← Book details Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 105

Sashe 62

Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kitchen ta shiga suka gaisa da Saude ta Tambayeta sai tace suna cikin Fridge,tana budewa ta gansu tasan aikin ya Aisha ne a kitchen din ta samu Roba ta Hada rama da Zogalen ta saka yaji da kuli da magi taci ta koshi ta kora da ruwa ta koma Daki ta iske Yakaka na sallah itama alwalan ta Dauro tazo tayi sallah.
Tana Idarwa Yakaka sai kallonta take yi Amina ta tura baki tana Fadin"Wai na Chanza miki ne da kike ta Kallona haka..?
Yakaka ta tabe baki tana jan Carbinta tace"Kya ji da gulmarki.
Amina tatashi ta Hau gado ta kwanta Domin ta gaji matuka badadewa sai ga su Dannallam sun shigo har Dakin yima yakaka sallama zasu tafi ta rike baki Tana fadin"Da yamman nan..?
Na zata fa sai gobe ga su Usmanu basu nan ai kwa jira su kuyi Sallama ko..?
Aliyu yace"zamu yi musu a waya Baaba..Saboda wajen aikin mune akwai matsala..!
Jin haka yasa tace"In hakane kuna da gaskiya ai ma mungode Allah ya bar zumunci Allah kuma ya kaiku lafiya..!
Suka amsa mata da Ameen Ameen Aliyu 5k ya bama yakaka Umar ma haka ta ki amsa suka matsa sai data amsa tana ta musu godiya,Da kuma godiyar Ruwan zamzam da Dabinon da suka kawo musu jiya taji Dadinsa matuka.
Danmallam ya mike yana kallon Amina data juya baya tana barci yace"Baaba barci take yi ne..?
Yakaka ta kalli Amina kafin tace"Waya sanin mata ko duk tana jin mu..?
Ko da fa kuka shigo sai wani Ture turen baki take yi kalli ledan chan data shigo da ita inda ta watsar..!
Mirmishi yayi kafin yace"Shikenan tunda ta kwanta a kyaleta zamu yi waya..!
Yakaka taso a tada Amina Danmallan yace ta kyaleta har Waje ta rakasu tana musu godiya sai da taga motarsu ta fita daga gidan sannan ta koma cikin Gida Daki ta koma ta leka Amina taga barcinta take sha sosai Yakaka na yar Dariya tace"Yar nema waya gayamiki Borno gabas take..!
Ledan data shigo dashi ta Duba duk kayan Zaki ne ta tabe baki tana Fadin"Shi mai ya kaisa biye mata..?
Ai munan hanata shan zakin nan muke wajen haihuwa nake jiye mata zaki yayi mata yawa ajiki mu shiga uku..!
Guda Daya ta Dauka ta Bude ta faraci tana Tabe baki sai gashi ta Cinye har da kari tana Fadin"Abun kuma Dadi ne dashi..!
Su Aisha sai dai suka Dawo sukaji Tafiyar su Danmallam ya Aisha bataji Dadi ba sai da ta Kirasa a waya sukayi sallama Amina kuma har Lokacin bata tashi ba tana ta barcin gajiya yau din Daga yakaka har Aishan ba wanda ya Takuramata ko miye Dalilinsu..?
Sai da suka Dauki Hanya Sosai Sannan Aliyu ya juya yana kallon Danmllam Daya kwanta jikin kujeran mota yayi shuru kamar wani mara Lafiya.
Aliyu yayi dariya kafin yace"Ko zan zauke ka ne ka koma..?
Umar ko kallonsa bai yi ba ballatana yasan yana mgana sai da ya kara saka Dariya sannan ya gintse fuska yace"Shehi How comes abubuwa suka faru haka banda Labari..Amina nada Ciki dawowarta Abuja da sauransu..?
Bamu taba mganar dakai ba..!
Yafada yana maida Hankalinsa wajen Tukin Dayake yi.
