← Book details Rumana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 34

Sashe 8

Rumana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kirjina ya tsananta buguwa tunanin yanda zanyi dashi nafara Sabida yabani tausayi sosai.
Ganin bawani hankaline dashiba yasani dage rigar barcina sama nakai kirjina daidai bakinshi aiko kamar wasa yafara lasa kamin wani lokaci kuma yafara tsotsa yana dirka nishi na fitar hayyaci.
Zafi ya isheni amma Sam yaki saki gashi yaki canza dayan,Hawayen wahala nafara amma araina nace Allah ya k'ara ubanda ya aikeni.

Dakyar nasamu nasakamishi dayan sannan nafara shafar jikinshi yanda zaisami nutsuwa babu inda hannuna be kaiwa ajikinshi domin gara intemakamishi yasami nutsuwa ko Allah zaisa yabarmu muyi barci.

Irin nishin da gurnanin da yakeyi yasani jin kamar insako fitsari ga azabar zafi da kirjina keyi Wanda bansan ranar sakinshiba.
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 11

Yinin ranar
nayishine cikin kewar inna shiyasama nakasa hakuri har saida, nakira wayar baba nace yabata mu gaisa.
Cikin shagwabar da sai yanzu nasami damar yinta nace inna kin manta dani ko?
"Dariya tayi cikin jin dadi kamin tace ke kuwa autata ya za ai uwa ta mance da 'yarta guda daya? Wannan ai ba abune me yuwuwaba kina raina wallahi har yanzu gidannan bekoma daidaiba munata gyare gyare ya gidan?

" Lafiya lau innata.

"Yauwa auta babu dai wata matsala ko?

" Babu komai inna ammadai nayi kewarki Allah.

Kuma gyara zamanta tayi kamin tace hakane nima nan har zazzabin rashinki nayi amma nasan ahankali zamu saba karshen watannan insha Allah zaki ganni nida k'awarki dije tunda ita tasan waje,Zanzo inga muhallin diyata, Ya mijin naki kunfara gaisawa dashi ko?

"Murmushi nayi kamin ince eh inna yana kirana duk safiya mu gaisa shima yanada kirki sosai kamar babanshi,Amma kinga da inatajin tsoron wane kalane shi.

"Hakane Ruma ainasan Allah zai tausayama maraicinki bazai barki ki galabaitaba yanzu ki ajiye wayar kije kiyi aikin gabanki sai kuma ankwana biyu dakaina zansa malam ya kiraki saimu gaisa nima ai nasai wayar bandai iyabane shiyasa.
" To inna sai anjima zan jira.

Jin motsinshi cikin daki yacika yawa yasani mikewa na nufi dakin,Watsi kawai yake da shimfidar gadon da filullukan yanawani gunji tare da make make.
Karatun alkur'ani na kunna awayata na lallaba na ajiye gefe nai tafiyata falo na zauna,Tun inajin ifface iffacenshi harnaji shiru shedar sun barshi kenan,Girgiza kaina nayi kamin ince hummmm wallahi bawani hauka aljanune kawai ke kaidamai tunanin,Allah ya sakamaka.

Saida nai sallar magriba sannan Na kira number da Abba yabani ta maman haidar,Kirjina yanata bugawa Sabida tsoron yanda zata tarbeni.
Bani da matsala da kudin waya domin Abban saida yaimin lodi sosai wai Sabida kiranshi ko kiran wani nawa.
Harta yanke ba'a daukaba saida nakuma kira sannan naji muryar wata mata na sallama.
"Jikina har rawa yakeyi Sabida tsoro, Mama ina yini ya aiki?

" Saida tayi Dan jim sannan ta amsa da lafiya lau,Amma bangane me maganaba nadaiga number daga Nigeria ko?

"Muryata ashake nace eh hakane Sunana Rumana.

" Murmushi me sauti tayi kamin tace ah Ashe diyatace sannunki ya kwana biyu ya bakunta?

Cikin jin kunya da mamakin ina tasanni na amsa mata da lafiya lau mama Dan Allah kiyi hakuri ki dawo mama.

