← Book details Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 105

Sashe 7

Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sakina na zaune inda Umar ya barta taga ya sake fitowa cikin mamakinta sai taga ya nufi Dinning ya Dauki katon mug ya tsiyaya ruwan tea ya saka madara da Milo sai siga bata iya shuru ba sai da tace"Habiba yau kuma Tea zaka sha da madara..?
Saninsa tun abaya madara bata wani Damesa ba,Bai mata mgana ba taga ya Dauki mug din ya nufi Dakin da Amina take wajen kallonsa kadan ya Rage bata fado daga kan kujera ba sai da taga shigansa sannan ta maida kallonta acikin ranta tana fadin kan uba..!
Shi kuwa yana shiga ya iske Amina inda ya barta kwance tana numfashi Sama sama,Kai tsaye yace"Tashi zaune..!
Ba musu ta mike tana wani karya wuya saboda yunwa mikamata Kofin yayi ta karba tana wani lankwashewa Cikin bada Umarni yace"Shanyesa yanzu..!
Ba musu ta kafa kai ta fara sha Jikinta da Hannunta na rawa Lokaci Daya yana tsaye ya jingina da wardrope din Dakin yana Binta da kallo ganin yadda jikinta ke rawa yasan taci Ubanta da yunwa yaji dadin haka shifa Tana cin Darajan masu Daraja ne ammh ba domin haka ba ko zata mutu ne bata isheshi kallo ba wlh.
Duk da kyamkyamin Dakin dayake yi bai fita ba yana Tsaye yana Nazarinta Abun dariya ya basa Daya ga karamar kafarta Dauke da Jan lalle tare da Hannayenta wai nan shi akayi mawa ko. ?
Shi allah kada ya nuna mai sanda zai kula wannan yarinyar wacce bakomai acikinta sai iskanci da rashin kunya.
Yana wannan Tunanin baisan tashinta ba sai kakarin amai da ya jiyo a Tiolet lekata yayi yana fadin"Ke miye haka..?
Amina na Duke daga cikin Tiolet tana maida numfashin wahala tace"Cikina ne ke juyamin..!
Tafada tana kara Dafe Cikinta Saboda yadda yake Hautsina mata Ta Dade bataci komai ba shiyasa Dan mallam karamin Tsaki yaja bai yi mgana ba Sai ga Amina ta fito tana layi ta sake fadawa saman gadon Cikin mamaki yake kallonta ganin harta gaban Riganta ya fara baci da amai haka gefen bakinta zuciyarsa yaji ta Fara tashi yayi saurin matsawa baya yana Fadin"Ke meyasa kin cika kazanta ne..?
Aman da kikayi wa zai wanke miki..?Sannan ji bakin ki da gaban rigarki duk amai baki da Hankali ne..?
Ya karishe fada yana kauda kansa Sabida bayason kallonta kyama take basa ita kuma ga ciwo ga fadansa kawai sai ta fashemai da kuka tana Fadin"Nifa banda lafiya in na mike jiri nake gani..!
Daure Fuska yayi yana fadin"To ba anan ba maza mike ki wuce Tiolet ki Tabbatar da kin wanke kazantar ki sannan ki tube kayan jikin ki,kin yi wanka..Wlh kada ki bari na Dawo na iskeki a haka ranki zai baci..!
Kukanta ta karama Volume tana fadin"Wlh bazan iya ba..!
Tsawa ya Dakata mata Lokaci Daya yana Fadin"Zaki tashi ki wuce ko sai na saka miki hannu..?Tunda kika zo gidan nan kike sakani mgana ki yi abunda nace tun kafin na yarda da Shawaran zuciyata na kaiki inda ake gyaraama irin ku zama..!
Ai bai gama mgana ba Amina ta mike tana Kuka ta shige Tiolet din Kamar ta Fadi Jikinta ba karfi Tsaki yaja ya Fice aransa yana Jinjina kazanta irin na Amina bai taba Zaton haka take ba.