Sai alokacin ya Dago jin Aliyu yayi Serious mgana Cikin sanyinsa yace"Nima haka abubuwan suka zomin a bazata Aliyu..!.
Nan ya shiga bashi Labarin abunda ya faru,tunda ga farko har karshe ya karishe da Fadin"Hajiya ce ta kawo Aminan nan sannan ta hana Fallasa Cikin a wajen kowa Dagani sai ita sai mallan sai kai yanzu dana Fadamawa ko Baba Sa"idu mahaifinta bai san Amina dana ciki ba kuma baisan tana Abuja ba..bansa Dalilinta ba Domin Dagani Har mallam batace mana komai ba.!
Aliyu yace"Alamarin Allah ya wuce wasa Shehi..Ba wanda ya taba Zaton haka..!
Danmallam yace"Whl kuwa..!
Aliyu yace'"To Allah ya raba Lafiya..Hajiya kuma tana da Dalilinta na sani sannan ni kaina sai naga hakan is Better fa..!
Umar ya kallesa kafin yace"Meyasa kace haka..?
Aliyu yayi mirmishi idonsa na kan Tuti yace"Araina naji hakan da tayi shine Daidai sannan hauwasa na Fadin abunda babba ya hango yaro ko yahau Rimi bazai gani ba..!
Ko mgana Danmallam bai karamai ba sai suka bar ma wannan mganar suka shiga wata Hirar har suka iso gumel bayan Isha"i,Agidansa Aliyu ya ijiyesa ko shiga bai yi ba adaran ya juya Dutse.
Sakina tayi ta rawan jiki dashi yayi wanka yayi Sallolin Dake kansa yaci abinci yace zai kwanta Dole ta kyalesa Sarood daman tana Falo bata cusa kanta ba ganin Sakinar ta tare komai sai ta mata uzurin ai ita suna Tare wattani achan ita kuma na dan Lokaci ne.
Sai Washegari yaje gidan mallam su Hajiya suka gansa yace sai jiya suka Dawo ya tabbatar musu da Amina tana lafiya tace agaishesu da Aisha mallam yaji Dadin haka shi da Hajiya Duk da Hajiya tasan daman Amina Zata samu kulawa sosai a inda ta kaita
Hanne da Hamida ma ya basu Sakon Amina na gaisuwa,ammh ya gargardesu kada su fadama kowa yaje wajen Amina sukace bazasu fada ba Hankalinsu ya kwanta Tunda Amina na Cikin koshin lafiya.
Aranar Amina ta kirasa suka yi mgana ta Tambayesa ya suka sauka yace Lafiya lau basu yi wani mgana ba suka yi sallama Har alokacin Amina Haushinsa take ji baisan me yayi mata ba ita ko Tunda yace zai tafi bakin ciki ya isheta in ta tuna inda zai koma shiyasa tayi kwanciyarta kamar tana barci da zai tafi Ahalin idonta Biyu bata son tatashi din ne.
Shima ganin yanayinta sai bai matsa mata ba,shirin tafiya ma suka fara domin yana ta Cukun cukun nema musu Visa, cikin ikon Allah kuma an samu Visar da wuri zasu tashi nan da kwana Hudu tunda ya fadama Amina zai koma da Sakina da Sarood Amina ta Daina walwala a kaduna Ya Aisha duk tasan Dalili itama abun na Amina ma Dariya yake bata wani Lokaci kishi sosai take yi in kuma an ce tana son ya Danmallan tace atafau ita bata son shi.
Ana saura kwana Biyu su koma ta Tadamai hankali awaya tana kuka Dole washegari ya taho Abuja da kansa ya Tuko kansa sai dai suka kara ganinsa kwatsan jidalin Amina yayi kira,Ranar bai kwana ba ko Awa Hudu bai yi ba ya Samu ya lallashi Amina ta Daina kuka bai dai yi shagalinsa chan ciki ba sai dai ya sha Shagalimsa Daga sama kuma bata Hanasa ba sai ma ta taimakamasa,Da wuri ya tafi bayan ya bata kudade a hannunta saboda Tasowar wani abu Amina kuka riris take yi kamar karamar yarinya mamakinta kawai yake ya rumgumeta yana lallashinta yana Fadin"Da Hajiya zata bari da na tafi dake Amina ni kaina ina Bukatarki kusa dani..!