Cikin jin dadi tace karki damu Rumana insha Allah inanan tafe kinji ko? Nasan komai akanki domin anyimin bincike kuma babu Wanda yagayamin wata magana ta banza akanki danhaka zandawo gidan nan kodan farin cikinku keda mijinki,Yanzu inashi haidar din yake?

"Yana daki mama amma idonshi biyu.

" Allah yaimiki albarka Rumana Allah ya albarkaci rayuwarku nima nan ba zaune nakeba wallahi kullun addua nakemishi nasan zai warke da yardar Allah ina nan dawowa inda nake aikine sunki bani damar barin kasar amma insha Allah zandawo kedai ki dage da addua sannan ko megadin gidannan kadda ki yadda dashi balle matan gidan idan da halima ki dinga zama bangarenki babu ruwanki da harkar kowa ina k'ara tunamiki karki wasa da ibada domin yanzu duk me harin cutar da haidar tare zai dinga hadawa dake.

"To mama nagode.

" Yauwa sai anjima zan dinga kiranki insha Allah Ammafa banso ki gayama alhaji sai anjima.

Najima ina kallon wayar bayan ta kashe,Muryarta taimin dadi daga gani 'yar gayuce sosai.

Ajiye wayar tayi kamin ta sauke naumfashi lallai Allah ya amsa addu'arta tunda yabawa haidar mace ta gari domin koda tasa akaimata bincike hankalinta be kwantace wai har sai taga ranar dana nemeta sannan zata tabbatar saigashi ko sati banyiba na nemeta lallai dole ta dawo kodan wa innan yara kamin acutar da marainiyar Allah Wadda batajiba kuma bataganiba.

Jin ana kwankwasa kofa yasani dawowa hayyacina daga tunanin dana lula,Wani mutun nagani tsaye Wanda bansaniba.
Kallonshi nake kamin in bude baki saiya rigani da hajiya ina yini Sunana mudi nine mekula da megida kamin akawoki nazo muku sallamane gobe zankoma gida.

Murmushi nayi kamin ince ah sannunka to shigomana.

Zama yai muka gaisa yake kumaban labarin ciwon na megidanshi tare dabani shawarwari nidai inajinshi Sabida dama nasan dole zaifini sanin komai tunda sunjima tare.

Muna nan zaune saiga Abba.
Ah mudi kana nan kenan? Cewar Abban.

"Eh wallahi alhaji nashigo yima amarya sallama da megida insha Allah lokacin da zan dawo megida ya warware.

" To Allah yasa aimungode sosai da temakonka Allah yasaka da Alkhairi ammadai nacemaka ka dinga waiwayomu Dan Allah.

"Insha Allah alhaji kadda ka damu ai anriga anzama daya.

Sai lokacin Abba ya zauna na gaidashi kamin yace Ruma yame jikin anfara samun wani cigaba kuwa?

Murmushi nayi kamin ince kai Abba daga farawa?

Duk dariya mukayi kamin yace to aikinsan mu mutane akwaimu da garaje nidai Allah ya nunamin ranar da zanshigo nan inga haidar zaune cikin hankalinshi.
Da ameen duk muka amsa.

Duk saida suka lek'a sukaga haidar din Ashe barci yayi sannan sukaimin sallama suka wuce nikuma na rufe kofata,Saidai ko zama banyiba naji ana kuma bugawa.
Nayi tunanin ko Abbane yai mantuwa amma ina budewa sainaga wata mata tsaye da kula ahannu tanamin murmushi.
Banyi niyyar bata hanyaba domin tashigo danhaka anan tsayen nafara gaidata.
Itaba bata damu da shigowarba Dan muna gaisawa ta mikomin gashi farfesune nayo muku keda megidan naki.
Saida na duka har kasa sannan na amsa gamida godiya, Tana wucewa nabi bayanta da harara domin haka kawai naji hankalina be kwanta da itaba.

Farfesufa har farfesu domin kamshin da yakema kawai abin dadine amma zuciyata nagayamin Allah kadai yasan surkellen da akai ciki duk kwanakin danai gidan ko ruwa babu wacce ta kawomin kaini yanzu hakama bazan iya bambancesuba amma shine hadda wani yomin to ai ba mayya bace.

Cikin Leda na juyeshi sawu na daukewa najefa cikin babbar bolar gidan nadawo na rufe kofata.

