← Book details Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 105

Sashe 27

Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bai kira Aliyu ba kamar yadda ya kudira daga farko sai ya maida akalan kiran nasa ga Hajiya, mallam sun yi mgana dashi da Safe agogon Dake kafe a afishin nashi yabi da kallo yaga karfe 12 da wani abu na rana yana Tunanin achan Nageria yanzu Tara ne da wani abu na Safe.
Wayar Hajiya ta shiga gabda zata katse ta Daga kiran cikin Sallamarta ya amsa mata Cikin Ladabinsa kafin ya Fara gaisheta ta amsa tana Fadin"Lafiya lau Danmallan ya madinar da wajen aikin ka..?
Ina Saratu ina Fatan tana lafiya..?
Kansa na kasa kamar yana gabanta yace"Duk muna Lafiya Hajiya..aiki kuma alhamudulillah cikin Nasara da addu"arku..!
Hajiya tace"Masha Allah Allah ya taimaka..Allah ya kare ka Dammallam ya baka Zuru"a Dayyaba..yadda kake mana Biyayyah Allah ya jikan ka ya baka mai jin kanka kaima..!
Addu"a hajiya yasa yaji kamar yayi kwallah kaunar Mahaifiyar tasa na kara shiga ransa.
Cikin muryan sa mai cike da Zati da Haiba yake amsa mata da Ameem Ameen.
Mallam da mutanen gidan ya tambaya tace duk suna Lafiya kafin yace"Hajiya yau she ne tafiyarki maiduguri.?
Hajiya tace"Satin na sama ne zan tafi inaga Ranar Laraba..!
Kai ya jinjina kafin yace"Allah ya kaimu zan turo ma Jafar sako..Ki kaima Goggo ta kara Allah ya bada zaman lafiya..!
Hajiya cikin Farinciki tace"Angode Allah ya kara Wadata Allah ya Dafa maka..!
Ya amsa mata da Ameen kafin su yi shuru na wani Lokaci jin shurunsa yasa sai ta Fahimci yana so yayi mgana ne.
Cikin Dattakonta tace"Danmallam me kake so kace ne..?
Ya sosa kansa kamar tana gabansa kafin yace"Hajiya jafar yace ya kawo miki waya ko..?
Hajiya tayi yar Dariya kafin tace"Eh wlh ya kawomin tun kwanaki na Shafa"a ne ban bama Aminar ba..Dayake bata zama Da sun Dawo makaranta abinci kadai suke ciki sai su tafi islamiya da sun dawo kuma nake sawa akaita gida ni kuma Shaf na manta..Ammh bari in ta Dawo yau zan bata insha Allahu..!
Kansa na kasa kamar yana gabanta yace"To nagode Hajiya Allah ya kara girma..!
Ta amsa da Ameen Daga haka sukayi sallama Hajiya ta zauna gefen gadonta Tana kara nazarin meyasa Danmallam ya Damu da Amina ta rike waya Daga baya alhalin ita ta kawo Shawaran siyan waya Daga baya da suka Tattauna da mallam sai ya nuna mata illar hakan saboda Har yanzu Amina yarinya ce sannan Karatu ne agabanta,in ta rike waya yanzu zai Shagaltar da ita daga karatunta in Saboda su rika mgana da Mijinta ne ga wayarsa ko ta Hajiya duk wacce shi Umarun ya kira zai yi mgana da Amina shiyasa bata maida kanta kan bama Amina wayar ba ko ayanzu ma Datace mai zata bata tadai cemai ne kawai ba domin zata Tsallake Shawarar da mallam ya bada ba.!

Danmallam kuwa suna gama waya da Hajiya sai ga kiran Sakina ya shigo Yana ma kokarin kiran Aliyu ne kamar bazai Dauka ba sai kuma ya Kashe ya Kirata Tuna yau kwana Biyu basu yi mgana ba Shifa har yau Haushinta yake ji kan abunda tayi mai In ya tuna yadda ta kulle ko"ina ta tayi tafiyarta shi abu daya ya Damesa yadda ta tafi ta bar yar Mutane acikin gida in da yunwa ya kamata ko kuma wani abu ya Sameta ai da ya shiga uku wajen Hajiya da mallam kila sai sun kusa mai baki.
Sama sama daman yake da ita in ya kirata shima saboda sauke Hakki da Nauyin Dake kansa ne ba da domin haka ba sai ta kara Raina kanta.

