Sashe 25
Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mamanmu na kitchen tana soya kifin da Aba yaba Jafar ya kawo Dazu wayarta Dake tsakar gida kan Tabarma ta Dau kara alamun kira Gidan ba kowa sai ita kadai Hamida suna gidan Amima jawaad kuma sun tafi Hadda.
Burin Mamanmu ya cika ita kadai ke juyi a gidan Sa"idu sai abunda tace akeyi sai kuma an nemi Shawaranta.
Fitowa tayi da Sauri bayan ta juya kifin Dake kan gas kada kafin ta Dawo ya Kone.
Tana Daukan wayanta taga Madina ke kiranta sai da gabanta ya fadi Bata rai tayi afili ta Furta"Har Abada madina baza ta barni na Huta ba
Haba wannan kawwazzaba dame tayi kama mtswww..!
Ta ja wani Dogon Tsaki kafin ta Daidaita kanta ta Daga kiran tana Fadin"Buhun Sikari baki Farin banza ba..!
Dagachan bangaran Anty Amarya ta Katseta da Fadin"Ba bu abunda zaki Fadamin Ya sanyayamin rai Dayyaba..Ki ma yimin shuru kawai..!
Mamanmu ta marairaice kafin tace"Me kuma ya faru..?
Allah yasa ba kwabarmu ce zatayi Ruwa ba..!
Anty amarya tace"Kwabata dai Zatayi Ruwa Dayyaba...aike kin samu abunda kike so shiyasa kika maidani Wata Shashasha ko nema na baki yi Dayyaba Tunda na gama Taimaka miki kin samu Sa"idu a Hannunki ni kuma kin kasa taimakamin nawa Burin ya cika ko..?
Ni ban raba Maallam da Sa'idu ba sannan ta bangaran Sakina har yau ba wani mgana mai Dadi..!
Mamanmu ta Harari wayar kafin tace cikin karyewan murya"Haba Madina meyasa kin cika gaggwa ne..?
Kin Tsaya na gayamiki irin kokarin da ni ke nan ina yi miki akan abubuwa su Daidaita kuma da kike Fadin na Samu Sa"idu ai ban ga samunsa ba Domin har yanzu akwai rina akaga Hajiya da mallam sun sha gabana..mganar Sakina kuma ai mun gama mgana kince zaki sa ka mallam yasa turama danmallam son ko ya tafi sai ya Dawo ya Dauketa sannan mu na Fatan Zata samu ciki kuma zai zauna Zata Haifesa da yardan Allah mganar Shegiyar yarinyar nan kuma Amina sai dai su mallam su gaji su Raba bazai Taba wani amfani ba..!
Sai alokacin Anty Amarya taji ta dan Sauka Cikin Saukan Numfashi tace"Dayyaba ni Hankalina yaki kwanciya gani nake yi abubuwa duk suna ta lalacemin Tsarina duk ya lalace..Umar din ya tafi ni Kawai Burina ya Dawo ya Dauki Sakina su koma,in har ya tafi mallam yace ba lalle ya dawo nan kusa ba kinga mallam da Hajiya haka zasu gaji da ganinta ahaka su raba auren daman wanchan balarabiya Hoto ce itama in ta gaji zata kara gaba ne..
Mamanmu tace"Sosai ma ina amfani Zama da miji Hotiho ba wani amfani ina mai Tabbatar miki bazata zauna ba..Ki kwantar da Hankalinki Saura Kiris burinmu ya cika kada ki manta Sakina ba Juya bace tana samun cikin yana Barewa ne..!
Anty amarya tace"Dayyaba shine abun Damuwata ko an samu cikin baya Zama na fara Tunanin akwai wani a kasa..!
Mamanmu tace"Ko..?
Kanar na menene..?
Anty amarya tace"Ciki wajen sau Hudu da an sanu sai ya lalace anya Dayyaba..?
Mamanmu tace"To kin sa malam ya Duba mana kuwa..?
