← Book details Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 105

Sashe 100

Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

zata bi ya Danmallan madina sai Tsiya suke mata wai wa ya ga Amina a madina ita kuma tace sai ma sun ga ta Saje da Larabawa..! Sun Fara Neco dinsu cikin Nasara wani Lokacin da Yakaka suke zuwa makarantar in suna kuka takan fito ta basu Nono malaman makaranta su kansu mamaki suke Amina ce ta zama uwa ta kuma natsu kamar ba ita ba Tsakaninta da kowa sai gaisuwan mutuntawa Kamar ba itace a ka sha Gwagwamarya da ita ba Daman Haka Rayuwa ta gada Danmallam kuma Amina na Neman ta Hauka tashi ko barci ba yayi yasa ya nemi Tahowa sai dai bai sami Dama ba Sai karshen wata Yasa sai ya bari karshen wata in yazo sai su yi ta kare shi da Amina yarinya karama zata chazamai kai da Rigimanta Shi yana ganin Rigiman mata ammh na Amina na musamman ne ita kadai take Fushi Dashi yaji ya Damu yanzu hakama Duk ya kasa sukuni har su Sakina sun Fahimci wani abu na Damunsa ya Dade da Samin Amina nada Jidali Sai dai baisan haka take da Taurinkai ba sai yanzu da ta nuna mai Sai yaji yana raina ta ashe ta wuce nan sannan kuma yana raina matsayinta aransa sai yanzu yasan Amina ta fita zakka ko acikin zuciyarsa komai in da tayi Birgesa take yi. Bai yi shawara da kowa ba ya nemi Visa suma su Sakinan sai ana gobe zai Tashi ya Sanar dasu zai je Nageria Duk da bai Fada musu ba susan wajen Amina zai je basu ji Haushi ba Matarsa ce sannam kuma uwar ya"yansa.! Washegari yabi Mota zuwa Jidda Sannan Daganan jirgin Dare yabi zuwa Abuja,washegari suka sauka Filin Jirgin Nnamadi azikiwe Dake Abuja da yammah sallah kadai ya Tsaya yayi ya hau Motar Haya zuwa Gumel batare da ya kira kowa ba. !motar bata gudu sosai basu isa Gumel ba sai Dare misalin Karfe Tara a masallacin Anguwan ya Tsaya yayi Mangariba da Isha"i sannan ya nufi Gidan Amina get din na Rufe Daman bai Dauki megadi ba ta cikin gida ake Rufewa..wayar Amina ya Kira Duk da yasan bazata Dauka ba Haka ya Dinga jera mata Kira bata Dauka ba. Sai ya Hakura ya koma yana Faman Buga get din Amina na Dakinta kwance ita da ya"yanta har sun gama Hira da yakaka ta nufi Dakinta ita kuma tazo tayi wanka yaran daman yakaka ta musu na yammah ta Gaji yau English sukayi tun Safe sai yammah suka Dawo Har yaran sun gaji suna shan Nono sukaji Ruwan zafi suka fara Barci itama barcin Take ji Tana Fitowa wanka tayi salla ta Saka Rigar Barci masu Taushi Riga da wando ta saka Hula ta kwanta wayar ma na chan gefen gadon kuma tana Silent ne shiyasa ma bata ji ba Sannan har buga gidan bata jiba sai Yakaka ce Data fito Daukan ruwa a Kitchen taji kamar ana Buga gida. Sai ta Tsaya ta kara Saurarawa taji Dai da Gaske ne har zata leka Amina sai kuma ta fasa jikinta ya fara rawa tana Tunanin waye ne da Daddaran nan..? Sai tayi tunanin ko su Jafaru ne..? Yasa ta Dauki Tocila ta fita har Haraban gidan dayake an Dauke wuta tana fitowa taji buga get din anan ne yasa ta karisa jikin kofar tana Fadin waye..? Danmallan Dayaji muryan yakaka sai Hankalinsa ya kwanta Cikin Muryansa mai Sanyi yace"Ni ne Yakaka..!itama ta gane Muryansa Cikin mamaki tace"Danmallan..? Yana mirmishi yace"Nine yakaka..! Da Hanzari ta Cire sakatan kofar get din sai gashi ya bayyana a gabanta Har ya shigo tana cikin mamaki ita ta koma ta kara kulle kofar get din ta Juyi Tana Fadin"Danmallam zuwa ba Sanarwa haka.? Danmallam ya shafa kanshi bai ce komai ba yana Sanye da yadi mai Santsi riga da wando kansa ba Hula sai Sumar kansa data Fara Tahowa yana gaba tana Binsa a baya har Cikin Falon gidan sannan suka gaisa yaga gidan da Duhu Lokaci Daya yace"Yakaka Sun Dauke wuta ne..? Yakaka tace"Da yammah nan suka Dauke ammh nasan zasu dawo dashu..!. Danmallam yace"Yakamata aa Hada muku Solar Duhu ai ba Dadi..! Yakaka tace"Dayake ma suna barin wutar..Sannu da zuwa kasha Hanya...bari na kawo maka ko ruwa na yau bamu yi girki ba Takwara makaranta ta wuni sai da zamu Dawo ne muka biya gidan mallam muka Dauko waina gatanan in zaka ci na Zubi maka... Danmallam yace"Bakomai yakaka wanka ma nake so na farayi..! Yakaka tace"Eh to ya kamata shiga Ciki Aminar na ciki ina ga sun kwanta daga ita har yaran sun gaji..ya amsa mata da Toh ya juya kenan Tace"ahf kaga na manta ya wajen su Sakinar ne da mai juna Biyu..? Fatan dai suna Lafiya..! Danmallam ya juyo yana amsa ma yakaka da Lafiyarsu kalau sannan ya shige Dakin Amina a gaban gadon ya Tsaya kawai yana kallon Amina tana Barcinta Cikin kwanciyar Hankali ta saka Hannunta ta rumgume ya"yanta su Aba yake mamakin girmansu da kibansu wani Annuri na shiga cikin Ransa yana kallon Amina aransa yana auna yarda yar yarinyar nan ta Hanashi Sukuni Zama yayi gefen gadon bayan ya Sauke karamar Jakar Hannunsa yana kokarin Dauke hannun Amina kan yara saboda ya Samu ya Daukesu Caraf ta Rike Hannunsa da Karfi Lokaci Daya tana Bude idonta sai ya Fada kansa suka kura ma juna Ido na wani Lokaci shi na murnan ganinta ne da wani sonta da sha"awarta ita kuma na Bakin ciki da Takaici ne Daya Taimaka wajen Dakushe Zumudinta. Kauda hannunsa tayi ta mike Zaune Fuskarta ba Fara"a tace"Mallam Lafiya..? Girman Idonsa ya kara yana kallinta Cikin mamaki kafin yace"Mallam kuma..? Kawai sai taga ma zai raina mata wayau ya sake kai hannu zai Taba yaran da Sauri ta make hannun nasa ya Dago Cikin mamaki yana kallonta kafin yace"Amina ni kike bige ma Hannu don zan Dauki ya"yana..? Amina tamai wani kallon Tara saura kwata kafin ta sauko Daga kan gadon batayi wata wata ba ta Dauki Aba ta goya ta saka showel din Dake gefe ta Daureshi dashi sannan ta Dauki Mallam a Hannunta ta juya zata bar Dakin da Sauri ya mike yana kiranta,
Chapter 100 · 0% Book details