Sashe 81
Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
kawai sai jin kakkusan muryan Aba sukaji ta karade Falom Cikin wani amo mai karfi da ba"a taba jinsa yayi irinsa ba..!
Sai kallo ya koma kansa ayadda Idanuwansa suka kada suka yi Jajir kamar gauta sai ya baka Tsoro ya mike jikinsa na karkarwa yana nuna Mamanmu da yatsa yana Fadin"ke kika kasheta..Kika rabata da Duniya Batare da ta miki komai ba. ?
Meyasa kikayi haka..?
Meyasa kika kashe ran da bata taba Sauya matsayin ki aranta ba .?
Balaraba Bazaki taba gamawa da duniya Lafiya ba..!
Kawai sai kuka jikinsa ya fara rawa yana neman Faduwa Jafar ya mike da gudu shi da Nasir suka taroshi ya Fada Jikinsu yana kuka jikinsa na rawa yana karkarwa yake fadin"Ita ta rabani da Hadiza..Ya Allah ka wulakantata..!.
Sai kuka gabadaya sai kowa yaji ya kara Raunana.
Jadwa da Jaleela suka ruga wajen Abba suka rikesa suna kuka sai ga Jamila itama da Jawahir,har da Jawaad na wurin yana kuka duk da ba Duka yake Fahimta ba ya Fahimci kan Rasuwar Yaya ce.
Ganin haka yasa Amina ta kalli ya Dannallan cikin rauninta tace"Ina so naje wajen Aba!.
Bai musa ba ya Saketa Lokaci Daya ya mike ya taimaka mata ta mike ya karisa da ita gaban yan"uwanta dukkansu suka Dago suna kallonta Aba yana Kuka Kukansa na Fitowa yace"Ki yafemin Amina..ki yafemin..!
Kawai sai Amina ta zube kan kafafun Aba ta wani saki kuka,kukan da kowa yaji sai da jikinsa ya kara yin sanyi Su Jamila suka Fada kan Aba suma suna kuka mai tsuma zuciya Danmallam na gefe yana jin kukan Amina har Cikin Ransa da Ruhinsa ammh ba yarda ya iya Bai isa ya hanata kuka ba..!
Su Zulfa suna ganin su ya Jawaheer wajen Aba ammh kunya da Bakimciki sun saka sun kasa karisawa garesa suna Zaune sai sharban kuka suke kada Hamida ma taji Labari..
Anty Amarya ta runtse ido sai ga Hawaye lokaci Daya Tana Fadin"Tun Lokacin da naji labarin wannan auran Hankalina ya tashi..Saboda bai kamata wata tazo ta sha gaban Sakina ba..Duk da duk kokarina Burina bai Cika ba,Sakina ta samu Ciki sau hudu tana barinsa..Auran Amina ya razanani ni da Sakina razanan da bamu yi shi Lokacin auransa da Sarood ba Saboda ita na saka mallam ya maidata Hoto..An yi ma Umar Sihirin da bazai iya Zama namiji awajenta ba..Awajen Sakina ne kadai zai amsa sunansa Namiji..!
Danmallam ya kalleta Tsam kafin ya juya ya kalli Mallam shima shi yake kallo.
Danmallam kansa ya maida kasa bayan sun Hada ido da Aliyu da mamakin abunda ke faruwa yasa ko motsi ya kasa Anty Amarya ta Cigaba da Fadin"Yadda Mallam ya shammacemu ne yafi batamin rai..Sannan ina Tunanin da Sanin Sa"idu komai ya faru..shiyasa na yi alkawarin shima sai ya Kurbi kwatancin bakimcikin daya kunsamin na Kira Dayyaba muka yi mgana..Nace mata ya kamata Yaya TA,MUTU..ita kuma tace Tabbas ya Dace ta Mutum..Ko domin ta Rama Bakin cikin da Sa"idu ya Dade yana kunsamata aranar na Kira mallam na Fadamai komai,Adaran kuma ya Turo ma yaya Hayakin Daya Turketa ya Sarke mata Numfashi...Numfashin Da yayi Sanadiyar mutuwarta..!
Anty Amarya ta karishe Fada Cikin gunjin kuka ita da Mamanmu gabadaya Falon aka Dauki Salati sai kuka Mamata na Sharan hawaye tana Fadin"Wannan wani irin mugunta ne..?
Gaskiya Balaraaba bazaki gama da Duniya Lafiya ba sai kin lalace..!
Hajiya kanta sai da ta Durkusa kan gwiwiyonta cikin rauni tace"Wani irin Rudin Duniya yake diban ku da har kukayi Tunanin Kashe ran da bata muku komai ba..?
Kai Haabunallahi wa"inamal wakeel..!
Hajiya take fada sai ga Hawaye ganin yadda Hajiya ke kuka ga Aba nayi da su Amina sai kusan kowa ma ya fashe da kukan banda Mallam da Mazan dake da sauran kwarin zuciya.
Ammh yau kam Jafar shima kukan yake rerawa Hawaye wani na korar wani.
