← Book details Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 105

Sashe 47

Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Amina tace"Tab wazai bisa madinan..?
Ya Aisha tace"Yakaka kina jinta ko..!?
Tace"Yi tafiyarki barni da yar nema..!
Bata lambar mijin nata ta Kirasa da kanta..!
Ya Aisha tace"Munyi mgana yanzu yace zai kirata..!
Yakaka ta amsa da Toh fita Aisha tayi ta barta da yakaka sai Fada take mata ta shiga bata labarin irin yadda tayi gwagwamarya agidan kakan su Usman Cikin mata Biyu har sai mijinsu ya rasu ana ta Kishi da ita Amina dai tayi bakam tana jinta kafin tace"Yakaka in ka hadu da masu asiri fa suna zuwa gidan Boka..?
Yakaka tace"To Sai me..,?
Ai akwai su duniya ta lalace sai ka koma gefe ka rike Allah ka sa aranka Bawa bai isa yayi maka abunda Allah bai maka ba..yar nan rike gaskiya ki rike Allah ko min Dadewa gaskiyanki Zata bayyana sannan Allah baya barin Azzalumi da sannnu hakki zai bayyana .!
Kai ta jinjina domin ta gamsu da mganar Yakaka suna Cikin hirar ne Taji karar wayar dake gefenta da Farko ta Firgita sai da Yakaka tace mata wayar tace sannan hankalinta ya kwanta Mikewa yakaka tayi da Go ranta ta fice tana Fadin"Mgana mai Dadi kuma ban da Tura masa wannan bakin..Ki ce sabuwar amaryansa tana gaishesa .!
Ta fice ta bar Amina da waya a Hannunta sai da ta Katse sai kuma ya Sake kira tabi jerin lambobin da kallo bata Nigeria bane,Daukan wayar tayi Domin sak irin ta yaya ce tasan yanayinta tana Daga Kiran taji Sanyayyar Muryansa yana mata sallama sai taji kamar an kwara mata Ruwan sanyi ko"ina na jikinta yayi Sanyi har Bakinta ma yayi nauyi ta kasa amsa mai sai da ya maimaita sannan ta iya amsa murya shake Cikin Haibansa yace"Amina ya jikin ki..?
Tura baki tayi kamar yana ganinta kafin tace"Ni ai lafiyata kalau..!
Gemunsa ya sosa kujeran Office dinsa tana Dan juyawa dashi,yace"To ko ya nauyin jiki zan ce..?
Amina sai taji kunya ta kasa mgana cikin wani yanayi yace"Nayi ta Kiranki ban samu ba tunda Hajiya tace min ta baki wayar..!
Uhm kawai tace ya Cigaba da Fadin"Amina kinga lamarin Ubangiji ko..?
Wannan rabon Dake Tsakanin mu shine silar Faruwar duk abunda ya Faru..!
Amina tayi shuru batayi mgana ba shims shurun yayi kafin yace"Ba inda ke miki ciwo ko..?
Amima sai taji wani Rauni ya shigeta kafin tace"Eh..!
Cikin Rudewa yace"Eh kuma..?
To ina ke miki ciwo..?
Amina kai Tsaye tace"Menene mgani in an yi ma mutun sihiri sannan ta wata hanya Zai gane an yi masa..?
Umar yaji mamakin mganarta Cikin mamakin yace"Amina waye akayi ma Sihiri..?
Cikin wani yanayi Amina tace"Ni ce..!
Baki ya Bude kamar tana ganinsa Cikin mamaki yace"Ke kuma..?
Ta ce"Eh..!
Sai kuma kawai ta Fashemai da kuka Har da Sheshsheka Saboda Dacin abun na taso mata lokaci Daya Rauninta na bayanna.
Danmallan jikinsa yayi sanyi Cikin wani yanayi yake fadin"Kinga Amina..bar kuka nan yimin bayani yadda zan gane..!
Ina ko jinsa batayi sai faman kuka take yi Dagacin kukan datake yi Daga karkashin Zuciyarta ne kansa ya Dafe Cikin wani yanayi duk da yasan yarinyar akwai kukan banza har da na siyarwa sai dai jin kalamanta da wannan kukan datake yi tabbatar wani ya faru wanda kedamunta acikinta kuma ta kasa fadamawa kowa..!
Cikin sigar lallashi yake fadin"kiyi hakuri ki daina kuka sanar dani abunda ke faruwa..!
Sai taji muryansa kamar wani waraka ne ga matsalanta yasa tace mai cikin kuka"ban taba Fada ma kowa ba sai kai..Wlh duk abunda Zan fada maka ba karya bane ya Dannallam..!
Da Sauri yace"Eh naji bazan Fada ma kowa ba taimakeni kibar wannan kukan saboda yanayin Dakike Ciki..!
