← Book details Rumana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 34

Sashe 13

Rumana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida yagama duk abinda ya kaishi harma ya turo da kayan Nigeria sannan ya nufi India cike da kwarin guiwa domin tuni yagama duk binciken daya dace kai daidai da gidan da umman take zaune saida yasani lokacin fita aikinta lokacin dawowarta kai da duk ma sauran shige da ficenta.
Kwalliya yasha kamar zashi zawarci sai bula kamshi yakeyi saidai tuni zuciyarshi ta dade da hautsinewa musamman da yake tunanin wace kalar tarba zai samu sannan ya zaiganta.

Numfashi ya sauke me karfi lokacinda yaganshi tsaye kofar gidan,So wajan biyar yana kai hannu zai kwankwasa sai yaji tsoro ya kamashi,Saida yaga hankalin masu wucewa yafara yowa kanshi sannan yai shahada ya kwankwasa.
Jin motsin taba kofar za abude yasa kirjinshi yai wani irin mummunan bugawa Wanda har saida yakai hannunshi yadafe.

Ido biyu sukai da ita lokacinda ta bude kofar,Kallon juna suka tsaya yi kallo irinna tsantsar mamaki.
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 15

Alokacinda garin
Allah ya waye har kosawa nayi inji kiran malam liman musamman danaga har rana tafito.
Kudi nabada aka shiryamana kayan kari me kyau musamman Harun Wanda besa da wa innan gargajiyan ba tunda anaji da gayu ga dukiya Allah ya hore.
Saida nagama shiryawa tsaf sannan kiran malam liman ya iso gareni.

Jikina har rawa yake tsabar sauri,Zama nai gefenshi na gaidashi kamin inbude kunnuwa domin jin yanda zance zai kasance.

Yajima cikin yin shirukamin yace"Alhamdulillahi dukkan godiya ta tabbata ga Allah insha Allah komai yazo da sauki ummu ruman domin Allah ya gwadamin komai yanzu ga magunguna nasa anhadomiki Wanda zakije dasu wa'incan jarkunan kuma duk rubutune nida su saminu mukayi shi jiya domin ban kwantaba har saida naga komai yamin daidai,Yanzu bin komai za ayi ahankali kadda ayi gareje domin tabbas akwai sharrin jinni cikin hidimar ga sihiri Wanda tuni aka kaudamishi da tunani Wanda wannan shine za adan dauki lokaci kamin ya warware amma sauran matsalar inshaAllahu kamin wa innan magungunan sukau Allah yayi maganinta.
Wannan nakine sha zaki dingayi kullun in zaki kwanta sannan ki dage da addua kinji ko?
Wannan aruwan wanka zaki dinga sawa kadan aimai wankan har kanshi ma'ana ko ina da ina, sai wannan kidinga fesamishi idan zai barci komi kokwawarshi kadda ki barshi insha Allah duk zasu gudu su barshi.
Babu ke babu sauraren kade kade da wake wake domin yin hakan shine zaisa kosun tafi su dinga kokarin dawowa,Wannan kuma rubutunne yakasance ruwan shanshi,Kicigaba da hakuri insha Allah wataran sai labari sannan kibar wannan maganar amatsayin sirri lallai kadda ki yadda wani yasan maganar nan balle taje kunnen iyayenki na dangin babanki kinji ko?

Kaina akasa na amsa da to insha Allah zan kiyaye Allah yasaka da alkhairi ga wannan Dan Allah sai adinga mana sadaka lokaci zuwa lokaci wannan kuma sai asallami su yaya saminun domin samun lada da warwarewar matsalar.
Saminu Dan yayan mama ne kuma shima masanine sosai afannin addini shike temakama malam liman da wasu abubuwa sabida hali na tsufa.

Wayar Harun na kira nace yashigo dakin malam inaciki sabida in nanata maganin agabanshi kadda sainaje gida kuma in manta.

Ina cikin mishi bayani sai kawai muka tsinci muryar IYA tana rafka sallama.
Da sauri malam yace zuba wa innan aljihunka Haruna zansa akaimuku sauran mota,Wannan tsohuwar yanzu saitai tunanin wani Abu daban.
Da sallama ta hankade labulen tashigo tana sannunku malam Ashe ana ciki da jikalle ai naji shirune nace baridai inbiyo hanya.
"Dariya yayi kamin yace yanzu take shirin zuwa nan ai na tsaya nema mata maganin miyagune shine Wannan abokin mijin yashigo muke gaisawa kamin shi kegidan yasami sukunin zuwa.
Zama tai kamin tace" Ehfa wallahi ainima ina nan inazuba ido na ganin megida.
Gaisawa sukayi kamin Harun ya gaidata nima na gaidata lokacin harun yabar dakin nikuma tanata kallona tare da cewa shakiyya jiya sainaji shiru baki komaba ko?

Murmushi nayi kamin nace muna hira dasu inna baraka barci ya kawasheni inaga gajiyar hanyace tatasomin.

Saida ta tasani sannan hankalinta ya kwanta anan gidan nabar harun akan ya taddani can saimu wuce.

Duk yanda mukaso muyi tafiyar wuri hakan be yiwuba sabida dangina dasukaita aikomin da irinsu daddawa barkono kubewa kuka da sauran kayan amfani na gargajiya,To shine sai suka bada shawarar gara duk a daddakamin sabida yanda zaifimin dadin amfani.