Ayanzu wajan watana daya kenan cikin gidannan babu abinda nanema na rasa na canza naiwani kyau nasamun hutu babu ruwan matan Abba dani balle ince sun dameni,Abba kullun zai shigo so biyu dubamu indai yana k'asar da safe dakuma dare.
Kula da haidar be zamemin wani aikiba domin ayanzu na saba inyimishi wanka da sauran bukatu wani lokacin inacin bugu wajanshi amma wani lokacin sai inyi sati be kaimin buguba tunda abun zuwane.
Ance ko mahaukaci yasan me kuladashi yanzu da kanshi yake zuwa kusa dani ya zauna babudai magana sannan idan yafara kallon waje saiyai kusa minti talatin bedenaba wani lokacin ma saina kaudamishi kanshi.
Magani dai yi akeyi amma saidai ahankali ni nakeganin saukin tunda inatare dashi amma Abba kullun cewa yake shifa bega wani canjiba
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 10

Inacan nai nisa
wajan tunanin yanda zanyi mishi kawai saidai naji tallatsin ruwa ajikina,Tsalle nai nakoma gefe ina maida numfashi,Ashe wai fitsarin ya fallatsomin Sabida bugashin da yake da hannunshi.
Addu'a nafara duk kalar wadda nasan ta Neman tsarice tare da kariya daga shaidanu sannan na matsa kusa dashi hadda yin bismilla na mikamishi hannuna so nake inga zaizo wajena.

Yajima yana kallon hannuna kamar me karanto wani Abu sannan ya maida hannuwanshi bayanshi ya kauda kai ga barin kallona.
Janshi nai zuwa toilet din dake dakin na antayamishi ruwa daga sama har kasa sannan na rufe idanuna na zaremai wando nai gaggawar saka mishi na hannuna shidai yana tsaye batani yakeba.
Yayinda nakejin kirjina kamar zai faso Sabida tashin hankali,Oh rayuwa kenan kowane bawa da kalar tashi kaddarar Allah kasa mucika da imani.

Wani dadine ya kamani lokacinda naji alamar katifar dakin me ledace wato idanma zaiyi fitsari saidai ashare,To da sauki nasami saukin aiki.

Sai wajan Tara na dare sannan Abba yadawo kawo magungunan kamar yadda yace.
Rubutune jarka guda sai Wanda za adinga badamishi idan zai wanka sainasha sai kuma wani kamar ruwa amma kamshi yake sosai shine Wanda za adinga shafamishi idan zanyi barci.
Saida yagama nunamin tare damin bayani sannan yadora da cewa"Saifa kin daure Ruma domin jihadi zakiyi sannan Dan Allah kema kadda kiyi wasa da addua Sabida yanzu nidai nafara sakankancewa da sharrin mutun.
Saida ya shafamai na Daren yau din sannan yabashi wata karamar kwaya wacce ke temakamishi wajan yin barci akan lokaci Sabida gudun tashin ciwon,Sannan yaimin sallama.

Tsayawa nai na gyare inda yabata sannan nakoma dakina na canza kaya tare da Alwala .
Harna kwanta saikuma hankalina yaki kwanciya naita tunani kala-kala daga karshedai mikewa nai tare da daukar alkur'ani na na nufi dakin.
Yanata barcinshi kamar me hankali fuskarnan gwanin kyau domin har saida naji kirjina ya buga,Na kalli faffadan kirjinshi mecike da gargasa lallai inbacin yana cikin wannan lalura nasan yafi karfina kilama ko kallona bazai iyayi ba.

Can gefe na rakabe bayan nagama kallonshi nafara karatu cikin tsananin sanyi da Neman temakon ubangiji akan wannan lalaura ta wannan bawa nashi.
Banjima da fara karatunba yafara motsi tare da juye juye kamar na meneman dauki kasancewar nariga nayi hadda kawai saina maida hankalina akanshi nacigaba da karatuna ammafa zuciyata ahautsine take tun yana motsi da mutsu-mutsu har saida yagaji yabari lokacin ina gabda gama bakara.
Saida naga barcinshi yai nisa sannan nikuma nasamu na raba gefenshi na kwanta bayan na tofeshi da addua.
Chapter 8 · 0% Book details