Sashe 32
Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Wannan karon ba Anty Amarya kadai da Sakina suka shiga Tashin hankali ba harda mallam da Hajiya Tare da Uban gayyar Danmallam da kuma ilahirin Masoyansu sun tausaya musu bisa rasa wannan cikin ma a karo na hudu kamar sauran.
Mallam shi ya saka ayi ma Sakina gwaje gwajen mahaifa domin a Fahimci inda matsalan take Dayake wani asibitin kudi dake cikin gari Anty Amarya ta kawo Sakina duk kudin da aka kashe mallam ya Dauki Nauyi sannan suna tsaye kan Sakina shi da Jafar da Nasir da ita kanta Hajiya da Aba din sakamakon Sakina ta Zubar da jini yasa sai da aka mata karin jini gabadaya yan"uwanta ne Anty Amarya ta kira tana kuka ta Fada musu wadanda ke kusa suka zo aka samu aka gwada jininsu sai Allah ya taimaka jinin kaninta wanda ke bimata yayi daidai shi aka diba aka sanya mata.
Sakina sai da ta kwana ta wuni sannan ta farfado ko ba"a fada mata ba tasan ta rasa cikin ta ma a wannan karon domin haka take yin indai zata yi bari tayi ta zubar da jini sannan ta Fice Daga Hayyacinta na wani Lokaci.
Sakina tayi kuka kamar ranta zai fita wannan karon Anty bata da bakin lallashinta domin ta Sare ta kuma kara yarda da Hasashenta na Tabbas akwai wanda ke lalata cikin Sakina akwai wanda ke neman shiga Tsakaninta da Cikar Burinta ko waye kuwa in ta ganosa sai ya gane bai da waye ita Madina bata fito ba sai da ta shirya.
Anyi ma Sakina gwaje gwajen da Mallam yace an kuma tabbatar musu da komai lafiya harta mahaifanta Lafiyalau ita Hajiya har tana Fadin ko kila Sakinar tana da Raunin mahaifa ne ammh sai likita ya tabbatar musu da Komai lafiya Sanadin barin dai bai gano wani abu ba sai a bar shi da Allah ke ikonsa Domin shi ke kashewa ya kuma ya rayashi alokacin dayake so Sannan Haihuwa ta sa ce ga wanda yaga Dama yake bamawa Haka Mallam ya dinga fadama Sakina alokacin Dayake mata Nasiha a daran Data cika kwana Hudu asibitin Daya kara zuwa Dubata shi da Hajiya da Daddare.
Hajiya ma ta kara da nata Nasihun Saboda duk mai imani in yaga yadda Sakina ta dawo sai ya Tsausayamata kuka kadai take yi,mganganunsu kwata kwata basu shiga kunnenta ba Hango kanta take a matsayin Bora duk Ranar da Haifarma Umar magaji ya kuskure kanta sannan ta Fara Sarewa da Tunanin Anty bazata iya ba Sannan wannan Burin nata bazai Taba cika ba Nasara kuma su daina Hasasota nan kusa tana da Nisa kafin su isketa bama domin haka ba itama Tana so ta Haihu sosai take son Taga ta Haihu sannan tafi so kowa Sanin yadda Umar ke son Haihuwa ya Fada mata ba Sau Daya ba sau Biyu ba,kawai yana da kawaici ne sannan addininsa yasa ya yarda da Allah ke yi alokacin da yaso shiyasa bai cika nuna Damuwarsa sosai ba..
Shiyasa har su mallam suka fita Sakina ma bata cikin Hayyacinta Anty ke kwana da ita tana kula da ita suna Fita Sakina ta Fashe da wani kuka mai karfi Daga karkashin ranta Anty Amarya ta taso zata riketa ta Daga mata Hannu tana fadin"Don Allah Anty kada ki hanani kuka ki bar ni nayi domin shine kadai zai sa naji Sanyin abunda ke damuna acikin Raina..!
Tafada tana Dakatar da ita da Hannu Dole Anty ta koma baya ta Jinjina kai gabadaya bata cikin natsuwarta Saukinta Daya yadda mallam da Hajiya da yan"uwan Danmallam ke Tsaye kan sakina da shi kanshi Danmallam din,arana ya kira fiye da sau Biyar yana tambayan Lafiyan Sakina Sannan ya Turo abokinsa Aliyu dashi ake ta Zirga zirga in bai zo yau ba zai zo gobe har da matarsa Aliya yazo Abinci kuwa baya zuwa hannu Rabbana da kwalayen maltina da kayan maarmari saboda karin jini ga ita Sakinar
Ta kira Dayyaba sun yi mgana gobe take so in kanwarta A"i tazo daga Dutse zata bar mata Sakina ta kula da ita zata koma wajen mallam tamai bayani so take ta gano wanda ke lalata mata aikin data wahala tayi shekaru tana Fata akansa in ko Zarginta ya Tabbata kan Uwani sai ta raina kanta sai ta Fahimci wacece madina ba marliya ba.
Tana gani Sakina na gunjin kuka bata da karfin gwiwan hanata saboda ta gaza Duka alkawarin data mata ta kasa cikamata,maimakon ta Fahimci Talalar da Allah yayi musu ta kare ne suke ganin sabawa akan lamarinsu ammh ina idonsa ya rufe gani suke a koda yaushe nasara tasu ce.
Suna Mota zasu koma gida Hajiya Dake gefen mallam ta kallesa tana Fadin"Mallam ka kira Danmallam ka yi mai Nasiha da Hakuri ko..?
Domin jiya da mukayi mgana yace min yana gida kwance bayajin Dadi..kuma ko shakka babu abunda ya faru ne ya tabasa kamar yadda ya taba Sakina wannan karon..!
Mallam ya muskuta kafin yace"Na kirasa da Safe munyi mgana..Sosai nayi masa nasihan na kuma tunasar dashi cikar imani shine yadda da kaddara mai kyau ko akasinta na horesa da yayi Hakuri ya jira kadan kila Tanadin da Allah yayi masa yana gaba ne Rashin hakurinsa sai ya bata komai..!
Hajiya tace"Hakane kan mallam..Allah yasa mu dace Allah ya basa zuru"a Mai albarka..!.
Mallam ya amsa mata cikin Damuwa a karkashin ransa yana jin Tsausayin Umaru ache kana neman rufe shekaru arba"in ko Haihuwan fari bakayi ba sa"o"insa ya tabbata Har da masu ya'ya goma wadanda sukayi aure da wuri ma kenan ga dai Amininsa Aliyu nan baya baya yayi aure ya"yansa Biyu tabbas yasan akwai Damuwa ammh bazai barsa ya nuna gazawarsa ba zai cigaba da Tunasar dashi Hakuri da Rayuwa a duk sanda tazo masa da kuma yanayin datazo maka sai ka saka Hannu Biyu ka karbeta.