← Book details Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 105

Sashe 14

Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Amina na dunkule akan gado tana rawan jiki taga lokaci Daya Haske ya kawo leko da kanta tayi sai taji dan sanyi a zatonta nepa sun kawo wuta ne,Sai rabin hankalinta ya kwanta ganin haske sai dai kuma me sai taji kamar tana jin motsi saurarawa tayi sai kuma bata karaji ba sai da ruwan yadan Dauke sama sama taji ana kiran sunan Sakina sai ta kara Tsoracewa kara Dunkulewa tayi saman gado jikinta na rawa kamar a mafarki taji an shigo Dakin data ke sai Amina ta kara shigar da kanta Cikin Filon ba inda jikinta ba ya rawa addu"a kadai take yi duk abunda yazo Bakinta sai ta fada Hawaye kuwa kamar an Bude famfo.
Kamar a mafarki taji muryansa yana Fadin"Ke...ina Sakina..?
Haka ya fada yana Tsaye daga kofar Dakin yana binta da kallo Cak ta Tsaya da rawan jikin sai da ta Leko ta filon ta hangesa Tsaye sannan ta sauke Numfashi Cikin Dan salama ta Dauke Filon Fuskarta ta mike zaune tana kara Dunkule Hijabin jikinta.
Kallonta yake yi ganin hawaye Chaba Chaba a fuskarta yasa yace"Me yasa same ki kike kuka..?
Ina sakina taje ne..?
Kanta na kasa tace"Ni bansani ba..Ni kadai ce agidan..kuma tsoro nake ji ina ta jin motsi..!
Sai ta kara fashemai da kuka bai Damu da kukanta ba Fadi yake yi"Sakina bata nan..?
Cikin alamun Tambaya Amina ta Dagamai kai kafin tace"tun dazu ba kowa agidan sai ni kadai agida..Tsoro nake ji don Allah ka maidani gida..!
Bai ma Saurareta ba gabadaya ransa ne ya baci kenan Sakina bataji mganarsa ba sai da tatafin yau kyafci yayi kawai yana Sakin Hucin Zafin zuciya,Allah ya kaddara bazasu tashi ba Koda ukun tayi matsalan bata kau ba nan aka sanar dasu sai jibi zasu tashi da Daddare yaso ya kama Hotel anan kano har zuwa jibin sai kuma yaji ya kasa gwara ya dawo gida bayason ya Wahalar da su Jafar yasa bai kira kowa ba ya tafi tasha ya hau motar Gumel sun fara tafiya Motar ta samu matsala wajen awa biyu kafin agama gyaran koda suka shigo gumel an yi issha"i sannan sun zo ana ruwa kamar da bakin kwarya,Shi ba ya iya Fakewa ako"ina shiyasa ruwan ya Tabasa sallar kadai ya tsaya yayi a wani gidan mai,kamar zai wuce gidan Mallam sai kuma ya fasa saboda bayama son sun san Tafiyarsa bata Yuyuba.
Sai gashi ya dawo ya iske wannan Rainin da Sakina tayimai gashi bai da key din kowani Daki acikin gidan Suna wajen Hajiya,Sannan akwai wani hannun Jafar yanzu kuma Dare yayi bazai yuyu ya kira yace a kawomai ba sai ya Tada musu hankali a yanayin Dayake ciki ko Ta kan Amina bai bi ba dake sharan hawaye Jakar hanmunsa ya Sabule nan saman Cafet ya taka ya nufi Cikin Tiolet din Dakin ya Rufe.
Ransa sai da ya kara baci ganin yadda kazantar Amina ya maidashi ga kayanta nan data cire saman kwandon wanki bazata iya Budewa ta saka ba sannan ga pant din ta nan da ta wanke basu fita ba ta shanya ajikin Famfo ransa ya kara baci bayin Daga gani an Dade ba"a wankesa ba Bashi da wani Zabi sai nan Tiolet din Shiyasa bai fito ba sai da yayi wanka ammh kuma sai da ya wanke Bayin tas sannan ya iya yin wanka da ruwa mai Zafi ya gasa jikinsa yana jin yunwa ga Mura ta kamasa ga kuma Sanyi Dayake ji Towel ya Dauro a kugunsa ya fito kayansa kuma Cikin kwandon wankin ya Bude ya saka yana Fitowa suka hada ido da Amina yadda ta Zabura sai da ta bashi tsoro Ido ta Runtse ta sheka da gudu ta Fice Daga Dakin tana fadin ta shiga uku da Harara ya Bita kafin yaja Tsaki Afili ya Furta kazama kawai.
