Sashe 89
Ta Fita Zakka Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Aka bar Uwani ita kadai Tana Faman da Bugun zuciya mutuwar Batula ya kara Raunanata Gata nan kawai ammh ita kadai Tasan Halin Data ke Ciki kuka tayi shi kamar Idonta zai Tsiyaye Kiran wayan su Nazeem kam har tagaji basa Dauka Shamsu ne ma ya taba Dauka yace kada ta kara kiransa Nazifa kuma Blooking dinta ma tayi,bata da karfin gwiwan komawa Gumel domin tasan zamanta achan ya Kare. Rayuwa ta juya musu baya alokacin da basu zata ba,. Sati Daya na Cika Anty Hadiza ta tare adakin Yaya,sai abunda ba"a rasa ba Hajiya ta kara mata sannan Aba yayi mata akwati Biyu na lefe su Yakaka ne gaba gaba yan raka Amarya ita da Haj.Nasara. Aranar da Daddare Danmallan suka zo shi da Amina data matsa sai ya kawota taga Hajiya da Aba da Mallam,sai da suka zo sannan Hankalinta ya kwanta Shashen Hajiya ya barta yaje shashen Hajiya nasara ya ga Sarood Tunda tana wajenta yace ta koma gidansu na kofar arewa tace ya barta anan tasan ba wani Damuwa da ita zai yi ba yana da amarya Shi ko ba haka bane gani yayi ba yanzu zasu koma ba Sai nan da wata Biyu gwara ta koma gidanta zai fi in ya gama kwanakin sa wajen Amina sai ya koma mata ammh sai ta nuna bata so..! Sai kawai ya kyleta ganin kishi take shi ko aransa ma tunani yake sarood bata iya kishi ba ai kishi na wajen Aminaa Jidali. Shi tunda abun nan ya faru bai kara neman sakina ba,shi abakin ma Hajiya yaji Yan"uwanta sun maida ta Dutse daganan bai kara bi ta kan mganarta ba sai da komai ya bayyana sannan ya Fahimci bai taba Son Sakina ba komai ya kare acikin Ransa kwata kwata shi dai bai ma tsaya ya yanke wani hukunci akanta ba sai dai bata acikin Ransa kwata kwata. Basu koma ba sai Sha Dayan Dare Har gidan Aba suka je,Mamammu ta window take lekonsu tana Kuka kukan Nadama da Bakinciki. Amina Bakinta yaki rufuwa ganin Anty Hadiza Dakin Aba ta rumgumeta tana murna sosai itama ta riketa cikin Farimciki jawaad tana murna ya samu mama. Haka kowa ke shigowa yana fita bawanda ya Damu da wata mamanmu mamakin karfin Halinta ma Aba ke gani data ke cikin gidan bata kara gaba ba. Agaban idonta ya shigo gidan da Ledoji a hannunsa ga shi yaci Farar Shadda yayi kyau rabonta data gansa tun Ranar da komai ya bayyana..! Agaban idonta Sa"idu ya Shige Dakin Yaya da wata mace suka Sakayo kofa sai taji jiri na Dibanta ta Daga kafa kenan Jirin ya yarfar da ita faduwar da zai yi Sanadiyar shanyewar barin jikinta Guda Daya..!