Amina ta share Hawaye tana jan majina tace"Yaya..Yaya. !
Ta fada sai kuma ta kara sakamai kuka Umar ya shiga wani yanayin Tashin hankali da jin kukanta Cikin mamaki yace"Yaya. ?
Amina tace"Eh yaya ba mutuwa tayi ba Kasheta MAMANMU tayi..!
Ta fada tana matse bakinta kada kukanta ya kara fitowa yana Zaune ne sai da ya mike Cikin wani yanayi a Muryansa yace"Yaya ba mutuwa tayi ba kuma..?
Mamanmu ta kasheta..?
Amina ta amsa mai da Eh Cikin kuka Umar ya katseta Cikin Muryansa da kaifi yace"Ki bar wannan kukan yimin bayani sosai yadda Zan gane..!
Amina sai kawai taji ta yarda Data Fadama Danmallam abunda taji ko zai Daina Damunta aranta ko Zata Samu Saukin abunda take ji..
Cikin kuka ta fara Fadamai komai Tun farkon wayar da taji Anty Amarya nayi a ranar da Hajiya tace zata tare da kuma Ranar da Ta kama mamanmu tana mgana da duka mganganunta,Sai dai ta Boye sunan Hajiya Uwa tunda bata san meye Tsakaninsu ba..
Amina ta sharbe hawaye tana Fadin"Da kunbina naji suna waya ya Danmallan..Da kunnina naji mamanmu na Fadin malaminta ta saka ya kashe mana uwa Saboda ta Samu Aba yadda take so Sannan da kunnena naji tana Fadamin Ba ni taso na ZAMA haka ba ya Jafar taso ya lalace da kunnina naji Tana Fadin Bazan haihu Dakai ba Sai Sakina sannan sukace har Abada sai dai aurena Dakai ya kare a gantali..Zuciyata tana min Zafi tun Ranar da naji haka..nayi kukan rashin Uwa Ya Danmallam bansan Dadinta ba Duka Mamanmu ta nesanta dashi ya Zanyi..? Abun na Damuna Zuciyata zafi take min kamar Zan mutu. !
Ta karishe fada Cikin kuka Danmallam Zufa kawai yake yi kansa na juyawa Mamaki da Dimuwa da al"ajabi sun kamasa ya kame awaje daya salati kawai yake maimaitawa acikin Ransa kafin ya samu yar natsuwa Cikin Wani irin Sauti yace"AMINA..!Kin tabbatar da mganar da kika Fadamin..?
Amina ta kara fashewa da kuka Tana Fadin"Wlh in nayi maka karya Allah ya..!
Da Sauri ya Katseta da Fadin"Amina ba kyau irin wannan rantsuwan ba kyau..!
Sai yaji yama kasa mgana Saboda mamakin abunda yaji,Amina kuka ta Cigaba da yi kamar ranta zai Fita yana jinta ya kasa mgana sai chan yace"Kin Sanar da Hajiya ne..?
Saboda yana tunanin kodai Hajiya ta sani ne Data Dauki wannan matakin sai Amina tace bata Fadama kowa ba...kansa ya Daure Tunaninsa ba Lokaci Daya bane yana Bukatar natsuwa Cikin lallashi yace"Ki daina kuka..Sannan ki cire damuwa aranki..Zan yi Bincike a barayina in dai mganar ki gaskiya ne akwai yuyuwar kowa yaji labarin nan,Alkawari Zaki min zaki Daina Tunani da Damuwa bakin gayamin ba .?
Da yardan Allah komai zai zama Daidai kada ki damu..!
Amina ta koma sheshshekan kuka tana Fadin"Haka mamanmu ZAta kashe mana uwa a banza kenan ya Danmallam..?
Kai ya girgiza kafin yace"Ai hakkin Rai ma bazai barta ba Amina..In ma da Gaske ne Allah bazai barta ba sai ya Wulakantata aduniya..Sannan ai Allah ya nuna musu basu isa ba..Suna nasu ne Allah shi kuma yayi nashi..Amina Kina da juna Biyu wannan kadai ya isa kisan Allah ne Kadai mai yi alokacin da yaso a kuma Sanda yaso..!
Amina taji jikinta yayi sanyi ammh bata bar kuka ba shi kuma ya tattaro Jarumtarsa yana ta bata baki da lallashinta Shima kenan datake da shekaru ya shiga wannan Halin balle ita mai karancin shekaru kamar Amina..?
Dakyar ya samu Amina ta bar kuka shi Tunaninsa ma kada Damuwar ta Haifar da Matsala ga abunda ke Cikinta sai da ya tabbatar da ya lallasheta tare da alkawarin komai zai zama Daidai ya karishe da Fadin"Zan zo Gida watan gobe..In nazo sai mu Sake zama muyi mganar musan yadda zamu bullo ma lamarin ni dai ki daina Damuwa Sannan kada ki Fadamawa kowa..!
