← Book details Rumana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 34

Sashe 29

Rumana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanana hamsin daidai muka nufi maska,Anan ne nazaga dangina na uwa Dana uba kowa sai nan nan yake dani,Yayinda 'yan uwana suketa k'aramin gata da kayan gyara irin namu na mutanen kauye.
[4/2, 3:09 PM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 56

"Kinga tashi muje asbt yanzu in aunaki nan bani da abun awo ko daya tunda bankawo hakan nan kusaba.
Wani irin sanyi jikina yayi danhaka saida ya temakamin sannan na shirya yana gaba ina bayanshi ko umma bamuyima sallamaba inaga saidai taji tashin mota.
Kuka na dinga saki cikin motar shiko ai dif yayi jiyake ko kwarin lallashina bedashi.

Kai tsaye key din office dinshi yasa yabude yashiga sannan yafita ya nemo abinda hake bukata yau babu wani cikowa ko likitoci tunda yau asabar,Danhaka anace yaimin komai cikin hukunci na lillahi saiga ciki harna sati biyar.

Zaman dirshan nayi gabanshi na bude bakina gaba daya ina kuka hadda murza k'afafuna Dan Allah yasani nagama rudewa da tashin hankali.

Rungumoni yayi jikinshi yana rufemin baki,Amma ina fisgewa nake kokarin yi Dan inyi kukana sosai.

" Wai kiyi shiru mana ko kina tunanin kukan zai samar da mafita ne nace kiyi shiru amma sai kuma bude baki kikeyi saikace su Abdul"

"Nidai koma menene wallahi bazan yaddaba kaga babu Wanda yasa dashi ka temaka ka zubarmin kamin asani Dan Allah.
Bedece komaiba yana rungume dani Saima tunani daya tsunduma yasan tabbas abun zaimin yawa ga shayarwa ga ciki sannan ga dawainiyarshi danshi kanshi yana jinjinama k'okarin danakeyi wajan daukar lalurarshi domin shi kanshi saidaga baya ya tantance kalarshi,Yasan ina kokari dashi sosai tunda ban gudunshi duk wuya saidai idan nagaji inyimishi kuka,Da kuma ya lallasheni shikenan.
To Amma idan yace zai zubar da cikinnan yana hango tashin hankalin da Abba zai sasu ciki bama wannanba idan kuma garinzubar da cikin matsala tataso sai yace me? Kai akwaidai matsala.

Allurar tsayar da amai yaimin yace intashi muje gida, Tuni na daina kukan Dan tunanina Allurar zubar da ciki yaimin.

Ajiyar zuciya naketa saukewa cikin motar yayinda shikuma yake kallona akai akai Sabida tare dajin tausayina.
" Akwai abinda kike buk'atane in tsaya insaimiki?

Kaina na girgizamishi kawai batare danai maganaba.

Umma taso ta fahimci akwai matsala amma dayake uwace ta gari Sam bata matsamanaba saima yaran datahana suzo su damemu.

Bunu-Bunu zanje induba jikina amma babu jini babu alamarshi saima tashin zuciya daya addabeni,Shidai yana kallona amma koso daya bemin maganaba.

Haka na yini cikin kunci da damuwa awannan rana Wanda shima rashin walwalata yanashi sukuni.

Da dare bayan nagama shayar da yaran ya kwashesu ya kaima Umma,Lokacinne takasa hakuri ta tambayeshi"Haidar mekaima rumah yau gaba daya bata cikin walwala?

Miyau ya hadiye kamin yace "Umma mundan sami sabanine amma nabata hakuri.

" To shikenan Allah ya kiyaye gaba Dan Allah ka dinga hakuri kaga Kaine babba yarinyar nan tanada hakuri da kawaici,Allah yaimuku albarka ya kade fitina tsakaninku.

Rungumeni yayi jikinshi yana sauke numfashi cike da kwadayi da son kasancewa dani,Amma abun mamaki jinai wani irin kunci da damuwa ya dabaibayeni har bansan lokacinda na tureshi daga jikina ba.

Da mamaki yatashi zaune tare da kunna kwai haske ya gauraye dakin,"Lafiya Rumana?

Wata uwar harara na wurgamishi kamin ince"Au wai tambaya kakeyi? To wallahi bazai yuwu in zauna banda aiki saina ciki da rainoba dama nasan yanda kake rarukata babu yanda za ai ciki yaki shiga tunda bawai tausayine dakaiba to wallahi ka zubar dashi danni banso bankuma shiryama wata wahalarba yanzu.