Tace"Eh ya Duba yace bai ga komai ba..Ammh ni haka kurum nake ji akwai wani wanda muke Tufka Daga Gefe yana mara warwara ko shakka bana yi.. kinsan daman ya taba Fadamin acikin matan mallam akwai wacce itama bata zauna ba..bai dai Fadamin sunan kowa ba.
Mamanmu tace"to wa kike Zargi..?
Anty Amarya tace"Cikin matan mallam ne dai..Ko Haj.Nasara ko Hj.Uwani..Akwai wacce acikin su bata so mu cimma namu burin..!
Mamanmu ta zaro ido kafin tace"in ma sune to saboda mene..?
Anty amarya tace"Saboda cikar Burinta itama..Kamar yadda muke son mu cimma namu Burin..!
Mamanmu tace"Tabdijam akwai kura Tsugunno bata kare mana ba..!
Ni fa basu nake zargi ba ina Tunanin ko dai Hajiya ce bata so Sakina ta Haihu..?
Anty amarya tace"Ba Hajiya bace..Bata yar da za"ayi ta hana Sakina Haihu wa kada ki fa manta Umar D'anta ne..zata fi kowa son ganin kwansa a duniya..!
Mamanmu ta jinjina kai kafin tace"Kuma fa hakane..!
Ni ban ma taba kawo wannan Tunanin ba sai da kika Fada na gane zai iya Faruwa..!
Anty amarya tace"Ai ki bar mugu..Bai da kama Dayyaba..Da mugu nada kama da Tuni Sa"idu da ya"yansa basu baki Dukkan yarda ba..Da mugu nada kama da Yaya bata taba Sakin miki Ragamar ya"yanta ba har Abada..!
Mamanmu ta bata rai kafin tace"Bangane ba..?
Ki sa min jaye mugaye zaki ce..!
Anty amarya tayi wata Dariya kafin tace"Ban kai ki mugunta ba Dayyaba. ina mai kara gayamiki ban kai ki ba..Domin ko ni sanda kika zomin da Fuskarki ta Dayyaba domin mu Hada Hannu na Girgiza ballatana Sa"idu da ya"yanku..?
Ina mai Tabbatar miki kiji Dadinki yanzu ammh in alalan geren mu ya tashi yin Ruwa da Tsami wlh naki sai yafi Nawa Tsamewa..!
Mamanmu tace"Da izinin lahi bazan ga haka ba..Ni Dayyaba Nasara na sani ba Faduwa ba Madina..!
Dariya tasake yi kafin tace"Muna fatan haka yanzu ba wannan ba yaushe zamu hadu..?
Ya kamata mu sauya Tsarin mu sannan mu san ta yadda zamu gano wanda ke kokarin batamana aiki..!
Mamanmu tace"Ina so mu hadu bana samun Lokaci ne gida ba kowa sai ni kadai..Hamida bata nan tana gidan Amina..!
Anty Amarya ta Zaro ido kafin tace"Wata Aminar..?
Mamanmu ta tabe baki tana fadin"Wacce kika sani mana..Bakisan suna gidan Amina ita da Hanne ba Tun Ranar alhamis da yammah Hajiya ta turasu..!
Anty Amarya ta mike Daga Zaunen Datake gefen gadonta tana fadin"Kan burauba..Bansani ba..Naji dai jiya Sa"adatun na fadin bata ganinsu a Hadda ban maida mganar mai ma"ana ba shiyasa ban bincika ba..Na Shigesu Dayyaba Sakinarma tun aranar da Umar ya koma tana Dutse..!
Mamanmu tayi shewa kafin tace"Au to..Aiko tayi wauta suna chan ta bar musu gidan suna Yadda suka ga Dama..!
Anty Amarya bata jira cewar Mamanmu ba ta yanke kiran ta bar Mamanmu da Hararan waya Lokaci Daya ta Ijiyeta nan kan Tabarma ta koma Kitchen tana fadin"Kawai kin zo kin Tsaidani kan mganar banza..Badai nawa Burin ya cika ba..Ban Damu ba..In dai ni na samu abunda nake so Uban kowa kada ya samu..!
Bana kaunar Amina ta Dawomin gidan nan zata lalatamin Tsarina Yadda tatafi tatafi kenan har Abada Shegiyar yarinya mai kama da Uwarta..!