Sakina ta na nan inda ya barta Tana jiran fitowarsa,kusa da ita yaje ya zauna yana sauke numfashi sai yanzu yaji ya shaki iska ammh Dakin chan wlh ba yanayi mai Dadi ganin yadda ya Zauna yayi ne yasa ta gyara zama tana Fadin"Meya faru Habibi..!?
Bai kalleta ba ya mike yana Fadin"Abinci ya yi saura..?
Cikin mamaki tace"Menene..?
Yana Tafiya wajen Dinning yace"Zuba ma yarinyar chan a filet ki shigar mata dashi..Sannan Daga yau ki rika Dafa abinci da ita kin ji ko..?
Sakina kadan ya Rage bata Danna ma Umar ashar ba sai ta Tuna mijinta ne ammh sai da ta Hararesa kafin tace"Nine ma zan rika girka mata abinci ina aika mata Dashi Daki ko..?
Kai Tsaye yace"Haka nace..!
Sakina ta kallesa Daga sama har kasa kafin tace"Saboda wani Dalili..? Ka manta kai kace Matsayina da nata Daya ne..?
Bai son doguwar mgana yasa yace"Saboda ita yarinya ce..Kuma Amana ce a wajenmu..!
Sakina ta yi shewa kafin tace"yarinya kuma suka aura maka ita..?
Amana kuma ai takace ni dai ba wanda ya bani wata amana..!
Gani yayi zata raina masa wayau yasa yace"Su wa kike mganar sun auramin ita cikin Raini Sakina..?
Yafada yanayinsa na sauyawa ganin haka yasa tayi saurin cewa"Ni fa ba su nace ba..kawai dai kai ma baka taki adalci ba..Zan Dafa abinci ammh wlh bazan Dafa mata na Bita dashi adaki ba in ta fito shikenan in bata fito ba ita ta sani..!
Tana gama Fadin haka ta Mike Dauke da wayarta zata shige Dakinta ya Daga Muryansa yana fadin"bazaki zuba mata ba kenan..?
Juyowa tayi kafin ta kallesa Duk da ta tsorata da yadda ya Hade ransa ammh wlh bazata zauna tana Boyin boyin Amina ba, yasa kai Tsaye tace"Eh..Kai ka zuba ka kai mata tunda ta zama Dolenka ammh bani Sakina ba..!
Daga haka ta shige ta barsa ya bita da kallo bayason Fitina ne yasa bai bi ta kanta ba ya isa ga kular abinci ya Dauki Filet ya Bude ya zubama Amina Daidai ya rufe ya Daukar mata Ruwan gora guda Daya mganar Mallam kawai yake tunawa yasa zai taimaketa kada Cutar yunwa ta mata Lahani fatansa Visar  sa ta fito wannan Satin ya saka kafa ya tafi sai yaga karyan iskanci daga ita har Sakinan sai su kashe junansu shi ba ruwansa.
Sanda ya koma Daki tayi wanka sai dai abun haushi kayan jikinta ta maida nan kasan Cafet ya ijiye kayan hannunsa yana hararanta  kafin yayi mgana ma ta mike jikinta na rawa tana fadin"Ban..baga kayan bane..!
Ghanas dinta ya nuna mata yana Fadin"Ai kinsan kayanki ne acikin nan ko suma sai na ciro na saka miki..?
Da Sauri ta girgiza kai ta wuce sumi sumi wajen jakunkuna ta Duka ta Bude Daya taga Littafan makarantar ne aciki sai da ta Bude Dayan ne taga kayan a goge sai da tayi hawaye tasan aikin Mamanmu ce ko Hamida aranta tace Allah sarki Hamida da hanne ina kewarku..!
Wata Doguwar riga ta Dauko na Material sai bakin dankwali,zata maida ta rufe yace"Ciro wani Hijabin ki Cire na jikin ki malama..!
Ba musu ta ciro aranta ta kudira ta gama mai gaddama gashi mara imani ga mganar Aba ayadda take din nan bata fatan ta kara yin wani abun da Aba zai yi Tir da ita,Tayi alkawarin har Abada an dai kaimasa kararta.
Kayan ta Dunkule Cikin Hijabinta ta gabansa ta wuce zuwa Tiolet chan ta Sauya kayan ta Sake fitowa da na hannunta yana Dakin bai fita ba ganin zata maida masu Dattin Cikin jakar yasa yace"ke wai meke damun ki ne..?
Masu dattin zaki maida Ciki kuma..?Common maida su Tiolet akwai kwando Dogo ki saka aciki nan zaki rika tara kayan Dattin da kika cire..!
Sumi sumi ta koma ta saka a inda yace sannan ta kara fitowa abinci ya nuna mata yana fadin"Ki zauna kici..Wannan shine na karshe da zan kawo miki abinci ruwanki ne ki Fita ki nema ruwanki ne ki zauna da yunwa..Kin ga dai ishara ko..?,Ita yunwa ba"ayi mata Taurin kai..!
Ba musu ta zauna Daman yunwar take ji dan Tea din Data sha ta Amayar dashi kama hanyar fita yayi kafin ya Juyo yana kallonta har taja Filet din gabanta Hararanta yayi ta kasan ido take kallonsa kanta na kasa cikin Sanyinsa yace"Ki tabbatar kuma kin sanya duka kayanan cikin wardrope bna so na kara ganinsu anan wajen kin ji ko baki ji ba..?
Da kai ta gyada mai kafin tace"To..!
Bai kara mgana ba ya fice ya ja mata Kofa kamar tana jira ta Fara cin faten Dankalin hannu baka hannun kwarya sai da ta da shi duka ta kora da ruwa sannan ta kara da sauran Tea din Dazu su Amina har ana lashe Filet,Sai Lokacin taji ta dawo daidai Ajiyar rai ta Sauke ta yaye Hijabin jikinta tana kara shan iska sai da ta huta sannan tatashi taje ta wanke hannu,ko ta kan Filet da kofin batayi ba ta fara Bude kayanta tana watse su a kasa domin bata son ya sake shigowa ya gansu Allah kadai yasan me zai mata in batayi abunda yace ba tana Tunanin su ya jafar ne mugaye sai yanzu take fahimtar akwai wanda ya Shafe su a mugunta ya Danmallam Tana da tabbacin daga shi har shegiyar gajerar matar nan tasa basu da Imani gwara ta bisu a sannu su wanye Lafiya.
Chapter 7 · 0% Book details