← Book details Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 105

Sashe 18

Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Abun da ya kusa bashi Dariya Har da Vests cikin kayanta shi yaushe Rabon da ya ga ana sa Vest aransa yace shi ne madadin Bra dinta shi kadai yana wankin yana Dariya har alokacin in ya Tuna Haduwarsa da Amina sai yaji wani iri acikin Ransa yanayi ne da bazai iya Fasaara shi ba ammh yaji matukar mamakin yanayin daya shiga Lokacin kasancewa da ita ko shi yasa Aliyu ke son auran irin su masu kananun shekaru..? Yadan gano sirrin kadan duk da Abun bai wani Samesa Yadda yake so har yaji ya ishesa ba an Dai Taba kawai an bari shima Tabawan kamar kudirin Allah ne.
Tas ya wanke su ya Daureye ya shanya su saman igiya sannan ya koma Cikin gida ya Zage ya gyara falon ya Share saboda duk yayi kura saboda isar da akayi shekaran jiya..
Dakin da Amina take ciki ya koma har Lokacin tana barci Zagewa yayi ya shiga Tiolet ya wanke shi Tas ya zo kuma ya gyara Dakin ya share duk ya Gaji bayansa har ciwo yake yi bai zauna ba wanka ya shiga yayi ya fito ya Saka Jallabiya baka ya Dauki walet dinsa ya fita yaje ya siyo musu abinci da katan din Faro sai na maltina Saboda Amina da kuma Tafiyarsa.
Sanda ya dawo ta tashi Daga barcin Kuma tayi wanka batare da yace mata ba Sai dai kayan jiya ta maida sai yace ta Cire ta sauya wasu ita daman tayi wankan ne saboda ta Lura yadda yake son wanka kamar kwado koma batayi ba sai yace tayi shiyasa tayi ammh yaushe zata jure wannan aikin kamar wata yar ruwa..!
Atamfa ta saka Riga da Sikat sai Alokacin yake ganin Rashin girman Jikinta tsawo dai gareta ba Kiba,Ammh a shekarunta in da tana da manyan gabbai da Tuni tayi Jiki Tunda Hamida da Hanne sun fita Girma yan kirjinta yake kallo kamar yayi Dariya abun chan manne Lalle kwaila ce Tabbas kwailace ya aura kuma kwailan nan ne ta Daukesa Tsab Allah mai iko domin ya yarda da akace abun ba daga shekaru ne ko Girma ba..!
Chiips ne ya siyo mata shi kuma Ruwan zafi yace su bashi achan yazo dashi ya sha Tea da buredi ita kuma ta Dora da maltina tayi gatsa ta sha mgani da ruwa yace taje ta kwanta Haka ta mike tana Tafiya sannu sannu ya Bita da kallo Hankalinsa ya kwanta ganin har tafiyarta ta Fara Daidaita ya Fara Tunanin in ya tafi yau Amina bazata iya zama agidan nan ita kadai ba ita kuma wanchan baisan yaushe zata Dawo ba..!
Shi kan shi akwai gajiya ajikinsa yasa ya kwanta saman kujera sai barci sai gabda azahar ya farka Sauri Sauri yayi alwala ya tafi msallaci bai Tsaya ba Illah abinci da siyo ma Amina da kayan su Fruit ayaba kankana lemo da Sauransu koda ya dawo ta tashi tayi sallah tana kwance ammh ba barci take yi ba.
Inda yayi wanki ya koma ya kwashe kayan Tunda sun bushe ya kawo su Falo ya zauna ya ninke mata sannan ya Shigar mata dashi har Cikin Wardrope ya saka mata yana Fadin"Mai wanki duk bayan sati daya yake zuwa karba..Ki rika Hada kayanki wadanda suka kamata banda Undies nasan ba hankali kika cika ba sai ki Hadamai da Vest dinki..!
Kunya ta kama Amina taji kamar ta Nitse shikenan ita kuma ya gama ganin komai nata Zanin gadon ya Ciro ya kalleta yana Fadin"Tashi na Shimfida..Kije falo na siyo miki abinci da Fruit..!