Haka tayi ta manganganu ita kadai.tana ciga da suyan kifinta Duniya tayi mata Dadi.
Anty Amarya kuwa Lambar Sakina ta Kira sai da kusa katsewa ta Daga ko Sallamanta bata amsa ba ta fara Fadin"To shashassha..kina nan kwance ga Amina chan da su Hamida suna yadda suka ga dama da gidanki. !
Sakina na kwance ne sai da ta mike tana Fadin"Bangane ba.?
Nan Anty ta shaida mata abunda mamanmu ta fadamata Sakina tace"Kuturun uba.... to ubansu zasu ci na kulle ko"ina har Kitchen fa..!
Anty Amarya kamar ta Zageta haka taji cikin Tsawa tace"Dayake ke kadai ke da key din gidan ba..?
Karki manta Uwarsa ma na dashi kuma na tabbata sun tafi dashi ki cigaba da zama agidan da nayi Burin ki Rayu ke kadai tun ba"a je ko"ina ba yana neman ya zama ba naki ba..!
Daga haka ta Datse kiran tana Faman Huci Dagachan Dutse kuwa Sakina ta Diro Daga kan gado ta Fada wanka sai yanzu ta Dawo Cikin Hayyacinta.
Allah ya taimaketa akwai wani yayanta zai taho kano shi ya Daukota har Gumel har kofar gidanta ya ijiyeta sannan ya wuce alokacin Shida na yammah har tayi san da ta abuga get din megadi yazo ya Bude mata bata Tsaya amsa sannu da zuwansa ba taja akwatinta ta nufi Cikin Falon.
Amina da Hanne suna Zaune Saman Cafet hamida na Saman kujera suna Hira sannan ga filets nan da suka gama cin wainar Fulawarsu nan da Ferfesun naman rago da sukayi ga Kofuna ga abun maltinan da suka gama sha Falon dai kaf ba Kintsi Saboda tunda suka gama suka koma gefe suna Hira sun ma manta yau zasu koma gida Tsabar yadda Rayuwa tayi musu Dadi gaddamace ta Sarke Tsakanin Hanne da Amina kan lokacin Bikin su ya Abida Amina na Fadin yadda Hanne ta manne ma Sa"adatu saboda yar"uwatance ita kuma Hanne tana kokarin nuna ma Amina Daga su har Sa"adatu duk Dayane hamida kuwa bata sako bakinta ba sanin Halin gaddaman Amina ko bata da gaskiya bata saki. kwata kwata basu san Sakina ta Shigo ba ashe ta Dade Tsaye taba Bin Falon gidanta da kallo yadda ya zama.
Ranta in yayi Dubu ya baci akwatin Hannunta ta saki ji kake garam lokaci Daya ta Rike kugu tana fadin"Kutumar Uban chan Falo na ne ya koma kamar gidan abinci?
Lalle yau zaku gane baku da wayau duk sai naci Ubanku daga ku har kazamar data jawo ku..!
Ta karishe fada tana Cire gyalenta ta Ci Darama dashi Tana jifan su Amina da wani matsiyancin kallo wadanda sai alokacin suka san da wanzuwarta afalon Hamida da Hanne ne suka Tsorata Amina kuwa ko ajikinta itama kallon rainin ta maida ma Sakina kafin ta tabe baki ta kauda kai.
Hanne ce da Hamifa suka mike da Sauri Jikinsu na rawa Hanne na faman Fadin"Sannu da zuwa Anty Sakina..!
Ita kuma Hamida ta fara Tattara filets din tana fadin"Kuyi hakuri yanzu zamu share mu gyara ko"ina..!
Sakina ta kariso Falon tana Hararansu Lokaci Daya tana fadin"Dilla kumin shuru..uban wa ya baku izinin zuwarmin gida batare da sanina ba.?
Hannu hamida tabi da kallo kafin tace"Kan uba har kitchen dina ma kuka Bude kuka shiga kuna min kazanta..?
Yau zan ga wanda zai Rabamu daku acikin gidan nan..!