Sashe 87
Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kawai sai taji Hawaye ya kawo mata Alherin Mallam bazai fadu ba sai dai sumai Fatan ya gama da Duniya Lafiya. Nan fa su Ya Jadwa suka Rangada guda ya Jawahir cikin Hawaye tace"Yaya tatafi..Ga Wata YAYAr ta dawo..! Kai Allah ya saka ma Baba Mallam da Alheri gwara Balaraba ta san ba mai yi sai Allah sannan da ranta zata ga Aba da wata mace sai dai Bakinciki ya kasheta muguwar mata..!. Sai kuka ya Jamila ne ma ke nuna mata su ya Zulfa da sukayi wiki wiki ga bakinciki ga kunya ammh bakinta ita da ya Jadwa bai yi shuru ba sai Dakin ya koma na koke koke Su Hamida nayi su ya Jadwa nayi sai da Hajiya Nasara ta shigo ta tsawa tar sannan kowa yayi Shuru. Daganan Shashen mallam aka kai su Hanne yayi musu nasiha shi da Aba da Sauran yayyi irin su Ya Danmallam Amina dai ta gaji da Zirga Zirga tana Bangaran Hajiya sai alokacin Taga Sarood duk yadda taso ta karbi Fara"an Datake mata kasawa tayi Domin wani Kishi ne ya taso mata afakaice Hararanta tayi ta Dauke kanta ita kuwa Sarood daman Yar Fara,"a ce koda yaushe Fuskarta a Sake ne. Ita abunda ma ya bata mamaki yadda Aliya matar Aliyu ke ta faman mata Sannu in ta ganta alhalin a baya ko mganar arziki bata taba Hadasu ba Amina bata amsa mata ita bata son munafunci wato taga ta bare ma Kawarta Sakina shine zata zo ta mata Bariki aiko gidan ta taras itama sai ta basar da ita kamar ma bata ganta ba. Bayan an fito dasu Daga shashen mallan har yan gusai maza da basu koma ba sun yi nasu nasihan yan bazanga dai sun koma har ta da kawun Hajiya sun Dauki Hanyar Bauchi tunda sun yi mai wahalar an Daura auran Sa"idu da Hadiza kamar yadda mallam ya nema..! An riga an gama saka kayan gara da Sauran kayan da baza"a rasa ba a motcin da za"a tafi da Amaren su kawai ake jira Hajiya ta ga Hamida da Sa"adatu bai kamata su tafi basu yi sallama da iyayensu mata ba Yasa ta Damka Sa"adatun Hannun Sadiya tace ta kaita wajen marliya suyi sallama itama Hamida ta Damkata Hannun Zulfa tace suyi Sauri kada Mallam ya sani. Kowa mamakin Kirkin Hajiya da zuciyarta ake yi ganin ko a Fuskata bata nuna Wata alama ba. Haka kuwa akayi Sadiya takai Sa"adatu shashen Anty Amarya da ko kaunar barayin yanzu basa yi tana Ciki kwance daga kuka sai kuka cikin kwana Daya ta fara sauya kamanni Tana ganinsu ta mike jikinta na rawa Zata rumgume su suka matsa baya. Ya Sadiya ta kalleta Cikin wani yanayi kafin tace'Ba wata mgana ya kawomu ba. sa"adatu zata tafi gidan mijinta..gatan nan in kinga dama ki bata Shawaran daya dace in kuma kin ga Dama ki Dorata kan hanyar da kike kai ayau..! Da haka ta Saki Hannun Sa"adatu ta Juya tana Sharan kwallah ta Fice Daga Shashen gabadaya Anty Amarya taji gwiwanta yayi sanyi ta Duke gaban Sa"adatu tana Fadin"Sa"adatu don Allah kada ki gujemin kamar yadda Sauran yan"uwanki suka gujeni..! Sa"adatu ta girgiza kai sai Hawaye Cikin kuka tace"Abunda kika aikata abun kunya ne da abun Tir..Ina Fatan kada Rayuwarki ta Shafi namu Rayuwar..Ko Sau daya baki Tuna kina Damu ba..? Sai yanzu ne da Kika Fara Girban abunda kika Shuka zaki ce kada