← Book details Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 105

Sashe 40

Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Mamanmu da izinin Lahi sai tayi mutuwar wulakanci sai tayi mutuwar kaskanci wannan Duniyar datake Fatan ta samu bazata taba cinta ba Har Abada tunda har tayi sakacin Datasan sirrinsu tayi alkawarin sai ta Daidaita Rayuwarsu daga ita har Anty Amarya kuma da yardan Allah zama da ya Danmallan yanzu ta fara Zama Daram Kuma Haihuwa da izinin Lahi indai Allah ke badawa sai ta Rokesa ya bata Ta Haifar masa dozin yan Bakinciki da mahasada sai dai su Fadi su mutu Allah Sarki bawan Allah yana chan yana aikinsa a nan an saka sa agaba Allah Sarki Hajiya da mallam kuna Zagaye da makirai da mugaye baku sani ba.
Ita ne nan zata zama sillar Tonuwar asirinsu.
An riga anyi walkiya ta gansu.
Sannan an Dade ana ruwa kasa tana Shanyewa..
Ita nan Amina Aminene ikon Allah badai ta mutum ba sai ta Allah kainuwan Dashen Allah indan Rana ta fito Tafin Hannu bai isa ya kareta ba..Daya bayan Daya sai sun tsinci abunda suka shuka wannan alkwarinta ne..!
Kukan da Amina bata samu tayi ba sai yanzu ya kwace mata sai da Filon Datake kwance akai ya jike da Hawaye kanta ciwo yake yi Idanuwanta sun mata nauyi ga Cikinta na murdamata Har da yunwa tana jin Hajiya ta shigo Dakin bayan ta Dawo daga Falon mallam sukace bata jin Dadi ta shigo ta Dubata ita kuma ta Tusa kanta cikin Hijabi tayi Luf kamar mai barci har ta fita tana fadin Ta samu barci.
Duk tana kwance taji Su Hamida sun shigo sun yi sallar mangariba sai alokacin Hajiya ta leko tana Fadin"Hamida ku tada Mamah mangariba tayi..!
Hamida ta mike ta isa wajen Amina tana tashinta kafarta tataba Taji Jikinta kamar wuta ta Dago tana Fadin"Zazzabi ya kamata jikinta Zafi..!
Hajiya ta kariso Dakin tana Fadin"Asshsha..Mamah Daure ki tashi kiyi sallah sai kici wani abu ki sha mgani..!
Dole Amina ta mike Hajiya sai da ta Tsorata da ta ga yadda idanuwanta suka koma Cikin wani yanayi tace"Amina meya faru kike kuka kinga idanuwanki yadda suka kumbura kuwa..?
Amina ta mike Zaune tana fadin"Hajiya Yaya na tuna..Sai na fara kuka sai kirjina ya fara ciwo da kaina sai Zazzabi ya kamani..!
Daganan kawai ta saki kuka Hajiya ta Dafa kanta Cikin Tsausaya tace"Addu"a zaki mata in kin Tuna ta kin ji ko mamah ba kuka ba..?
Kai ta gyada tana kara sharan Hawayen wasu na ambaliya ita ta mike ta kama Aminar da Jikinta ke Rawa ta kaita Tiolet ta barota ta Fito tana kallon su Hanne da Jikinsu yayi sanyi tace"Zo ki kar ban mata magani ke kuma Hamida shiga kitchen ki zubo mata abinci ga Jawaad ma chan afalo ki zubamai yaci kafin yayi barci.!
Da toh suka amsa mata ta fice suka bi bayanta Hamida tayi yarda Hajiya tace ta Zubama Jawad Jallop din Taliya da Miyar kifi ne ta Zubama Aminata kaimata ta iske tana Sallah a Zaune Hanne ma ta kawo mata mganin da Ruwa suka koma Falo suka barta kada su Dameta.
Tana Idar da sallah ta zauna sai kuka take yi ta rasa addu"an ma da zatayi kawai sai ta Daga Hannu tana rokar ma Mamanmu tabewa da bala"in Duniya kala kala tanayi tana kuka Kafin ta kife kanta ta cigaba Tana wajen aka kira isha"i daga Zaunen ta yi sallar ko abincin bata kallah ba sai da taji kamar Hajiya zata shigo sannan ta Jawo Filet din ta fara ci Turawa kawai take yi ko Rabi bata ci ba Cikinta ya Cuse zuciyarta ta fara tashi ta Nufi Bayi a guje sai amai sai da ta Amayar dashi Duka sannan ta koma gefe tana maida numfashi koiya Fitowa batayi ba sai da Hamida tazo ta fito da ita ta iske Hajiya da Hanne afalon abincin tace a Dauke a Hado mata Tea mai kauri to shi ta dan samu ta sha ya Zauna ta hada da panadol Hajiya ta fice zuwa shashen mallam ta Sanar dashi cikin wani yanayi yace Allah ya Sauwake in ba sauki gobe sai Hajiya ta kaita asibiti tun abunda ya Faru ne Dazu Mallan bai Saki ba har yanzu..!
Awannan Daran yadda Amina taga Rana haka taga Dare domin barci ko barawo bai Saceta ba ga kuncin zuciya ga Zazzabi Cikin Dare kaf Abunda ke Cikinta sai da ta amayar dashi kafin Safe Jikinta yayi zafi sai rawan sanyi take da Haduwar Hakora sallar asuba ma Dakyar ta iya yi tana neman Faduwa Hanne ta jira sai da Hajiya ta Dawo daga Shashen mallam ta Fada mata cewa tayi su sauya ma Amina Hijabi bari ta Fadama mallam ya ma Idi mgana yakai su asibiti.
Mallam na jin jikin Amina yayi zafi Hankalinsa ya tashi ya Kira Idi a waya yace yazo ya kai Hajiya asibiti ba Dadewa sai gashi Lokacin Hajiya har ta Shirya Amina ko Tafiya bata iya yi Saboda yadda Jikinta yayi zafi Hanne da Hamida suka riketa har Bakin mota ta shiga Suka Bita da fatan samun Sauki Cike da Tsausayi mallam ma Sai da ya Tsausayamata ganin yadda ta koma Cikin kwana Daya yace su Hajiya su yi gaba komai kenan ta Kirasa.
Kafin su tafi sai da Hajiya tace su Hanne su shirya su tafi makaranta Harda da Jawaad suka amsa mata da Toh suna masu Tsausayin Amina.
Suka koma Shashen Hajiya suka yi wanka suka karya suka yi shirin tafiya makaranta Harda Jawaad sai da suka fito ne suka ga Aba suka gaisa sai Lokacin ya rike Jaawad yana Fadin ya yi musu yaji shi da balaraba ko Mallam na wajen yace to yaga su Hamida sun dawo ina zai zauna in da ba kowa abunda mallam bai sani ba in Aba baya ga Jawaad bane yanzu mancewa ma yake yi dashi.
Hamida ta shiga gidansu ta gaida mamanmu ta sameta cikin kwalliya kamar wata yarinya ita abun ma sai ya bata mamaki sama sama suka gaisa ta shiga Dakinsu ta Dauki littafinta na Biology data manta Dashi bata ma samu Fadama Mamanmu Amina bata da lafiya ba Shidai Mallam ya sanar ma da Aba sai dai ba gida ya koma ba gidan gona ya wuce Shiyasa Mamanmu bata ji ba Sannan a matan mallam ba wacce ta Bude shashenta ma ballatana tasan abunda ke faruwa..!
Chapter 40 · 0% Book details