Tana Dauka ko Sallama batayi ba ta Fara fadin"Habibi..!
Rai ya bata kafin yace"Bana fada miki..Ki daina daukan wayata baki min Sallama ba..?
Tuna haka yasa tayi Saurin mai Sallama ya amsa mata yana tambayanta lafiyanta tace"Lafiya lau Habibi ya aiki..?
Yace"Alhamdulillah ya naji kamar kina kwance ne..?
Gyara kwanciya tayi kafin tace"Wlh kuwa ban tashi ba..Tunda nayi sallar asuba na koma barci..!
Cikin mamaki yace"To Haka Aminar ke tafiya makaranta bata yi kari ba kenan..?
Sakina ta bata rai kafin ta tabe baki Tace"Wacece haka..?
Yana jinta sai bai tanka ba Sanin Halinsa yasa tace"Kace min wannan kazamar matarka taka..Ohon mata Daman na Fada maka bazan dinga mata Bauta ba, ba zamanta nake yi ba..!
Sai kuma yaji bai ji Dadin sunan Data kira Amina ba Duk da shine silar saka mata sunan sai yaji bai Dace ba Domin karshen kazanta kenan ya Ratsa Amina ahakanta,aiko kazanta ya kare.
Tattare naman goshinsa yayi bai yi mgana ba yana kokarin Daidaita yanayinsa Sakina ta cigaba da Fadin"Da Safe ake zuwa Daukanta makaranta ni bana ma sanin Tafiyarta..Sannan bata Dawowa sai yammah ranar jumma kuwa in tatafi makaranta da saafe sai Lahadi da yammah take dawowa sai mu yi kwanaki bamu hadu ba in ma mun Hadu bata min mgana sai kallon banza Habibi yarinyar nan ta gama Rainani bata da kunya Ranar fa Har Zagin Ubana tayi bayan tafiyarka ba Dadewa..!
Yana jinta bai ce komai ba aransa yasan Amina zata aikata A dan Sanin da yayi mata da labarinta dayaji Sama sama Zata aikata sai dai bai yarda ba Sakinar ce ta fara Zaginta ba yasan ta Sarai Itama Sakinar bata da Hakuri.
Yana jinta tana cigaba da Fadamai Rashin mutumcin Amina shidai bai ce komai ba illah"Kiyi hakuri zan kirata zan mata fada..!
Sakina tace"To tana da waya ne..?
Kai Tsaye yace mata"A"a chan gida zan kira abata na mata fada..!
Sakina taji Dadi yasa ta gyara kwanciya tana kara shigewa Cikin blamket tace"Habibi yaushe zaka zo ka Daukeni..?
Ni in bazaka zo ba sai Su Jafar su Nemin Visa na taho..!
Yana jin mganarta yamata shuru Sai da ta fara magiya tana Fadin"Don Allah Habibi kayi Hakuri na tuba nabi Allah na bika..Wlh Daga yau bazan kara saba Umarninka ba..!
Ta karishe Fada Cikin kukan Shagwaba Saboda ko jiya sun yi mgana da Anty ta tabbatar mata da cewa mallam ya sanar da ita Umar zai zo ya Dauketa Dolensa..!
Shiyasa ta tadamai da mganar ita a Tunaninta komai ya zama yadda suke Fata abunda basu sani ba ba kowani Lokaci Allah ke basu nasara ba akwai lokacin da aikin da suke da yakini a kansa zai basu mamaki..!

Sai da ya gama jinta sannan yayi gyaran Murya yana fadin"Sakina na Fada miki abaya zan kuma kara Fadamiki a yanzu..in har ni mijinki ne mai baki Umarni ki bi to bazaki Dawo madina yanzu ba..Sai nan gaba in kin gaji da zaman gumel din..!
Sakina jikinta ya fara rawa  gabanta na Fadi ta ce"Habi..!
Bata karisa ba ya katseta da Fadin"A wanchan Lokacin sai da nace kada ki zo..Kika jin mganata kikace sai kin zo..Biki nawa ake yi baki san zaki je ba Zan ce miki ki shirya mu taho..?
Abaya bake kika bani Shawaran Dauko ki na kawo ki garin nan ba Ni nayi Ra"ayin haka,kamar ni nace ki Hakura da zuwa Bikin su Abida Tunda ba an gama sha"anin bane akwai wasu masu zuwa kika jin mganata kika kuma Zuga Sarood itama ta Tada min rigima Duk Saboda nace ki Zauna bani da kudi sosai sai wani lokacin..!
Sakina ta kwaso Rantsuwa bai bata Dama ba ya cigaba da Fadin"Ita mahaifinta ya Dakatar da ita bata Biyoni ba..Ke kuma kika Biyo ni kikazo to kuma Miye na jin Zafi Domin nace sai nan da wani Lokaci zaki koma..?
Ai kina son zaman nan din ne shiyasa nayi miki abunda kike so..Wlh itama Data sake ta Biyoni Dukkan nan zan barku nayi Tahowata lokacin da na Sanu Dama da Hali sai nazo na Taho Daku a kallah dai nayi muku abunda kuke so kada kuce nayi miki rashin Daidai..
Kinsan Wlh rantsuwa ce ko..?
Sakina sai in na Samu Lokacin nazo sai mu koma Tare in kuma kika ce zaki Biyoni bansani ba to ba da Izinina ba..!
Daga haka ko cewarta bai jira ba ya Katse kiran yana Faman kokuwa da Bacin ransa Sakina kuwa kamar tayi Hauka haka ta mike tana Laluban wayar Anty sai dai bata Sameta ba Kasa Zama tayi ta mike tana Safa da marwa acikin Dakin tasan Waye Umar kaifi Daya ne in yayi mgana baya Sauyata ammh sai da ts saki jiki da Anty da ta tabbatar mata da cewa zai zo su koma Tare,sai dai wannan Jadadda mganar tasa yasa ta kara Sarewa a baya ma acikin ranta har ta Tsara in bai zo ba zata yi Visa da kudinta ta bisa sai dai ya ganta ai tasan Hanya ba inda bazata kai kanta ba A madina ba.!
Sai gashi furucinsa ya sa wannan Tunanin ya bace mata tasan kuma tunda yace bada yawunsa ba in ta Sake ta taka wani abun ne kuma zai Faru na Dabam wanda bata Fata wayar Anty Amarya tayi ta Kira kamar zatayi hauka bata Sameta ba
Chapter 27 · 0% Book details