← Book details Rumana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 34

Sashe 24

Rumana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shima wankan yayo bayan ya zaunar dani gefen gado.
Zama yai kusa dani bayan ya fito ya riko hannuna yanadan matsawa "Sannu kinji ina kemiki ciwo yanzu?

Kaina kawai na girgizamishi wasu sabbin hawayen na ziraromin.

Jiyai duk hankalinshi yatashi ko wani mummunan Abu ke damuna,Matseni yayi jikinshi yana shafar bayana,Kiyi hakuri kinji gayamin mezaki yanzu in samomiki kadda dare yayi ko?

Jinai kawai bakina ya furta tuwo zanci shi nakeso.

"Idanunshi ya fiddo kamin ya shafa kaina" Tuwo Ruma?
Cikin shagwaba nace eh ko bazan samuba?

"A a jira insa kayana inje wajan umma nidai wallahi bansan inda zansami tuwoba yanzu ni nama manta da munada nau'in abinci mesunan tuwo jira ina zuwa.

Kwanciya nayi tare da lumshe idanuna,Inajin shi ya sumbaci goshina lokacinda zai fita.

Cikin damuwa ya k'arasa wajan umma.
Zama yai yana sauke numfashi iyayen duk suka bishi da kallon kauna,Kamin umman tace " lafiyarka kuwa?

"Ajiyar zuciya ya sauke kamin yace " Umma ruma tafara amai duktai laushi kuma wai yanzu tuwo zataci.

Wata kabbara Abban ya dauka kamar meshirin kiran salla duk suka bishi da kallo kamin ya kauda kanshi yana murmushi ganin yanda duk suka zubamishi ido.

Jinjina kai umman tayi kamin tace to yanzu ina zamu samu tuwo? Indama inada garine sai inyimata ko?

Shiru sukai kowa da tunanin da yakeyi,Kamin Abban yace bari inje wajan malam habu megadi nasan baza a rasaba tunda ina gani yaranshi na kawomishi wani lokacin.
Bayan fitar Abban sai ya lalubo wayarshi ya dannama harun kira, "Kai ango yane?
Cikin basarwa yace oho maka Dan Allah yau hajiya tayi tuwo?

Wani uban ihu Harun din yayi kamin ya tashi Yakama rawa duk da cewa shine Wanda ya tabbatar da samun cikin amma beyi tunanin za afara wannan artabun da wuriba, Shi kanshi yanason aure to Amma daya tuno irin wahalar da yayunshi kesha wajan laulayi da yanda mazansu ke zarya tsakanin gidansu saiyaji kasala da tsoro Dan kaf yayunshi babu meyin laulayi me sauki watama saidai ta dawo gida.
"Hello kana jina? Cewar haidar jin Harun din shiru.

" Eh inajinka,Aikasan hajiya bata rabo da tuwo bari inkawo yanzu kace babynmu me karfine tunda yafara bukatar tuwo tun yanzu.

Kallon Umma yayi wacce ta zubamishi ido tanajiran taji ansamu kokuwadai tatashi ta saba hijab.
Cikin Dan basarwa yace umma Harun zai kawo yanzu.

Saida me gadi ya idasa addu'anshi Sannan Abban yaimai bayanin abinda ke tafe dashi.
Cikin farinciki malam habu yace Alhamdulillahi,Ashe munsamu k'aruwa to Allah ya inganta yasa arabu lafiya bari inleka gidan nasan baza a rasaba insha Allah.

Godiya Abban yaimishi Sannan yakoma cikin gida bayan yaji megadin ya rufe kofar gidan tabaya.

Wata matsanciyar sha'awar tuwon ta tasomin jinake kamar idan banciba zan mutu,Hijab dina na sagala na nufi wajan umma ina kuka ko fahimtar haidar din yana ciki banyiba Sabida yanda idanuna suka rufe.

Tuni umman ta mike jikinta har rawa yake haka Abba da haidar, Jikinta nashige ina sauke numfashi.
Lallashina tafara kamin tace menebne?
Cikin sheshsheka nace umma nace zanci tuwo amma har yanzu bedawoba nikuma yunwa nakeji cikina harya fara ciwo.

Kusan atare Abba da haidar din suka mike daalama jin cikina yafara ciwo yasasu rudewa.

Atare suka fice daidai lokacin Megadi yashigo da k'aramar kula hadda hajin jego.
Abban ya karbo sukaimai godiya atare suka dawo falon har lokacin umma na rungume dani tana lallashi bakinta har kunne surukarta tafara laulayi.