Amina ta gyada kai kafin tace"Zaka zo nan ne..?
Wajena..?
Yace"Eh zan zo na ganki naga yadda Kika koma in kuma ga yadda Cikina ya zauna ajikinki !
Sai kunya ta kama Amina ta kasa mgana shi ma bai wani Damu ba,baya Cikin natsuwarsa Daganan ya mata sallama ya katse kiran.
Zagayen office dinsa ya farayi kansa ya Dafe ya shiga Tunanin mganganun Amina bai san mamanmu a boye ba sai dan Zahirinta Daya sani kadan ana Fadin Kirkinta,ko abakin yaya yasha jin haka Sannan shi bai da wani Sakewa da ita iyakarsa su gaisa sannan ita kanta Anty Amarya gaisuwa ce Tsakaninsu har gwara itama sukan yi Doguwar mgana Sanadin Sakina Sai dai kuma ya fara jiyo kamshin gaskiya kan mganar Amina Duba da Yaya ance Lafiyalau ta kwanta sai gawa duk da ita Mutuwa ko da Ciwo ko ba Ciwo sai an tafi..!
Ammh Amina yarinya ce ba yadda Zata Zauna ta Tsara mgana haka in ba ji tayi ba Sannan ya tuna yadda Sakina tada hankalinta kan Auran sa da Amina da kuma Matsalan data Faru tsakaninsa da Sarood Aliyu ya fara Hangomai Lamarin a matsayin Shihiri ammh bai yarda ba sai da Mallam ya sanar dashi Cikin Hikima har ga Allah bai zargi Sakina ba ammh kuma yanzu Dayaji wannan mganar sai ya shiga kokonta ya tuna Bakin kishi Sakina da Burinta ita ta Samu Ciki ta Haihu har wani Lokacin ya Dinga mata Fadan ta roki mafi alheri..
Bawai ya yarda da mganar Amina Duka bane sai dai kuma ya shiga Rudi da kokwanto agidansu ake wannan Tsantsan jahilcin da mugunta har da kashe rai..!
Indai ko gaskiya ne Anty Amarya da mamanmu Allah bazai barsu ba sannan sai ya nuna musu basu isa su raba auran da Allah ya kulla da kansa ba.
Cikin tashin Hankali ya kira jafar a waya yana Tambayansa Amina na karya?.. tunda sun fisa sanin yarintar ta shi ba mazauni banw baisan komai kan Rayuwarsu ba.
Ya jafar ya fara fada yana Fadin"Hala iskancinta ta maka..? Ai Amina sai Allah..Wlh ya Danmallan ka daina Sake mata ne. !
Cikin haushinsa yace"Tambayata zaka bani amsa ko zaka Tsaya kana gayamin abunda zan yi da matata ne..?
Saj jafar ya rike baki yana yar Dariya kafin yace"Amina bata da Halin karya..Bata da kumbiya kumbiya ita Free take abunta bata da Tsoro sannan tana da kafiya da Taurin kai yadda kasan zuciyan kafuran farko bantaba ganin wanda duka baya Sata tayi Laushi ba sai Amina..Ko zaka kasheta sai tayi mgana sannan abunda yake gaskiya take fada
Bansanta da karya ba gaskiya..Sai dai Rashin kunya da tsiwa da Tonen fada da Yawon tsiya..!
Danmallam ya jinjina kai alamun gamsuwa kafin ya Datse kiransa ya jafar afili yace"Ko son Amina ya Danmallam ya fara ne..?
Dariya yayi kafin yace"Tab..bai Fada hannu na gari ba..Amina ai jidali ce..!
Danmallam kuwa suna gama mgana ya saki Huci Amina tana da gaskiya wani abu na Faruwa sannan ya Fara ZArgin Hajiya tasan wani abu shiyasa ta hana Amina ta zauna a gumel sannan kuma ta hana kowa yasan da Cikin jikinta tabbas ya hasaso wani abu..
Sai dai koma menene ya kamata yaje Negaria yaga Amina su yi mgana sosai sannan yaga ta ina zai Bullo ma al"amarin da ke faruwa agidansu karkashin Tarbiyan mallam..?
Lalle ana Zaton wuta a makera sai aka sameta a masaka..Zuciyarsa ne taji ta Bude da duka mganar Amina da Tsausayinta da bai taba jiba ba..Dole ya tafi gida cikin watanan mai Shiga abubuwa Dadama suna Bukatar yaje ya gabatar dasu tukunnah..!
Chapter 47 · 0% Book details