Kamar zata fita sai kuma ta fasa ta kallesa yana kakkabe gadon zai shimfida Zanin gadon tace muryanta kasa kasa"Kawo na shimfida..!
Ko kallanta bai yi yace"Ki wuce nace..!.
Da sauri ta wuce har tana Hardewa sai da taji wani iri a kasanta duk da ya fara warkewa sosai ta ke tsarki da Ruwan zafi tana gani a littafan Hausa in haka tafaru kuma tana so ta warke shiyasa batayi wasa ba sannan kuma Ai da sukaje asibiti Dr haka ya fadarmuau hakan.
Tana fita ta jawo ledojin priderice sai kayan Marmari  Ayaba kadai taci sai kankana cikinta ya cika sosai mganinta na Dakin ita kuma tana jin kunyar komawa ba Dadewa sai gashi ya fito da mganin ya zauna gabanta yana Fadin"Matso na nuna miki yadda zaki sha kowanne..!
Ba musu ta matso ya nuna mata Duka kuma ya tabbatar da ta gane ya bata ganin bataci abinci ba ya Tambayeta tace sai an juma ta koshi.
Da kanta ta maballi mganin tasha ta koma gefe ta Rakube kanta na kasa shima bai bi ta kanta ba ya sha Kankana kadai ya mike ya bar mata falon ta Bisa da kallo aranta tace ashe yana da Mutumci wani lokacin..!
Wanka ya shiga Sauri Sauri yake yi Saboda yana so ya isa kano da wuri kuma Motar haya zai bi jirgin su karfe Takwas na Dare zai tashi zuwa jidda.
Sannan kuma wa zai kira yanzu yace mai bai tafi ba..?Kowa na da uzurinsa sannan kuma basusan an samu wannan Tsaikon ba,Duk da yasan sun neme sa a layinsa na Saudiya zasu ji a kashe layinsa na nan kuma bai kunna wayar ba yasan zasu yi Tunanin gajiyar tafiyace yasa bai Dora Layin ba yana da Tabbacin harda mallam ya Kirasa yaji ya ya sauka bai samesa ba..har ya shirya cikin Pakistan riga da wando masu ruwan madara yana
Tunanin mafitar yadda zai yi da Amina baza ta iya zama ita kadai ba sannan Hajiya bazata taba yarda ya maidata agida ba.
Tunanin kiran Hajiya yayi yace ko su Hanne ta saka idi ya kawo su yasan Aminar zata ji dadi da wannan Tunanin ya fito Cikin Shirin Tafiya Rataye da Jakarsa Amina ya iske tana Barci a zaune ya Dade yana kallonta karamar Fuskarta har ta Fada sai yaji Tsausayinta gashi zai tafi ya barta ba wani babba kusa da ita Allah yasa ma taji Sauki sosai.
Fuskar yaya yake gani a Fuskarta sai yau ya kara kare ma Amina kallo yaga ba inda ta bar yaya a kama,Baisan sadda ya Furta"Allah ya jikan ki yaya.!
Afili yana kara kallon Amina lokaci Daya yana kara ganin yarinta muraratun a kanta ganin har Biyu ta gota yasa ya karisa gabanta ya Durkusa yana Buga jikin kujeran Data jingina tana barci lokaci Daya da Kiran sunanta.
Firgigit ta mike tana Raba ido sai ta gansa a gabanta Tuni jikinta ya Fara rawa tana kokarin tashi ya Rike duka Hannuwanta yana fadin"Ki natsu mgana zamu yi..!
Duk da ta natsun ammh ta kasa kallonsa Kanta na kasa tana kallon yadda ya rike da hannunta sosai.
Cikin Taushinsa yace"Ya jikin ki..?
Fata kin sami lafiya..?
Kai ta gyadamai alaman eh Cikin bude murya kadan yace"Da baki zaki amsamin..!
Sai da runtse ido kafin tace"Eh da sauki..!
Kai ya kada kafin yace"Ba inda yake miki Ciwo..?
Kai ta kara dagamai kafin kuma da Sauri tace"Ba ko"ina..!
Shuru ya gifta na wani Lokaci kokarin Kwace hannunta take yi yaki Sakinta wani yanayi take ji Daya riketa shi kuma sai faman kai da kawon mganar yake yi kafin yayi shahada ya kira sunanta.

Amina..!
Chapter 18 · 0% Book details