Lotion din Sarood dake saman madubi ya shafa saboda komai nasa na Dakinsa,Jakarsa ya Bude ya sanya Jallabiya baka mai kauri kauri Saboda yana jin sanyi kan gadon yabi da kallo duk kaya ransa ya kara baci kamar zai Dauketa mata sai kuma ya fasa ya fita Falo ya ganta zaune saman cafet ta Dunkule waje daya asaman kanta taji mganarsa yana fadin"Wanene zai Dauke miki wadanchan kayan da kika zubema mutane akan gado..?
Agidanku haka kika ga anayi..?Ina amfanin Wardrope din Dake Dakin..?
Amina ta kasa Dagowa itafa tunda ta gansa ba riga jikinta ke rawa ashe haka yake da girma itafa saboda Tsoro ko kallonsa ma batayi ba azatonta bai da rigan ne Har lokacin.
Shiyasa ta kasa Dagowa tsawa ya Daka mata yana fadin"Ina mgana kina banza dani ni sa"anki ne..?Zaki zo ki kwashe kazantarki ko sai nazo na Tattakaki..!
Jin haka yasa ta mike jikinta na rawa tana fadin"Ka..yi hakuri..!
Hanyar Dakin ya nuna mata cikin fushi ta wuce sumi sumi tana tsoron yakai mata hannu haka ya tasata gaba sai da ta kwashe kayan saman gado ta Tura cikin wardrope a yamutse ya Dakamata Tsawa yace ta kwaso ta Ninke su hakanan ta kwaso ta ninke ta saka aciki tana sharan kwallah bayan ta gama ya nuna mata kofar Tiolet yana fadin"Shiga ki Tararra kazantar da kika shanya ki Samu waje ki boyesu da safe ki fita dasu bola..!
Amina ta kallesa kafin tayi mgana ya Rigata da fadin"zaki wuce ko kuwa..?
Da gudu ta shiga ta Tatarra kayan har da Pants din ta Tusa cikin kwandon Tana kuka fadi take"Mamanmu..Hajiya..mallam..!
Yana jinta har dasu Hamida ta Kira Dariya ma ta bashi ya tabbatar ma kansa yarinyar nan bata da kunya iskancinta kadan ne.
Haka ta fito tana Labe labe tana sharan kwallah kallo Daya yayi mata ya fice daga falon yunwa yake ji sosai kuma ga shi ba wani abu zaune yake saman kujera yayi Tagumi ya rasa mafita har na tsawon wani Lokacin ganin ba mafita yasa ya gyara kwanciyarsa saman kujera mai zaman mutum uku sai dai ina Sanyi da Zazzabi suka Damesa ga shi har Lokacin ana yayyafa kamar ma ruwan zai Dawo Takurewa yayi waje Daya saboda bargon Dakin Amina ko Sanyi  zai kashesa bazai iya saka Jikinsa aciki ba ya tabbata ya fara Warin Datti.
Har barci ya fara Dibansa yaji ruwa ya Dawo da iske tashi yayi ya Zuge Duka wimdunan falon sannan ya koma ya kwanta yana Faman kokuwa da yunwar Dake damunsa Ko achan Filin Jirgi Tea kadai yasan sha shima bada yawa ba tun kuma shine acikinsa.
Yana bukatar yasha ruwan zafi ko zai gasamasa ya"yan Hanjinsa sannan kuma da Zafin da jikinsa ya Dauka kafin wani Lokacin Hancinsa ya toshe Saboda Mura.
Yana kwancen yaji wata Tsawa da akayi shi kanshi sai da ya Bude ido Lokaci daya da walkiya mai Haske da Sauri yace"Bismillah...!
Kamar ihunta yaji kafin ya mike yaji ta, ta fadomai ajikin jikinsa tana rawan jiki yana Daga kwancen yajita kan jikinsa yadda ta kamkamesa kamar zata balla sa yana ma yi mamakin karfin hannun yarinyar.