Hasken ya kashe fuskarshi cike da damuwa ganin yanda yau daya kawai duk na yamutse amma bazaiso infaramishi rashin kunyaba.

Matseni yayi jikinshi da karfinshi ya kwanta dani Dan inagama hadda mugunta ya hadamin Amma ko qala beceminba game da maganar danayimishi ta ciki.

Asubama haka ya gwadamin karfinshi haryasami nutsuwa sannan ya kyaleni duk da irin kukan da nakemishi kuwa.

Safiyar lahadi nan ma beje ko ina ba iyakar tashin hankali yaganshi Dan tasashi nayi da kuka da bakar maganana har saida na cikashi ya fallamin wani lafiyayyen mari,Wanda ya tilastamin shiga nutsuwata batare Dana shiryaba ammadai bandaina kukaba.

Cikin wata irin zuciya yafara magana Dan nagama hasalashi"wallahi baby bayan inajin tausayinki dasaina lallasaki gidannan da wanne kikeso injine? Tun jiya kwana nayi Neman mafita amma bansamu yaukuma tunsafe kintasani da fitini kalli yanda yaranki ke kallonki dazu har baki kika fasama abdurrahim babu gaira balle dalili ga kukan banzanki Wanda ke tafasamin zuciya,So kikeyi zuciyata ta bugane ina jiye miki damuwa da tashin hankali kinakuma kai kanki ko? To tashi muje wajan umma tunda ni ban isa dakeba.

Fuuuuu ya yayi waje da yaran harwani huci yakeyi tsabar yanda ranshi yake bace.

Ko sallama beyiba haka ya diremata umma yaran ya fice duk irin kiran da abban kemishi besa yadawoba.

Inda nake ina kuka ya isa wata irin figa yaimin duk irin tirjewar danakeyi besa ya sakeniba saida ya isa falon umma to suma duk tsaye muka taddasu,Wani hantsalani yayi gabanta yana huci.

Wani irin shiru falon ya d'auka sai sautin kukana danakeyi kadan kadan,Yayinda suka zuba Mishi ido ganin yanda yake huci kai koni bantaba ganin fushinya irin na yauba iyakar zamana dashi,Sosai tsoranshi ya darsu cikin zuciyata.

Ruwa umma ta debo tabashi yasha sannan yafara sauke numfashi Ahankali.

"Meya faru? Cewar Abba dake rungume da yaran dansuma sun tsorata tuni suka lafe jikin Abban.

Yajima cikin yin shiru kamin yace" Abba Ruma Sam batajin lallashi ni bansan yanda takeso muyiba sotake dole saitakaini karshe naimata abinda bata zataba sannan hankalinta zai kwanta!!!

"To ai ance meya hadaku har rayuka suka baci haka? Cewar umma wadda ke kusadani zaune.

" Cikine da ita wai dole sai an zubar dashi"

Agigice duk suka mike musamman Abba Wanda har ya kawo kusadani,Batare Dana fargaba ai tuni nai baya atsorace ina kuma sakin kuka.
[4/2, 3:09 PM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 52

Nai mamakin ganin kiranshi domin idan ban mantaba to lallai inaga munfi sati bamuyi waya dashi ba saidai ya kira inna su gaisa ya tambayi yara amma bazai nemeniba,Yayinda nima na tattareshi na watsar sabida haushin fushin daya dauka dani babu gaira balle dalili.

Ina kallonta harta yanke wani kiran yakuma shigowa,Nan ma banza nayi da wayar haddama harara tasamu kamar haidar dinne ke gabana alokacin.

Wani huci ya fitar me zafi kamin ya kuma danna kiran kenan harya gama kure hakurinta,Lallai idan hakane be kyautaba,Kuma inda ya dauki shawarar harun da abin bekai hakaba.

Saida na mula na mulmule sannan na d'aga wayar kuma nai shiru abuna,Jira kawai nake inji yaukuma dawata masifar yazo.

Ajiyar zuciya ya sauke kamin ya furta"Babyna kinyini lafiya ya twins?

Bakina na tabe kamar yana gabana kamin nace "Lafiya lau ya aiki?

" Lafiya lau babyna ya maskan?

Hararar Abdurrahim dakeshan nono nayi kamin jin yanda yake janshi kamar sai janye ruwan dake ciki duka,Kamin nace "Uhumm Ashe kasan munzo maska?

