← Book details Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 105

Sashe 17

Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tunda ya kwanta bai tashi ba sai karfe biyu narana da wani abu Allah ya taimakesa daya tashin ciwon kan ya sauka harda muran ma ta fara sakinsa bai ji dadi ba tun jiya yake rasa salla cikin jam"i abunda baya faruwa dashi sai da wata lalura mai karfi.
Dakin da Amina take ciki ya shiga har Lokacin tana ta barci sanin Halin Datake ciki yasa bai tasheta ba Tiolet ya shiga ya Dauro alwala ya fita Falo yayi sallah jin sa yake yi sakayau kamar ansauke mai wani kaya mai nauyi ajikinsa nan kan kujeran ya cigaba da zama yana Tunanin makomar abunda ya faru Tsakaninsa da karamar yarinya irin Amina inda Allah ya Rufamai asiri natsuwarsa acikin jininsa take bai ce baya rasa natsuwarsa wani Lokacin ba ammh bai cika rasa shi duka ba yanzu da ya zo ma Amina da karfi ya jimata ciwo har ta kai da wata matsalan da asirinsa ya Dade da Tonuwa in kuma Hakan ya faru akwai kunya da kuma zubewar kimarsa ko mallam da Hajiya baya fatan su ji labarin aika aikan daya aikata ita kanta yarinya yana ta mamakin Dauriyanta da jarumtar ta sosai ta bashi mamaki bai taba zaton zata iya Daukansa ba,Duk da abun ba wani Dadewa akayi ba sannan abu ne da yafaru dukkanasu basu da zato ko Tsammani.
Gajiya yayi da zaman shuru yasa ya tashi ya kunna Tv tashar Sunna tv ya saka yana sauraran wa"azin Dr.Jabir mai hula har la"asar tayi ya tashi yayi sallah baya so ya fita ya bar Amina ita kadai ta farka ta fara kukanta na Fama har kuma Lokacin bata tashi ba ya Lura kamar akwai mganin Dake sakata barci aciki shiyasa ya barta ta Huta ba laifi ai taji jiki tana Bukatar Hutu.
Sai wajen Biyar da Rabi na yammah Amina tatashi shima din ya shiga ya Dubata ne ya isketa zaune kan gado tana ganinsa ta dukar dakai bata son suna Hada ido shima dim kunyarta yake ji yasa ya kauda kansa yana fadin'"Ya jikin ki..?
Kanta na kasa ta amsa da cewa da Sauki Tiolet ya shiga ya Hada mata ruwan zafi ya fito yana fadin"Tashi kiyi wanka..Kiyi sallar dake kanki..Azahar da la"asar..!
Batayi gaddama ba ta Sauko daga kan gadon tana jin kuzarinta ya fara Dawowa sannan jikinta ya Daina mata Ciwo kamar dazu sai dai har Lokacin kasanta na mata Zafi Tafiya kadan kadan take yi kamar yar koyo zata wuce ta gabansa ba zato taji hannunsa saman kanta ya taba Lokaci Daya yana fadin"Zazzabin ya sauka..!?
Cikin sigar Tambaya duk da sanda ya Tabatan dukkansu sai da tsigar Jikin su tatashi da sauri ta gyada mai har jikinta na rawa ta shige Tiolet din da Sauri ya Bita da kallo.
Darduma ya shimfida mata ya ijiye mata Hijabi sannan ya koma Falo kada ya Takura mata sai bayan wani Lokaci ya Dawo ya isketa ta gama Sallah bai Tsaya ba ya fita ya Dauko mata Ragowan kazan dazu da youghourt,ya bata daman kamar ya sani Cikinta kamar an yi yasa sai dai bakinta ne ba Dadi ya tasata sai da ta Cinye ta Dora da mdaran sannan ya bata mgungunanta na Rana lum da ido ta dinga yi tana so ta kwanta nan kasa ya Hanata Cikin Sautinsa yace"ki zauna mganin yabi jikinki..Kika kwanta zaki iya yin amai..!
Amina ta ji hawaye ya kawomata cikin Sanyin murya tace"Barci nake ji..!
Mikewa yayi yana Fadin"Ba kyau barcin yammah dazu ma don naga baki tashi bane..!
Ita dai batace komai ba ta maida kanta kasa Filo ta ga ya Dauka ya Fita tana ganin haka ta kwanta saman Cafet ba zato ta ga ya sake dawowa Saboda kada ya ganta yasa ta mike da Saurin da sai da kasanta ya amsa ta Cije baki tana fadin"Wash..!
Kallonta yayi kafin yace"Sannu..Ki taso muje falo ki zauna..yammah tayi kwanciyar bata da amfani..!
Bataisa tayimai gaddama ba ammh da zai gane da ya barta anan ta zauna din bata son hada ido dashi ko zama kusa dashi ammh bai kyaleta kafa kafa ya Satasa suka koma falo kan kujera mai zaman mutum daya ya zaunar da ita bayan ya kara mata Filo shi kuma ya koma mai zaman mutum biyu ya zauna Lokaci daya ya maida kansa wajen kallon abunda ake haskawa a Qur"an tv Saudi domin ya sauya tasha.