Kokarin riketa yake ammh taki basa Dama kanta take tusawa saman kirjinsa da Karfi Tana kuka lokaci Daya tana fadin"Na shiga uku..Ka boyeni Tsawa..Tsawa...!
Haka take fadi jikinta na rawa sai kuma ta fara wani abu irin na kakkafewa Saboda an karayin wata Tsawar ganin haka yasa shima sai ya Riketa ya fara Tofamata addu"a ganin yanayinta ya fara tunanin wani abu.
Addu"an dayake tofamata yasa sai ta bar kafewan ta koma ta kamkamesa ta fashe da wani kuka mai cin rai har Muryanta na Shidewa fadi take"Wayyo mamanmu...!
Haka take fada Cikin kuka duk yadda yaso ya cireta acikin jikinsa ya kasa kamkamesa tayi kamar zasu zama abu Daya tana kuka Danmallan yaji wani bakon al"amarin daya Faru dashi wanda bai taba Faruwa dashi ba ko da akan Sakina ne.
Wani irin Dumi yaji jikinsa ya kara Dauka wani abu ne yake yawao ajikin jikinsa Tunda ga yatsun kafarsa har saman kansa nan da nan yaji sa cikin wani yanayin yanayin da bai Taba Riskan kansa ba.
Hannuwansa yasa duka Biyu ya Dafe bayan Amina yana Lallashinta lokaci Daya yana Tofa mata addu"a sai aka samu tayi sanyi da kukan data ke yi,Neman yake yi ya rabata da jikinsa ko zai daina jin yanayin dayake ji,ammh ina ta rikesa gam taki Sakinsa ga sanyi ga Iskar ruwa tunda kamar ruwan ya Dawo ne da Bakin kwarya yasa ya mike rike da ita har Cikin Bedroom din da Amina ta baro,Saman gadon ya so ya kwantar da ita ammh Amina taki yarda yana so yaga Fuskarta taki bari sai boye kanta take yi a jikin jikinsa Danmallan ya kalleta sosai yana kara nazarinta meke damun yarinyar nan..?Addu"an ya cigaba da tofa mata sai jikinta yadan saki kadan ammh kuma taki sakinsa gam take rike dashi Cikin Sanyin murya yace"Sakeni mana..An daina Tswan baki ji bane..!
Amina taki sakinsa fadi kawai take"Don Allah ka boyeni tsoro nake ji..!
Dole ya koma ya zauna saman gadon yana Rike da ita addu"a bata bar bakinsa ba har sai da yaga ta Dawo Cikin natsuwarta sannan ya kyaleta bayan ya kalleta yace"To sakeni..!
Da sauri ta sakesa ta koma gefe ta lafe jikin gadon tana raba ido Sauka yayi Daga kan gadon sai gata itama ta Dirko ta rirrikesa juyowa yayi yana kallonta kafin yayi mgama tayi saurin Fadin"Don Allah kada ka fita ina jin Tsoro..!
Cikin idanuwanta yake kallo yaga gaskiyanta itakuma kanta ta maida kasa sai hawaye,Cikin Taushinsa yace" ba fita zan yi ba..Nan kasan Cafet zan koma na kwanta ke ki kwanta saman gadon..!
Cikin Tsoro ta ce"To..to...to..Don Allah ka da ka fita..Wlh tsoro nake ji..!
Ta karishe fada da kuka karo na Farko da ta bata bashi Tsausayi sai ya Tausasa Murya yana fadin"bazan fita ba..ki koma ki kwanta in kin ji tsoro sai kiyi addu"a..!
Kai ta gyada mai cikin Sauri yana Tsaye rike da hannunta ya maidata kan gadon ta kwanta tana Raba ido sai Hawaye sharr ganin haka yasa yace"In baki bar kuka ba zan yi tafiyata..!
Jin haka yasa da Sauri tace"Toto...To...Don Allah kada ka fita..!
Kai ya gyada mata kafin ya Dauki Filo ya jefar a kasa zai kwanta tana binsa da kallo ganin zai kwanta a kasa yasa ta mikamai Bargon Dake kan gadon tana Fadin"ka shimfida bargo ya Danmallam..!
