci Daya yana Fadin"Allah ya albarki Rayuwarki Noor Dake da zuru"arki gabadaya..!
Amina na sharan Hawaye a kafadan Mijinta Uban ya"yanta UMAR YUNUS ABDULRAHAMAN BAZANGA murya shake ta Furta"Ameen Ameen Hubby..!

*Janafty*
[10/25, 11:52 AM] +234 810 431 4972: *TFZB2030*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Chapter 94 · 0% Book details