← Book details Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 105

Sashe 20

Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ita kuwa mamanmu Rana Tsaka kawai hanne tazo tace Hajiya tace ta bada Sako zasu wajen Amina..
Ita har ga Allah mantawa ma take da wata Amina kudi kuma tabi ta kansu  Shiyasa ta Dauko wannan Turaran Tsinke wanda mamata ma ta bata shi ya Dade bata taba amfani dashi ba tamikama hanne domin bata taba Zaton Sa"idu yayi zencen ya bata kudi da Hajiya ba. ganin suna ta Murna yasa batace komai ba gwara Hamidan taje ta gano wani irin Halin da Amina ke Ciki don ta tabbata Sakina bazata mata wasa ba ita fa a gayyas gida yanzu ya Rage daga ita sai mijinta Jawaad yanzu in Aba ya Dawo yadaina zuwa saboda samunsa tayi tajamai kunni yaro kuma da Tsoro ko Aba ya Dawo ko ya kirasa daya zo sai yace yana da Homework sai ya tafi hakan yafi ma Mamammu Duniyarta take so taci ita kadai bata san Takura.

*Janafty*
[10/19, 6:19 PM] +234 810 431 4972: *TFZB2009*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad'ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*

Hamida da Hanne cikin rawan jiki suka gyara komai Hanne ta share falo ta goge shi tas hamida kuma ta kintsa Kitchen din ta wanke kwanukan da suka bata ta goge kitchen lokacin har an fara sallar mangariba a masallatai yasa suka wuce dakin da Amina take suka isketa Ta fara salla,suma alwalan suka Dauro suka zo suka jera da Amina suka tada salla har suka idar Amina bata musu mgana ba suma ganinta cikin wannan yanayin yasa suka mata shuru.
Tana ganinsu suna hada kaya sai ranta ya kara baci Haka kurum take jin wani zafin zuciya wanda ko a baya ba irinsa take ji ba tasan dai tana Saurin Hasala ammh Bata da Saurin Harzuka kamar na yanzu sai ta Danganta haka da Tafiyar su Hanne Abunda bata sani ba wannan zafin zuciyar da aka kara mata ne maimakon tayi shi ga wanda akayi Domin sa sai ya kuskuremai Bashi a kusa da ita sai abun zai tsaya ga wanda ke kusa da ita da kuma wanda ke bata mata rai a kusa.
Sallar da tayi ne ma yasa taji dan Dama Dama ammh ranta yagama baci da abunda Sakina tayi mata yau ji take yi daman ta Tabata da sunan daambe da ta gane bata da wayau a yadda take jin kanta da karfi sai sun kwashi yan kallo domin karfin jikinta ya Dawo sannan ta warke kasanta ma batajin wani ciwo ruwan zafi da mgangunar nan sun tainaka mata wajen dawowa da ita Daidai shiyasa ko su Hanne basu Fahimci komai ba tota ina ma zasu gane..?
Amina ta fi su Budewar ido kan irin abubuwan nan saboda ita tana karance karancen Littafan hausa su kuma fa dukum ne su basu riga sun san wasu abubuwan kamar yadda ta sani ba.
Suna cikin Hada kayan ne suka ji knooking daga kofar falon Amina ta Dago tana kallonsu hanne ma ta kalleta kafin ta mike tana fadin"Ina ga Idi ne..!
Ba jimawa sai ga shi ta dawo tana Fadin"Shine Hamida..Hajiya tace maza maza ya Daukomu gobe akwai makaranta..!
Hamida batace komai ba ta Zura Hijabinta haka Hanne suka Dauki Ledan kayansu Hamida ta kalli Amina Dake Zaune tana kallonsu tace"Amina mu zamu tafi..
Amina tayi kamar bata ji su ba kuka taji yana neman tasomata Hanne ce Cikin karfin hali tace"Kiyi hakuri ai gobe zamu biyo mu Dauke ki..Ki shirya da wuri..!
Hamida da Hanne suma karfin hali suke kada su yi kuka ganin yadda Amina Tayi ganin ta musu banza yasa Hanne taja Hannun Hamida suka Fice Daga Dakin Amina na ganin haka ta mike Zaraf ta biyosu falon tana Fadin"Yanzu wai tafiya zaku yi..?
Ku bari gobe mana basai mu tafi makarantar tare ba..!
Hanne tace"To ai uniform din mu na gida kuma kinga Hajiya ce ta aiko a Daukemu..!
Amina bata kara mgana ba kawai ta Juya ta koma Dakinta ta Zauna gefen gado sai kuka wiwi kamar wacce aka Daketa Tana jin karan Bude get tasan su Hanne sun tafi kawai sai ta kwanta Saman Cafet ta cigaba da kukanta kuka mai Cin rai rabin kukan na kewa ne da Zaman kadaici rabin kukam kuma na kuncin zuciyar da ta rasa Dalilinsa wani Kululune ya Tsaya mata  arai yaki wucewa tana Tunanin in tayi kuka zata samu sauki.