Bai kara ma ko kallon barayin Amina ba sai chan ya duba barayinta sai yaga tana barci a zaune mirmishi kawai ya Saki yana da tabbacin mganin akwai mai sa wannan barcin bai tasheta ba sai da aka kira sallah bayan ya Dauro alwala yace taje daki tayi alwala tayi sallah zai tafi masallaci ya dawo Daganan ya fice.
Kamar yadda yace haka tayi sai bayan data idar da sallar shuru shuru bai Dawo ba ta fara jin tsoro ita kadai agida Falo ta koma ta Rakube kan kujera tana Zaran ido abu kadan ke sakata kuka yanzu sai kuka Allah ya Taimaketa akwai wutar nepa.
Shi kuma bai bar masallaci ba sai da ya Tsaya yayi sallar isha"i yaje Atm ya cire kudi saboda na hannunsa sun kare Allah ya taimakesa ba banki Daya garesa ba,Guda uku garesa anan gida sannan yana da Biyu achan Saudiya ba domin haka ba da Abunda Sakina ta aikatamai da kashinsa ya Bushi wato haka take so koda ya tafin yunwa ta kashe yarinyar Mutane tajamai bala'i wlh Nageria tayi kadan shi da Sakina sai ya nuna mata shi ke auranta ba ita ke auransa ba!
Restaurant yaje ya siyo musu abinci da abun sha sannan ya Dawo koda ya Dawo tara ta kusa Amina ya samu nata kuka shi ya zata ma ko ciwon ne ya Dawo ya fara tambayanta ina ne ke mata ciwo..!?
Cikin Hawaye tace"Tsoro nake ji..Ni kadai agida..!
Bai yi mgana ba illah abinci da yace ta Sauko taci ferfesun ganda ya siyo ma kansa ita kuma na kayan ciki sai Fruit salat saboda a yanayin datake ciki yasan zata ji dadinsa sai ruwa da Maltina da yawa,kuma taci sosai saboda barinta yayi ya koma Daki yayi wanka ya Sauya kaya zuwa wata Jallabiya koda ya fito ta cinye duka harda shan romo tana ganinsa ta koma ta nade waje daya kanta na kasa bai nuna ya Fahimceta ba tambayanta yayi ko ya isheta ta Daga kai Fruit salat din ya Turamata gabanta yace ta sha,cikinta ya cika yasa bata sha da yawa ba mganinta ya bata ta sha bayan ta tabbatar mai da tayi sallah yace taje ta kwanta kamar ya sani barci take ji ammh sai ta kasa tafiya Tsoron kwanciya take yi ita kadai ganin haka yasa yace mata ta je in ya gama abunda yake yi zai shigo..!
Dalilin dayasa tatafi taje ta kwanta kenan ba jimawa sai gashi ya shigo shima kadan yaci gandan ya sha mgani nan kasa ya shimfida bargo ya kwanta Alokacin har Amina tayi barci batama sani ba shi ya cire mata Hijabin Jikinta data kwanta dashi Saboda tasha iska ko motsi batayi ba bayan ma mgani ya Lura tana da nauyin barci.
Shima yana kwanciya bai Dade ba sai barci saboda na muran yana saka barci karfe hudu na asuba ya tashi yayi wanka ya fice zuwa masallaci sai 6 ya dawo ganin Amina bata da Niyar tashi ya tasheta yace tayi sallar kamar mashayiya haka tatashi tana Idar da Sallar ta koma ta kwanta tana samun Hutu sosai.
Shi kuma yana falo yana kallon labarai wayarsa tun jiya ta cika ammh Hakanan yaki kunnata baya so ma wani yasan yana nan Tafiyarsa shekaranjiya bata samu ba sai yau,Sai wajen 8am na safe ya leka Amina tana ta barci bai tasheta ba ya shiga Tiolet kayan data tara a Kwandon wanki ya kwashe harda zanin gado yaso ma ya Kira mai musu wanki ne sai kuma ya fasa,Gwara ya wanke su da kansa yasan in ya tafi bai wanke ba akwai matsala Amina bata san ciwon kanta ba Tukunnah ko kuma yace ba"a koyamata ba Daga yanayin yadda bata iya komai sai tace Mamanmu ko Hamida ke mata Daga gani su suka batata ammh ace kamar ta ace batasan gyara ba sai kazanta.
Ta harabn gidan akwai wata Kofa inda suke da famfo da tankinsu na ruwa nan ne sukayi wanki ko shanya in wani abu ya faru na gaggawa,nan ya kwashe kayan ya fita dasu Allah yasa Megadi na Dakinsa bai gansa ba ba Omo kwata kwata agidan sai da ya Fita ya siyo ya Zage ya wanke zanin gadon nan tas da kayan Amina pants dinta kuma Data wanke basu fita ba ya Zubar a Bola domin bazai iya wanke mata ba, ba domin yana kyamarta ba yana da kyamkyami sosai ne sosai bazai iya wankewa ba,Ammah ai karshen kyamkyami kuma ai ya kare tsakaninsa da Amina tunda mai afkuwa ta riga ta afku
Chapter 17 · 0% Book details