na gujeki..? Nagodema Allah da zan yi nisa da Rayuwarki gabadaya sannan kuma Insha Allahu zan zauna da mijina da Danginsa Lafiya zan masa Biyayya har karshen Nunfashina..! Daga haka ta juya tana kuka Anty Amarya ta Tashi Tana kiran sunanta bata juyo ba tana shirin Barin Falon tace"Wani Hali Sakina take ciki..? Cikin Dakushewar Murya Sa"adatu ta Tsaya Cak kamar bazatayi mgana ba Sannan tace"Saboda abunda kika aikata ta kara rasa Cikin jikinta..Sannan su Anty A"i sun Dauketa ita da sauran yayinta sun maidata asibitin Dutse Dazu da Safe..! Da haka ta fice ta bar Anty Amarya da Gunjin kuka Duniya ta juya mata baya alokacin da batayi zato ba ballatana Tsammani ba..! Abangaran mamanmu kuwa Ita take ganin Abunda ta aikata Domin ko yan"uwanta sun ce badai zuru"arsu ba Ta nemi wani Ahalin sukan sun yafe ta,Tayi kuka kamar ranta zai fita Tana gani suna Hada kaya sun ce ana wucewa da Amare zasu kama Hanya Tazama kamar wata mujiya acikin mutane ya"yanta kaf sun juya mata baya bama ta su Jafar wadanan tasan Da wuya su iya yafe mata. Ita kadai agidan dukkansu suna gidan Hajiya tana cikin Dakinta tana gunjin kuka,Sai ga su Hamida har aranta taji Dadi ta mike da Sauri zata rumgumesu Hamida ta tureta sai da ta Fadi Cikin Bakinciki ta nuna ta da yatsa tana Fadin"kul kar ma ki fara..Na Fada miki ban sanki ba baki sanni ba..! Zulfa ta kasa mgana sai kuka Daga karshe ma sai ta fice Daga Dakin Mamanmu na kwance in da ta Fadi tana wani irin kuka take fadin"Hamida ni fa mahaifiyarku ce..? Ko Duniya zasu juyamin baya na Dauka kuna tare dani..? Hamida tayi wani Dariya kafin tace"Wlh nayi Nadaman dana fito Daga Cikin ki..Nayi nadamar kiran ki da sunan uwata da nayi..Yadda kika Cutar damu kika bar mana Bakin Fenti kema Bazaki taba Gamawa da Duniya Lafiya ba..! Sannan ga wani karin albishir Aba Yayu din nan tare da auran mu mallam ya Kara Daura masa aure..Da Diyar kanwar Hajiya kin ga kenan tundaga nan kin fara ganin karshenki..! Mamanmu ta Zaro Ido gabanta ya Fadi cikin rawar baki tace"Au...Reee..? Hamida ta gyada mata kai Ta cigaba da Fadin"Kuma na tabbatar da cewa ke ba matar Aba bace yanzu..Gwara tun wuri ki neni inda zaki..Ni dai zan tafi gidan mijina ina Fatan kada Laifin ki ya Shafi rayuwarmu kije Duniya ce..Da Sannu zaki girbi abunda kika Shuka..! Ta juya tana sharan kwallah zata Fice Mamanmu ta riko kafafunta tana Kuka tana Fadin"Hamida kada ki tafi ki barni ina zan je..? Kuma ai Sa"idu bai ce ya sakeni ba ko..? Hamida na kuka da kuma Dariyan Bakinciki tace"lalle Balaraba kin raina ma kanki wayau ba kuma ki da kunya. ! Duk abunda kika aikata kina Tunanin kina da wani Sauran kima ne..? Kima kara gaba tun kafin kifara wulakanta..! Daganan ta Fizge kafarta ta fice tana kuka,a haraban gidan ta hadu da Zulfa suka rumgume suna kuka jin su shuru yasa Ya zulaihat ta Biyo bayansu ganin suna kuka itama sai ta Fara kai mamanmu ta lalata rayuwar ya"yanta. Hakanan suka fito suna kuka Daman duk an fito ana kofar gidan baba mallan ganin Tafiyar Amaran duk yadda Amina taso kada ta fito sai da ya Abida taje ta Taho da ita domin Hanne da Hamida sun