Juyowa yayi yana kallonta kafin yace"Kefa..?
Kai Tsaye tace"Bana lulluba dashi..!
Kamar bazai karba ba sai kuma ya sa ka hannu ya karba Domin yana jin Sanyi,Kwanta wa yayi sannan ya Rufe kafarsa da Bargo sai da ya tabbatar da baya wari lafiya kalau yake shi.
Dukkansu idonsu biyu sun kasa barci Yana jin motsinta sai ta tashi ta lekasa sai tagansa sai ta koma ta kwanta Shima bai iya barcin ba yana mamakin Lamarin Amina ne ya fara Zargin yarinyar nan na da wata matsalar da bakowa ya Santa ba.
Har barci ya fara Daukansa Yaji ihunta Da Sauri ya bude ido ya mike Lokaci Daya sai gata ta Dirko Daga kan gado ta Fadomai,Tana wani rawan jiki Cikin tashin hankali ya riketa yana faman kiran sunanta bata ji ba Fadi take ye ya Boyeta Tsoro take ji Dakyar da addu"a ta Dawo Daidai sai kuka Rumgumesa tayi gam tana Fadin"Ya Danmallam kayi ma girman Allah ka hawo gadonan mu kwanta..Ko ka maidani gida wlh agida in na tsorata abayan mamanmu ko na Hamida nake iya barci..!
Tsausayinta ya kamasa bai iya mata gaddama ba tana rike dashi suka karisa kan gadon sannan yace mata"To sakeni ki hau gadon..!
Ba musu ta sake sa ta hau gadon shima ya Hayo yana hawa ta kara Rikesa baki ya saki kawai yana kallonta kafin yace"Kina addu"a kuwa in kikaji irin wannan tsoron..?
Kai ta gyada sai hawaye kafin yace"To me kike karantawa..?
Amina sai ta Rushemai da kuka baki ya Saki kawai yana kallonta Ya fara Zargin wani abu na Damun yarinyar nan,kansa ciwo yake yi yasa ya samu yalallasheta ta bar kukan yana dora kansa saman Filo tabisa ta Danne kamar zata maida shi Ciki Danmallan ya Dafe kansa kawai yana Salati ita bata san in tana tabasa yanayinsa na Sauyawa bane.
Ta gefensa ya zura hannu ya kashe Hasken Solar Dakin ganin Duhu yasa Amina ta saka Ihu Saurin Daka mata Tsawa yayi yana fadin"In kika sake min Ihu zan tashi na yi tafiyata Wlh..!
Jin haka yasa tayi Tsit ta koma kan kirjinsa tana Sauke Numfashi
Wani al"amari ne da Allah kadai ya bar ma kansa sani yanayinsa yake ji yana Hauhawa Tare da tafiyar Numfashin Amina Dake kan kirjinsa abunda bai taba Tunanin zai Faru dashi ba in yayi Duba da wasu sabbin Abubuwan da suka faru dashi bayan auran Sarood.
Lamarin ya faru ne batare daya shirya ba ko nace sun shiryama hakan ba Dukkansu,Umar bazai iya Dora komai akan lamarin dayake shirin Faruwa ba,Amina bata Farga ba Domin tana cikin Tsoro sosai,shiyasa sai da abun yayi nisa ta Farga tayi kokarin kwace kanta sai dai ina Bakin alkalami ya Riga ya bushe..!
Acikin wannan Daran ana cikin Tsuga wannan ruwan na Farkon Damina Wani al"amari ya Faru Tsakanin Amina da Danmallam,Umar ya karanto addu'ar da Annabi ya koyar damu acikin Ransa yana kuka,kukan kokowa da yanayinsa ya Ratsa Amina Ratswar da zai zama silar abubuwa Dadama wanda bawa bai tsammani ba..
Wasu basu zata ba..Tsammanin Abunda basu yi Tsammani bane zai Farun..
Alkwarin Allah ya sake cika.
Zanen kaddaransu ya hadu.
Allah ya amintar da Ruhinsu ya Gauraye jininsu waje daya batare da masu kokarin hana Faruwar hakan sun Farga ba..!
Chapter 14 · 0% Book details