Sakina kuwa ko da ta shiga Dakinta ko gani batayi Ranta ya gama baci tana Tunanin karamar yarinya kazama kamar Amina ce zata tsaya tana Zaginta Lalle sai ta gane bata da wayau Zata Kira Habibi ta Fadamai Rashin kunyar Amina sai ya Dauki mataki akanta domin ita bazata iya Zama da ita haka ba Allah nagani.
Wayarta ta Dauka ta kira Lambarsa ta Saudiya ta shiga sau biyu bai Dauka ba ta Duba Lokaci bakwai Saura na Dare su achan zai zama tara da wani abu kenan bai isa ya kwanta ba Duk da Tun da ya tafi sai jiya ta kirasa suka gaisa bai tsawaita mganar ba yace mata yana Aji ne in ya koma gida zai kirata kuma bai kara kiranta ba.
Ganin bai Dauka ba Sarood ta kira ita kan ta Dauka suka gaisa take tambayanta Habibi ta sanar da ita baya nan ya tafi Cikin gari masallaci Har yanzu bai shigo ba.
Sakina ta gyara zama tana cema Sarood  ta rokar mata Umar don Allah ya zo ya Dauketa yaki komawa da ita Madina Sarood tace mata kawai zata mai mgana da haka suka rabu Sakinar ta Lura kamar Sarood din bata son Wata Doguwar magana da ita tana sota kawomata Labarin Amina sai tayi Saurin Dakile mganar da cewa Tana girki ne kada ya kone..
Abunda bata sani ba ita kanta Sarood din tunda ya Dawo sama sama suke domin daman kafin su tafi sun yi Rigimar tahowa tun Tarkon da Sakina ta Hadama mata ita kuma ta Fada har sai da Mahaifinta ya shiga mganar To kishi da kuma takaicin abunda ke Faruwa Tsakaninamsu ya Rufemata ido gani take yi yana chan yana jin Dadinsa da Sakina da Amaryansa ita kuma ya barta anan ita bata ga Tsuntsun ba ga Tarko shiyasa taso ta Biyosa batare da sanin ko iyayanta nata ba Sai dai kalmar daya fadamata na sai tazo ne ya bata tsoro yasa ta fasa zuwa Tasan Halinsa kaifi Daya ne.
To kwana Hudu Tsakani ya Dawo Tunda ya Dawo ta sakamai Rigimar ita bazata yarda ba, da gangan yake yi Ba wai bazai iya kadaicewa da ita bane meyasa shi da Sakina Lafiya kuma gashi har yayi amarya itama tasan ai lafiya kalau meyasa sai itane bazai iya Raba ba .
Alokacin akwai gajiya tare da shi,Shiyasa bai biyemata ba sannan kuma ta wani Fannin tana da gaskiya ta wani Fanni kuma bata dashi Saboda ai ba Laifinsa bane sai da yace su sanar da manya mganar in da cutarwa tace taji ta gani sai kuma Daga baya ta Bullo da wata mgana Ba domin ma Su din ba su cika yarda da Sihiri ba, da haka yasan zatace Duk da shima lamarin ya bashi mamaki ammh bai Taba Zargin wani ba ga Allah kadai ya Dogara shiyasa yake Neman waraka daga garesa..!

******
Chapter 20 · 0% Book details