← Book details Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 105

Sashe 66

Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Har Abuja sun ji Labarim auran su Hamida da hanne watan Gobe Aisha da kanta ta fadama Amina aranar Amina wuni tayi bakinta har kunne Domin ta Jiyo kamshin zuwanta Gumel sai dai takaicinta Daya bata nan ai da mutane sun ga Hura Hanci a Bikin Hamida da hanne ko su ya Abida sai ta rama suma wulakancin datake musu in ana Biki ita ko Cikin jikinta bata Duba ba hango kanta kawai take suna Kara"i ita dasu Hanne Tun kuma Daga ranar bata da wani Hira sai wannan Bikin yakaka har ta gaji da Haddace Labarin Bikim nan a bakin Amina shi kanshi Danmallam Topic din kenan kullum sukayi waya sai tace ranar Bikin su Hanne Hmm kaza kaza yana so yace da Cikin zaki yi kaza..?
Yana tsoron ya ballo ma kansa Ruwa sai dai yana Tausayinta in Hajiya tace bazata zo ba ya zatayi..?
Ai ya tabbata wannan Jidalin na Amina in ta fara shi ko mallam to sai kila sai dai shin zai iya lallashinta yadda taci burin Bikin nan ya tabbata bata ci burin haihuwarta haka ba.
Shima ai yasan da labarin bai Fada mata ba Tunda Mallam ya fadamai haka Hajiya ma duk sun yi mganar su sakina ma bashi ya fada musu abakinsu ma yake jin suna kara zencen yace musu Hakane Sakina sai Murna take yi Nageria tayi kira abu nasu to Har Sarood ta Shirya wannan karon sai tazo itama shi dai ko ci kansu bai taba Ce musu ba kan Bikin ya zuba musu ido ne kawai yana kallon ikon Allah.
Haj.Uwani kusan sai da shafe wajen kwana goma sannan ta Dawo ta saki Ranta ana ta sha"ani da ita Domin mama tace mata ta kwantar da Hankalinta ana gama wannan Bikin Itama Umaima za"ayi nata to shi yadan Sanyayamata rai sannan tana chan Tsafe Uzairu yazo gida Ya kwana Biyu bata nan daga Chan Delta in da yake Bautar kasarsa har ya tafi bata Dawo ba sai da sukayi mgana ta waya.
Haka take shigema Hajiya ana komai da ita Hajiya bata taba nuna mata tasan Wacece ita ba ta barta ne sai Ranar kin Dillaci domin ta nan zuwa Ranar da Allah zai tona musu asiri a bainar nasi.
Mazajen su Hanne sun zo kuma sun gana dasu,Manemin Sa"adatu ya fara zuwa Dan gombe ne ma"aikacin Costume mahaifinsa ne sukayi karatu da mallam a kano,Sai kuma na Hamida Dake lecutring anan Kango Abu Zaria shima yazo Cikin Daliban mallam ne da ya koyar da Mahifinsa tun zamansa a zaria yana Dalibi ma alokacin.
Sai na Hanne da Shine Karshen zuwa Haifaffan garin Adamawa kuma mazaunin yola ne.
Dukkansu ba wacce bata yaba da Zabin Maalllam ba,sai hanne da tun taga ta ganshi take kuka cikin Damuwa kuma taki Fadan Daliinta Hamida ne kadai ta sani kuma ita din ma batayi Zencen da kowa ba.
Shiryen Shiryen Biki fa ya kamkama ta kowani bangare mamanmu ta fi kowa Shiri domin tayi alkawarin kece Raimin da bata taba yi ba sai a bikin Hamida Autarta duk tana Barikin cewa Jawaad ne Autanta wanda yanzu suka fara JSS1 Shi da Sabeeha a kasan ranta ko nan bata ma kaunarsa bataki shima ya mutu ta koma Daga ita sai Sa"idu ko ba ko Hajiya ta Daukesa ta daina ganinsa kamar yadda ta Dauke Amina daga gabansu.
Danmallam da kansa ya Kira Mallam ya fadamai zencen gidan daya siya ma Amina mallam yaji dadi ya dinga sakamai albarka shi ya Kira Hajiya ya Fadamata addu"an da Danmallam ya sha kamar Hajiya zata goyasa albarka kuwa ya shata har sai da ya kusa kwallah yana Tunanin wanda bai Sakama iyayensa ba Allah kuwa zai barsa. ?
Aliyu yama mgana ya kawo ma Mallam Takardun gidan sannan ya Dauke shi da Hajiya kai suka ga wuri Hajiya kamar tayi kuka fadi take"Allah ya tsareka Danmallam..ya yalwata arzikinka..Allah ya Jibanci lamuranka Allah ya kara budi na Alheri yadda ka faranta mana ka rike Amina da Amana Allah kai ma Allah ya rike Hannayenka cikin Aminci..!
Mallam ma haka ya dinga sakama Danmallam albarka sai Tsausayinsu ya kama Aliyu da sukayi waya da Umar ya fadamai irin albarkar da ya sha Wajensu Hajiya Danmallam ya murmusa yana Fadin"Aminene ta mallam da Hajiya ce..Suna shiga farinciki matukar aka kyautatamata kuma kaunar Baba Sa"idu ce ta Shafeta. !
Aliyu yace"Ai kacigaba da kyautatama Amina..ka riketa Amana har ya'yanka sai albarkar Hajiya da mallan ya bisu..!
Umar ya saki kayattacen mirmishi kafin yace"Insha Allahu..!
Hajiya ta kasa auna farincikinta Daga ita sai mallam suka kara tsara kayan Gidan Amina kamar yadda mallam yayi alkwarin yima Amina kayan Daki kamar sauran yan"uwanta haka kuma akayi tare da nasu hanne aka bada Oder din kayan gidan sannan Hajiya ta Tsara in kayan sun iso ya"yan yagana yayarta zata kira ta bata aron su su biyu bayan sun tambayi izinin mazajensu su zasu taimaka mata cikin Sirri su gyarama Amina gidanta Sabida tana so duk ranar data dira agarin ta iske komai ya kamallah.
Hajiya ta kudiri niyyar sai da wannan Bikin Amina zata bayyana sirin Boye zai bayyana a kuma Lokacin take Fatan Allah ya bayyana mugayen Fuskokin Dake tare dasu domin ba Shakka bayyana Amina da Ciki Sai ya Razana su kuma ita ta sani shiyasa bata yarda da kowa ba yanzu Daga ita sai mallam suke sirrinsu ko matan sun Lura da hakan sai dai daman ba wanda yasan Tsakanin Hajiya da mallam tare aka gansu irin su Hajiya Uwani da Anty Amarya sai Bakinciki Daga nesa..!
Hajiya ta zama kadagaren bakin Tulu basu da yadda suka iya da ita. !

*Janafty*
[10/19, 6:19 PM] +234 810 431 4972: *TFZB2023*

*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*

*Gumel..*
Chapter 66 · 0% Book details