Kular Abba ya ajemin tare damin sannu,Ko jiran umma data tafi dauko filet banyiba na bada yajinnan nakama cin tuwon kamar Allah ya aikoni ni kaina bansan inacin tuwo hakaba Dan damacan bawani damuna yaiba.
Hatta 'yan kasusuwan dake ciki saida na taunesu tas Sannan nai gyatsa wani irin sukuni da kwanciyar hankali naji yana saukomin,Bansan lokacinda na lumshe idanuna ina murmushiba.

Sukansu dake kallona ko wanne sai fuskarshi ta cika da murmushi musamman Abba Wanda har wata kwalla ke tarar mishi cikin ido Anya befi haidar son cikinnan ba?

Saida nagama hutuna sannan na bude idanuna aiko wata matsananciyar kunya ta kamani ganin yanda duk suka zubamin ido suna kallona.
Boye kaina nayi cikin cinyoyina ina murmushi saikace banice nagama kukaba.

Harun ne yashigo falon,Duk aka gaisa sannan ya zauna na gaidashi shima bakinshi har kunne yakemin sannu kamin ya ajiye kulolin dake hannunshi.
Tare duk suka fice Sabida sallar isha'i da ake niyyar kabbarata.
Nima anan nayi sallar wajan nakoma na zauna jin cikina nakeyi har kirji Sabida yanda nai cin tsiya to ban sababa ni bammasan nayiwannan mugun cinba saidaga baya danaji cikin yaimin wani hake hake.

Harun wucewa yai gida Abba kuma fita hai haidar ne kawai yadawo kuma nan wajan umman yayi zamanshi bayan yaci abinci suka dasa hira,Nidai inajinsu kawai.

Wani uban nama Abba ya dire agabana sai baza kamshi yakeyi,Yace gashinan Ruma kici ki koshi megadi nabiya Wanda kika cinyemai saina karo miki.
Boye kaina nayi ina dariya,Suma duk dariyar sukeyi.

Haidar ya daukar min ledar da kulolin tuwon da Harun ya kawo mukai bangarenmu.

*** ****

Hanani cin naman yayi wai cikina zaiyi nauyi da yawa Saidai na wanko bakina nazo kusa dashi na kwanta.

Mun kwanta shiru naji babu wani bayani da alama yau yayi niyyar barina sainaji duk babu dadi bansan abinda yahau kainaba naji kawai shinake bukata.
Kirjinshi nafara shafa Ahankali ina lumshe ido aiko nan da nan bugun zuciyarshi ya sauya amma danya tabbatar saiya kama hannuna ya rike.
Kukan shagwaba na sakarmishi tare da murza kafafuna cikin nashi domin dama aharde suke.

Rungumata yayi yana jijjiga tare da furta sorry kinaso ne?

Kuma shigewa nayi jikinshi batare danace komaiba saidai salon danakemishi shiya tabbatar mishi da abukace nake domin bantaba kwatantamishi hakanba.

Idanunshi alumshe yace"Ruma karfa ki amayemu da tuwonnan wlh!!

Nidai banza nai dashi shima dole yai shiru yafara biyamin karatun danakejin shi kadai zangane alokacin.

Saida tafiya tai nisa sannan nasakamishi kuka,Aiko yanajina amma yai biris saima murmushi dayasaki danya lura rigimace kawai irinta masu yaronciki.
[4/2, 3:09 PM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 47

Tallabeni jikinshi yayi yana sakin k'aramin kuka betaba tunanin cikina biyu bane domin kusan so hudu yanamin scanning amma sh

Hawayen wahala keta ziraromin ga wancan yaron nata son fara kuka gakuma na jikina yaki fitowa duk kokarin da yakeyi.

Muryarshi na rawa yace daure Ruma kadda ya mutu rikeni sosai kiyi nishi me karfi zai fito saiki huta kinji.
Cikin muryar kuka nace "bazan iyaba haidar mutuwa zanyi"

Da sauri ya sakeni yakoma cikin kayan da yake ajewa sabida tsaron lalura irin Wannan saigashi da allura,Acinya yaimin ita kamin wani lokaci nai wani mugun nishi daya fiddo ragowar babyn,.

Wani irin barcin wahalane yai gaba dani kokuma sumewa nayi oho dai nidai bankuma sanin inda kaina yaiba tunda nasamu wannan azababban ciwon ya sakeni.