ki shiga mota sai kuka suke yi Ganin Amina yasa suka kara rudewa Amina taso ta Daure ammh ta kasa itama sai kuka Aminu kansa kawai ya kauda har da su Nenne a yan Lallashi, Hajiya bata wajen tana cikin gidan su goggo Yagana da su Hajiya Nasara sai yan gusai dake wurin ya Danmallam ma na falon mallam ya Shamsu yaje ya Kirasa yazo ganin yadda suke kuka shima sai da ya tabasa ba kunya ya Riko Amina ajikinsa ya Rumgumeta yana lallashinta ita kuma jinsa ajikinta yasa ta kamkamesa tana kuka Da haka aka samu suka shiga Mota Sa"adatu tuni har sun mika Hajiya da kanta ta sakata a Mota Allah Sarki Hajiya mai rama Sharri da Alheri Su ya Abida suna ta gulmar ya Danmallan ganin ya nufi Cikin gida rumgume da Amina suna Fadin abaya ya Dammallan ko mgana da matarsa bai iya yi gaban mutane sai gashi yau har da su rumgumewa gaban mutane..! Dakin su Nazeem ya shiga da ita yana ta lallashinta Sai da ya dan mata jan ido ne ta Daina kuka ta koma ta Lafe a Kirjinsa tana kuka sai da ya tabbatar da ta daina kuka sannan ya fito da ita da kansa ya rakata har kofar shashen Hajiya sannan ya Dawo..sallama sukayi da Aliyu zasu wuce shida Aliya,Hajiya ta rkota har haraban gidan ta mata godiya bayan ta bata kayan Biki haka su Aliyu suka Dauki Hanya ba tare da sun kara tada mganar abunda ya Faru Jiya ba Sun dai yi mganar Amina yau za"a rakata Sabon gidanta Aliyu na mai Tsiyar yau ango yake shi kuma yana jin Dadi ita kuwa Aliya duk jikinta yayi sanyi ta kara tsorata da Duniya. Ana tafiya da amare yan gusai sukayi Harama Zafira dai tun kafin tafiyar su Hanne ita da mamata sukabi yan Daurin aure suka koma. Ba yadda Hajiya batayi su bari su raka Amina Gidanta ba sukace bakomai in ta Haihu zasu dawo suna gabadaya ransu babu Dadi kaf dinsu suka juya aranar gidan Aba bako Tsinke sai Mamanmu ita kadai da Halinta kaf su ya Jadwa sun koma Shashen Hajiya Babba. Hajiya uwani kuwa abakin Umaima sukaji bata agidan itama taje shashen taga ba kowa Ya Nazifa ke ta kula da kanwar nata ya uzairu ya koma inda yake Service ana gama Daurin aure Ko Tsayawa bai yi ba,Nazeem kuma nan da Sati Daya zai tafi Lagos ya Fara aiki sun yi mgana da Nazifa zata roki Mallan ya bata Umaima tatafi da ita Domin suna da Tabbacin zamam Mahaifiyarsu agidan mallam yazo karshe Duk da sai Dare ne mallam yazo da Labarin rasuwar Batula shima wani Cikin yayyin su Batula ya kirasa yake fadamai sai Lokacin ma kowa yasan bata agidan. Ba wanda ma ya Damu ana ta Hada Hadar raka Amina Sabon gidanta Hajiya ta kasa zama su ya Abida sun tafi tun Mangariba suna gyara gidan suna Share kura da saka labulanya sannan Hajiya tasa Hadiza Amarya Aba ta dan ma Amina gyaran jiki Dayake Sana"arta ce sannan tazo da kayayyanki Tunda tayi ma su Hanne yan"uwanta sai tsiya suke mata suna cewa zata gyara yarta ita kuma tana jin kunya ba Zato ba Tsammani taji auran nan Daga sama har ta fara kuka Hajiya tace kul dinta ta Godema Allah Sa"idu mutun ne har da Rabi,Tun bayan Rasuwar mijinta bata kara marmarin aure ba, ta koma makaranta Tayi NCE sannan ta ke kuma Hadawa da Sana"ar gyaran jiki. Sannan ita bazata ce ga Aba ba,