Ganin dai yanda hirar tamu take duk sai ahankali sai kawai ya kuma tambayar yaran yaimin sallama.

Tagumi ya zabga yana mamakin fushin danake dashi saida yai dogon tunani saikuma yaga ai duk laifinshine tunda shi yafara,Amma yasan ahankali zai shawo kan komai.

Niko murmushi nayi dannafahimci jikinshi yai sanyi sosai,K'wata nayi kamin ince dani kake magana wallahi ni bazan dauki wannan zuciyar takaba.

Satinmu daya amaska muka koma bakori da kayan arziki niki niki.
Koda muka dawo bawani zama mukaiba sabida shirye shiryen komawa kullun umma saita tambaya to nadai sami wadataccen gyara ko? Nidai sai dai inbita da eh cike da kunya.

Kuma gaskiya inna tai kokari dan ko farfesun kaji inaga naci yafi na kaza shabiyar haka caccabi ni kaina inaji ajikina dan gaskiya ni kaina nasan na gyaru.
Magunguna kuwa wa inda inna ta daka da kanta sannan sune suka zama kamar yajin cin abincina kai innafa tasan takan duniya.

** *** **

Irin gyaran da bangarena ya diba sai mutun yai mamaki kullun cikin gyare gyare yake yahana kanshi sakat tsabar zumudi duk da cewa yana zullumin haduwarmu tunda yasan cewa fishi nakeyi dashi,Ammadai ya k'udure komadai menene yasan zan huce indai nadawo din.

Ranar da zandawo kuwa ai hana Harun sakat yayi tun safe yadameshi da kira dayake shine Wanda zai daukomu.

Nagama shirina tsaf haka inna tagama kintsamin duk abinda tasan zan buk'ata duk da umma da Abba sun gargadeta akan kadda taimin wata wahala daban amma ina saida ta hadamin kayan da ake raka mejego dasu da yawa hadda dan akuyanta ta yanka aka soyeminshi.
Dijee na hadama kayana sosai da wasu danabarma inna din da atanfofi kozata dinka hakama baba nabashi kudi sosai dan tuni ansaimin fili da kudin danasamu wajan haihuwa gakuma ragowa da inna tace sai azuba kiwo.

Anshiryasu cikin kayan sanyi sabida iskar mota yaran sunyi wayau fiye da tunanin me karatu har wasa sunsani dan sunfara dariya sunyi wata irin kiba kamar sunyi watanni hudu ko biyar nan ko watansu biyu da yan kwanaki kawai.
Jinai kamar insaka ihu lokacinda harun ya iso,inna ta tarbeshi sosai saida ya huta sannan ya shirya kayanmu cikin motar har baya dole saidai wajan zamana ya kasance gaban motar dan sosai kayan sunyi yawa waifa damma narage sosai nace abawa mabukata.

Rungumar yaran yayi yanata murna da santin yanda suka koma ko wannensu idanunsu k'yar tsabar wayau sai dariya yakeyi dajin dadin ganin yaran balle dayaimusu wasa yaga sunyi dariya.
Kallona yayi yana dariya gaskiya madam haidar yaimiki wayau yo ai naga babu ta inda yarannan sukaimiki kara ta dauko wani kamanni naki kin lura da hakan kuwa?

Nidai murmushi kawai nayi,Dan ni kaina ina mamakin irin kamannin yaran da mahaifinsu.

Saida yaima inna kyauta ta girma sannan mukabar garin bakori munbar inna da sharar hawaye bata taba tunanin zanjawomata arziki irin hakaba,Saigashi dabata haihuba Allah yabatani kuma tanajin dadi.

****

Tafiya tayi nisa na sakasu cikin hijab sabida iska amma yarannan sukace ba hakaba saima uban ihun da suka sakamin lokacin guda gashi nasaba da inna na temakamin aduk lokacinda suka fara rikici.
Jinai kamar insakamusu kuka lokacin dole saidai ya faka motar ya rikemin daya sannan naba na hannuna nono saida ya barci sannan na lallaba na kwantar dashi ajikina na amshi na hannunshi,Kusan atare muka sauke ajiyar zuciya nida Harun din lokacinda yaran sukai barci kamin yacemin "Sannu da k'okari madam Allah yasa masu jin kammune!
Chapter 29 · 0% Book details