Anty Amarya bata yi shuru ba ta cigaba da fadin"Mun so auran Amina da Umar ya kare a lalace ne Ganin An Dibi Lokaci basu tare ba sai muka Saki jiki..Sai kuma kwatsam Hajiya ta taso da mganar tarewar Amina Data rugazamin Shirina ni da Dayyaba ba yadda bamu yi ba kada hakan ta Faru ammh ina Bakin Alkalami ya riga ya Bushe Allah ya Rubuta kaddara zama Tsakanin Amina da Umar..Bayan ta tare na saka mallam ya kara mata rashin kunya da Fitsara saboda Umar ya gaji ya sakota sai kuma yazo ya bar garin ta kare abunta kan Sakina..Alokacin hankalina ya karkata kan yadda Umar zai zo ya tafi da ita Madina har kiranye na saka an yi mai ammh ba Nasara hankalina ya kara tashi Lokacin da Sakina ta samu Ciki ta karayin barinsa alokacin ne na gane bayan ni acikin matan mallam ma akwai wata mai Buri irin nawa..Saboda mallaminmu ya tabbatar min da ita ke lalata duk cikin da Sakina take samu..!.
Anty Amarya kawai ake kallo wacce ta Runtse ido ta cigaba da Fadin"Dana Fahimci ko wacece naso nayi fito na fito da ita Sai dai ina sai ta nuna min In an shirye nake ita atafe ta kwana..Daga karshe sai ta nemi ta lalatamin Duka Shirina ta lankwasa komai ya koma kaina..awannan gabar na rasa madafa.sai da naga Umar ya Danu sannan su Hajiya ma haka sai Hankalina ya kwanta..Ban taba kawo ma kaina wani abu zai ya faruwa ba nan gaba ko da Hajiya ta Dauke Amina nayi Tunanin maiduguri ta kaita sannan Daga baya sai mukayi Tunanin ba auran ne sannan Balaraba kuma hankalinta ya karkata kan Sa"idu da ya koma sai abunda tace mai ni kuma ma samu Natsuwa tunda Umar yazo ya tafi da Sakina sannan Sarood bamu da damuwa akanta Sakina tajata ajiki da farko da sai da ta riga ta mata illah taja baya da ita..Sannan Mallam ya tabbatarmin dacewa sai dai ta gaji da zama dashi araba auran sannan ita kanta Aminar banmu taba Zaton wani abu zai shiga Tsakaninta da Umar har ta samu Ciki ba Shiyasa muka bar wannan Gibin bamu Cike ba..Na rantse har ga Allah Sakina bata da Laifi nice idona ya rufe da Cikar burina ammh ita bata san komai ba,sai soyayyar Mijinta da kaunarsa komai ta aikata ni ce Sila..Ni ce silar duk abunda ya faru..Don Allah ku yafemim..!
Sai kuka har da Shasaheka Falon yayi shuru sai tashin koke koke Mallam kansa na kasa yana ta Salati kansa ya Daure acikin gidansa acikin zuru"arsa Shirka ya samu wajen zama bai taba Sani ba..?
Bai sani ba sai da Hajiya da Danmallan suka zo suka same shi da mganganu wadanda ya kasa gasgasta su ya rude ya shiga Dimuwa Sannan alokacin ya kasa gasgasta mganarsu ammh yaji Daga Bakin da bazai mai karya ba Hajiya da Umaru...sannan Amina bazata taba fadin Wani abu kan Balaraba ba indai ba Gaskiya bane..ita kanta Hajiya ta shiga Rudani sanda Danmallan yake sanar da ita abunda Amina ta Fadamai sai dai bata ji ita kadai ba,ta tarasa suka isa gaban mallam ya sanar dasu abunda Amina ta Fadamai alokacin zuciyar Mallam ta raunana matuka tundaga wannan Lokacin baya barci Damuwa da bakincikin irin wannan abunda yake faruwa acikin iyalansa bai kara barinsa ya runtsa Dakyau sannan tun alokacin jikinsa yayi sanyi da bai Taba yi ba.
Danmallam ma ya girgiza da jin wannan al"amarin ballatana mallam..?
Hajiya kuwa duk ta san wani abu sai da labarin Balaraba ya girgizata.
Dukkansu shuru sukayi da mganar Suna jiran wannan ranar da dukkan sirrin Boye zai fito Fili.!
Baba Mallam ya Dago kansa Rawaninsa ya jike da Zufa duk da Sanyin A.C dake cikin Falon Cikin son ya kara Tattabarwa yace"Wacece ita wacce take Lalata Cikin da Sakina ta samu..?
Muna so mu santa sannan mu ganta..Allah ne ya nufemu da Sanin Ainihin Fuskokin wadanda muke Zaune dasu..!
Yafada cikin raunin murya raunin da ko Hajiya bata sam mallam dashi ba.
Anty Amarya zatayi mgana kenan sukaji muryan Hajiya Uwani Daga Bakin kofar Falon na Fadin.
"Gani nan..!