Jikinshi babu inda be rawa sabida tsabar rudewa sai shafa yaran yakeyi gasu zabga zabga kamar haihuwar daya daya,Saima kokarin kuka da sukeyi.
Dakyar ya jawoma kanshi dauriya ya goge yaran dayake dama kayan haihuwar ashirye suke saida ya gama gyarasu tsaf sannan yaima hasan din sheda sabida kwata kwata babu abinda ya banbantasu.
Kuma saka hannunshi ahancina yayi yaji ina numfashi sannan ya kwashe yaran bayan yasakamusu riguna ya nanndesu cikin bargunansu masu taushi,Addu'a yaimusu sannan ya koma wajena lokacin tuni barcina yai nisa.

Ruwa me zafi yafara hadamin sannan yatasheni,Wani kuka nasakamishi ina kwace hannuna"Nika kyaleni inyi barci"

Cikin lallashi yace "To aidama barcin zakiyi zo ki gyara jikinki yanda zakiji dadin barcin ko?

Saida yaimin allura sannan yaimin wankan da kanshi hatta jinin saida ya rageminshi sannan na idasa gyara jikina nafito. Shikuma ya tsaya wanke bayin Dan na zubar da jini sosai.

Riga da zani nasa na daura kallabina sannan na lallaba kusa da yaran na kwanta wata irin azaba nakeji gabana nayi Wanda dacan banjishi sai yanzu.

Idona biyu har yagama gyaran ko ina ya wanke kayan dana bata da nashi danshima mugu mugu yayi saikace shima haihuwar yayi.
Saida yasa turare sosai bayan ya lullube har fuskar yaran sabida zai iya yimusu karfi,Sannan yadawo kusa dani ya zauna yana sauke numfashi.

" Hannunshi nakamo na rike gam ina hawaye.
"Hannun nawa yacigaba da mirzawa cikin lallashi yace" Kiyi hakuri kindan k'arune shiyasa kikejin ciwo bari in inyimiki dinki yanzu saimuyi barci kinji ko?
Nidai ba baka sai kunne.

Saida yaimin allurai har biyu sannan yaimin dinkin banwaniji zafiba sannan ga allurar hadda ta barci danhaka bankuma sanin me akecikiba.

Ajiyar zuciya yaita saukewa akai akai kamar Wanda yaga halaka ya kufce sai kallon yaran yakeyi wa inda keta barci har hawayen dadi yayi tsabar farinciki jiyake kamar canzashi akayi.

Wanka yakumayi sannan ya dauro alwala yafara nafilfili yana godiya ga Allah dayaimishi wannan kyauta lokacinda beyi zatoba sannan kyautar da babu wani mahaluki daya isa yaimaka irinta.

Saida yai sallar asbahi sannan yasamu ya tsallaka can karshe ya kwanta yaran na tsakiya saidai su motsa su koma.

*** ***

Umman haidar ko zaki leka yarancan ne nifa bansan inji shiru banji motsinsuba kinsan bawani hankali garesuba ko?
Farfesun dake gabanta ta ture kamin tace "Alhaji kadaisan halin haidar da shiririta yaufa lahadi tunda yasan ba aiki zashiba aidama da wuya sutashi yanzu"

"Uhumm kofa sallar asuba bejeba kidaije ki lek'a kokuma ni inje.

Tashi tayi tana " Kai alhaji ko bari inje tunkamin katashi kai gaba,Cikin nan dai ko kai za ahaifar mawa iyakarta kenan!!! Ficewa tayi tana dariya yayinda shima yabita da kallo yana dariya.

Tajima tsaye tana bugun kofar amma shiru babu wani bayani,Da sauri ta juya Dan dauko key din dake wajanta Dan lokaci guda zuciyarta tafara gayamata ba daidaiba.

Ganin tashiga amatukar rude yasashi biyota data dauko key din,Ko ina lif babu haske duk da cewa Tara na safe yama wuce.
Tsaye sukai tsakiyar falon suna sallama nan ma shiru.
"Bafa tsayawa zakiyiba binta shiga zakiyi kiga ko lafiya nikuma zanjira nan.

Dakin datasan munfi amfani dashi ta nufa zuciyarta inbanda matsanancin bugu babu abinda takeyi,Fatanta daga alkhairi ba sharri ba.

Innalillahi wa inna ilaihirraji'un Alhaji zokagani Dan Allah.
Lokaci guda salatinta ya karade gidan,jikin Abban har rawa yake wajan afkawa cikin dakin wani irin burki yaja lokacinda ya fahimci metake nunamishi.
Chapter 24 · 0% Book details