Sashe 60
Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
yaaja ya kashe wayar yana kallon Amina data boye kanta cikin kirjinsa Dagota yayi yana fadin"zaki bini Amina..? Cikin wani yanayi tace"Ina..? Bai mata mgana ba ya taimaka mata ta mike ya Dauko mata hijabinta Dake kan gado ya saka mata yasaka mata takalmi Daya gani bakin gado yaja Hannunta suka fita Daga Dakin. Falo ba kowa Aisha na Dakinta ita da Usman Yakaka ta shiga Dakin Amina tayi sallah bayan Aliyu ya tafi Sallah Dakin Dake yammah acikin falon na Saukan baki. Awaya Umar ya Kirasa yana Dauka yace"Fitomin da key din motarka..waje..! Daga haka ya ja hannun Amina suka fita Daga falon bayan ya katse wayar. Aliyu cikin mamaki ya fito haraban dan madaidaicin gidan yana kallon Umar Dake jiransa yana zuwa a bakin motar yaga Umar da Amina har kuma Lokacin yana rike da Hannunta. Aliyu ya rike haba zai yi mgana Danmallan ya warce key din a Hannunsa Amina kunya ya kamata ta kasa Motsi hannunta yaja sannu har inda zata shiga mota bangaran mai zaman banza ya Danna wani abu jikin key din motar ta Bude ya bude mata ta shiga ya taimaka mata ya zagayo bangaren Direba zai shiga yana cema Aliyu"To na bar gidan kanwata sai ka hanani shakatawa da Matata..! Daga haka ya shiga ya kunna Motar yayi hon megadi ya Bude masa get ya sulala waje ya bar Aliyu da baki sake yana yar Dariya afili ya furta"Shege Shehi..Ya dirkama yarinya ciki ya Lallabo zai kwashe romon..!