← Book details Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 105

Sashe 72

Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Hamida sai kwarmin ido,sun yi wani Zuru zuru dasu su ya Aisha ne kan gaba ke ta Hidiman Baki. Aan basu kyauttuka Hamida an bata na Tajweed da Kira"a am bama Hanne na Larabci da sanin Nahahu sai Sa"adatu ita kuma na zuwa makaranta ba Fashi Hanne sai da tayi kuka sun farota da Amina ammh yau ba ta awajen da zasu yi bankwana da makarantar su haka ma Hamida sai da sukayi kuka,su ya Abida duk sum san kukan da suke yi na rashin Amina ne suma ai sun damu sai dai ba wanda yama Hajiya mgana, ba Tarbiyansu bane yin katsaladan a Hukuncin babba sai dai su hanne sun Fada musu Hajiya tace zata zo insha Allahu. Su ya Zeenatu aka bari da lallashin su Sai da suka saki ransu,Sannan suka koma Bangaran sallaman Baki su da sauran yan ajinsu na Hadda sannan kawar Hajiya tazo tayi ma Amare nasiha sosai sai shidda na yammah aka tashi Sakina anan suka Hadu da Sarood tana ganinta ta manne mata sai Hararanta suke ita da Aliya ita ko Allah Sarki bata sani ba tana tare dasu da zuciya daya ne,Har Hajiya tazo wajen Walimar chan gabda za"a tashi mamanmu kuma ai suna gaba gaba ita da Anty Amarya sun saka kayan alfarma Anty Amarya Shadda ta saka itama mamanmu shadda ce taji aiki ammh kalan kowa Dabam kafafunsu sun ji Lalle kamar wasu yara har yan gusai nama mamanmu Tsiya ta koma yarinya tace a wajen Sa"idu ai ita yarinya ce Danya sharaf Sai Dariya take yi cikin Nishadi suma suna tayata da tsiyan da suka saba mata musamman ma abokan wasan Aba Na gusai. Ana tashi daga wajen walimar aka Dumgumo zuwa gida Amaran dai Gidan su ya jafar suka koma su da ya Zeenatu da Abida sauran kuma sun koma gidan baba mallam wasu kuma gidan Aba Dayake ana ta kiran sallar mangariba suna komawa sai kowa ya fara shirin salla a waje kuma su ya Danmallan sunyi alwala suka Shiga masallaci duk da mallam ya Dawo shi ya bada salla da mangariba suna da Karatu yasa duk suna cikim masallacin suna Sauraran karatun Baba Mallam Har Nazir da shima Gabda mangariba ya sauka Daga Lagos. Adaidai Lokacin misalin karfe bakwai da yan mintina na Dare Motar Usman Mijin Aisha prado mai lambar Abuja ajikinta ta yi Diran cin Taya a kofar gidan Baba mallam Dake Dauke da Haske Tar domin an kunna Gen da wuri saboda Sha"anin da ake ciki ko"ina Haske ya bayyana sai dai kofar Gidam ba kowa duk suma masallaci Tsit mata kuma duk suna Cikin gida. Ya Aisha ta fara fitowa bayan Direba ya Bude mta kofar Mota ita agidan gaba ta Zauna yayinda Amina da Yakaka ke gidan baya. Tana fitowa tace"Salihu bude booth ka Fito da kayan Dake Ciki Duka..! Ba musu ya amsa mata ya nufi Booth din ya Bude ya fara Fiddo da akwatunan Amina Sabbi yana jerawa a kasa ita kuma Aisha ta Bude bangaran da Yakaka take tana Fadin"Yakaka Bismillah mun iso..! Yakaka ta Fara fitowa tana Salati Lokaci Daya tana Fadin"Mun isa barka..Tafiya ai yankin azaba ce..! Lokaci Daya tana kare ma gidan mallan kallo da yanayin anguwam ta Furta"Masha Allah..yau gani agidan mallam..! Take fada daidai Lokacin da Amina ta Fito Daga Motar kofofin Hancinta na Budewa da Shakkar Iskar gumel din Data Dade bata shaka ba,Gabadaya Sai taji ta kamar ba ita ba,Sai taji kamar bakuwa ce ita tana kallon kofar gidan Mallam da nasu gidan wasu abubuwan da suka shude a baya suna Dawowa mata Daki Daki kamar yanzu komai ke faruwa Sai da taji Hawaye sun kawo mata. Tana Sanye da Doguwar riga Baka na Saudiya cikin Tsaraban Danmallan ne sai jan hijabin Dake jikinta Tunda adon Rigar ja ne,hijabin gwiwarta kadai ya Rufe Cikinta gashi nan ya bayyana Kafarta sanye Cikin Takalmi mai Saukakken Tudu kafafun sun kara kumbura saboda Zaman mota Fuskarta ta kara Cika tayi kwaba kwaba kamar Danyen Nama. Duk wanda yasan Amina abaya in ya ganta yanzu da wahala ya ganeta komai nata ya sauya. Tsaye kawai tayi tana bin gidajen nan guda Biyu data yi Rayuwarta aciki da kallo acikin Ranta tana jin wani Farimcikin da bata taba ji ba Dazu suna Hanya sun yi mgana da Danmallam yace mata dukkansu matan suna wajen Walima har suka iso Bata kara mgana ba taso ta samu Walimar su Hanne ammh Allah bai yi ba. Tana jin ya Aisha na cema Yakaka bari ta kira waya a daukan musu kaya tunda ba yara a wajen kawai sai ga Ya Shamsu ya fito Daga gida zai shiga masallaci yaga ya Aisha ya tsaya suna gaisawa tana Fadin"Shamsu yaushe ka zo..? Yace"Dazu da yammh ya Aisha sannun ku da zuwa..! Ta amsa shi kuma ya juya yana gaida Yakaka ta amsa Cikin Fara"a. Ya Aisha ke Fadamai kaya ne daman za"a dauka don Allah ko zai taimaka ya kira mata su Akilu su Daukan mata,Yace to bari yayi musu mgana suna Cikin masallaci da Hanzari ya tafi ya kirasu sai alokacin ya Aisha ta Daga kai tana kallon Amina Data jingina jikin mota batace komai ba.. Cikin kulawa tace"Amina kari so mana..Ko jikin ya rike ne zaman mota ko..? Amina sai alokacin ta tako zuwa wajensu kafin tayi mgana Yakaka ta chabe da Fadin"Dafa gajiya..Ko mu da bamu da komai mun gaji ballatana ita mai Lalura..Jiki fa ya rike sai dai mun shiga ta samu ta watsa ruwa a shafe Jikin da man zafi taji Dama Dama..! Amina ta tura Baki tana Fadin"Man zafi kuma yakaka..? Yakaka ta Harareta Tana fadin"Shine zai sakar miki jiki har kiji Dadi wannan kumburin da kikayi duk ya Saki..! Amina bata samu bakin mgana ba Sai ga Shamsu ya fito bayansa Akilu ne da Zubairu har suka kariso suka gaisa da Ya Aisha da Yakaka basu lura da Amina ba sai da Ya Aisha ta nuna musu Kayan da zasu shigar musu dashi Ciki,Saitin akwatina guda Bakwai sai kuma wani saitin mai Hudu suma Dabam sai kayan su da kuma wasu kaya a kwalaye acikin wani babban Buhu. Ya Shamsu ne ya fara ganin Amina sai ya Tsaya kawai yana kallonta kamar Amina kamar ba ita ba ita kuma ganin Haka yasa tayi mirmishi tana Fadin"Ina yini ya shamsu..!
Chapter 72 · 0% Book details