Baki Ta tura tana Hawaye tace"In ka tafi yaushe zaka Dawo..?
Yana rike da Hannayenta yace"Wlh bazan Dade ba ai nasan Halin da na barki ga kuma waya ZAMU dinga mgana da juna kin ji ko..?
Kai ta gyadamai tana share kwallah ya taimaka ya share mata Cikin salonsa Sannan ya kalleta Cikin ido yace"Zan yi kewar ki Aminata..!
Baki ta Turamai kafin tace kasa kasa"Uhm in guzumayen matanka sun barka kayi kewata ba. !
Yajita sai da ya Bude baki yana kallonta da Sauri ta juyamai baya yafa riga ya sani Amina kishinsa take yi dashi da matansa ba nawa wasa ba Na Sakina kadan ne.
Juyo da ita yayi ya kama bakinta ya tsotsa sosai sannan ya saketa yana Fadin"Ba ruwanki da matana..Ai nasan dasu nazo wajenki Tundaga Gumel Amina..?
In kikace haka sai naga kamar ban yi miki adalci bane .?
Ganin ya Damu yasa ta fada jikinsa ta Rumgumesa sai Hawaye tace"Kayi hakuri..!
Yana shafa bayanta yana fadin"Baki tabamin komai ba..Sai kuka ne kadai Tsiya na Dake kuma shima na yanke shawaran ki gayamin kudinsa na siyesa na Huta.!.
Tana Dariya tana Dukan kirjinsa yana Tayata ganin zai bata Lokaci yasa ya saketa yana fadin"MEENA zan tafi..!
Kanta na kasa tace"Allah ya kiyaye hanya..Allah ya tsareka. !
Ya amsa da Ameen cikin sanyinsa har ya juya ta rike mai riga ya waigo yana kallonta kafin ya sami bakin mgana ta Zo gabansa ta yi Dage ta kama Bakinsa da Hannayenta ta yi mai Dogowar sumba sannan ta a sakesa tana sharan hawaye ta shigo Tiolet ta kulle sai da ya tafi ta fito duk ta sha kuka ya Aisha da yakaka na mata tsiyan bata som miji tana kuka zai tafi sai ta kara fashe musu da kuka ji take yi kamar zata mutu shikenan sai tayi wattani zata sake ganinsa..?
In da ma shi kadai ne achan da sauki ammh har da matansa fa shine karin Haushinta..
Shi kanshi Danmalllan in za"a bashi Zabi Tsab zai ijiye sakina ya tafi da Amina sai da bamai zai fara ba Hajiya bazata taba yarda ba,Wlh har acikin Ransa yake jin mgana washegari jirgin yammah suka bi zuwa Jidda kamar an zare mai lakka haka yake ji bai da karsasashi kan tafiyar har su Sakina sun fahimta.
Anty Amarya dai sai hamdala domin Hankalinta bai kwanta ba sai da Sakina ta kirata tace sun sauka a madina sannan taji Ta Sauke numfashi ta gama da wannan bangaran yanzu Haj.Uwani zata nuna ma bata isa ba zasu goga shege ka fasa..!
Domin Taga alamar zata iya nasara akanta Tunda har yanzu Tare da Nazeem Aba ke komai abunda bata sani ba,Haj.Uwani ta fita sanin komai kan Dukiyar mallam,Domin zama take da Nazeem tana dukan ruwan cikinsa tana jin komai balle ma da Aba ya sakarmai bangaran Lissafi da Shigar kudi da Fitarsu Hajiya uwa ta gama Tsara taci nasara ma ta gama Domin ta fara hango kamshi hakan.
Chapter 62 · 0% Book details