Gaskiya wannan karan naji dadi zuwan maska domin kowa sai nan nan dani yakeyi,Duk da cewar nasan sabida daukakar da Allah yaiminne ammadai naji dadi tunda adacan babu Wanda yadamu dani balle yayi tunanin farantamin rai.

Sai azahar mukabar maska wannan karan ko kuka banyiba,yo yaushema zanyi wani kuka hankalina yanakan mijina domin tunaninshi yagama illata zuciyata.

Harun yayi kokari sosai sannan tabbas yacika cikakken masoyi domin inda wasu abokanne lallai a irin wannan lokacin saidai su gujeka.
Da kanshi yake kuma bani haske akan yanda zan zauna da ya haidar koda ya warware tare da karfafamin guiwa sabida sosai nake tunanin halin da zan shiga idan ya warware dannsan yafi karfina nesa ba kusaba yo wama zai hada.
Kiran Abbane yakuma shigowa wayata lokacin munshiga katsina kenan.
Rumana baku isoba har yanzu ko?
"Abba munkusa insha Allah lafiya kuwa?

" karki damu saikun iso Allah ya tsare.

Dariya Harun yayi kamin yace kodai oganki ne yahanashi sukuni naji kamar yanacikin damuwa kinsanfa damacan mijinki ko lafiyarshi lau wallahi mugun fitinanne ne.

Fuskata na rufe da hijab dina kamin ince aiko kamar akunnenshi kafadi maganar nan matukar yaji sauki.

Murmushi yayi lokacin yana danna hon get din gida"To shikenan Allah kaimu lokacin lafiya aini haka nakeso nayi kewar fadan my aboki.

Gabadaya ta window matan gidan suka dinga lekenmu nidai tunda na kallesu so daya bankuma kallon ko shashin da sukeba kai bama zasu ganecewa na kalli inda sukeba.
Abbane yafito da sauri yanayimana sannu da zuwa fuskarshi cike da walwala da farinciki.

Duk zama mukai afalona ana gaisawa Abbane ke cewa"ke Ruma Ashe mijinki haka yake da rikicin tsiya wallahi jiya dakyar yasha fura Sam kin yadda dani yayi.

Dariya harun keyi yayinda nikuma kunya takamani kenan shima yayi kewata kamar yadda nai tashi.

Dagashi sai wando gajere na jeans sai karamar riga jikinshi Abba ya kamoshi be ajeshi ko inaba sai kusa dani kunya kamar zan nutse wajan.
Kallona yaitayi kamar yaune yataba ganina kamin yai kwanciyarshi akan kafafuna ya rufe idanunshi,ganin wandonshi da lema yasani cewa Abba ai fitsari yayi ma.

Dafe kanshi yayi kamin yace bansaniba wallahi,Baridai insa asamomuku abinci tukunna kinga Dan gidanki ya ganekifa,Abba ya idasa maganar yana murmushin jin dadi.

Saida sukai sallar isha'i duhu yayi sosai sannan suka shigo da jarkunan rubutun saida naima abban bayanin komai sannan harun yaimana sallama shima Abban sallama yaimin sabida na huta.

Allah yatemakeni aranar nafaramishi amfani da magungunan tunda naimai wanka naimai addua ya bingire barci nima amfani nayi da nawa nai kwanciyata zuciyata cike da samun nutsuwa da farinciki.

Washe gari.
Fitinar haidar tatasheni domin kirjina kawai yake laluba Allah yasa nai sallata tun asuba rigata na dagamishi sama nabarshi da abinda yakemawa.

Saida yagaji Dan kanshi sannan yabarni lokacin har hawayen wahala nayi sabida azabar zafi to be iya abun masu hankaliba balle insan inda ya dosa kai anyama ba tunaninshi abin wasa bane? Kai gaskiya inaga haka haukanshi ta gayamishi.
Barci yakoma nikuma nafice domin hadamana abin kari.na[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 27

Washe gari, Tunda natashi da asuba nake zubar hawaye jikina kamar anyi hadarin mota dani ko motsin kirki banso inyi.

Shima koda yai sallah komawa yai yayi kwanciyarshi yana sauke numfashi dai-dai.
Adaddafe nai wankana Sam banyi tunanin ana samun ruwan zafi agasa jikiba nadaiyi wanka dame dumi sannan nai salla sonai in fice in koma dakina,Amma saida yabari nakai bakin kofa sannan naji saukar kakkafar muryarshi"Karki kuskura kibar dakinnan hajiya.

Komawa nai gefen gadon na kwanta nacigaba da kukana bansan lokacinda barci yai gaba daniba.

Lallabawa yayi ya koma kusa dani tare da rungumeni a jikinshi yana murmushi"Rigimamma kawai.

Wani irin barcine mukai me matukar dadi da samar da nutsuwa.

********

Alhaji nifa shirun yaran nan yafara damuna wlh yo naga har goma nasafe ya wuce amma shiru karfa ya cutarma mutane da yarinya muna nan zaune.

"Nagayamiki babu matsala tun haukanshi na hauka betaba cutar da itaba balle yanzu damukesa ran saura idashe,Saidai ko barcine yaimusu nauyi.

" humm to nidai gaskiya lekosu zanyi wallahi hankalina yana Kansu.
"Nasandai duk dannatashi nabarmiki dakinne kiketa wani fakewa da maganar haidar bansan lokacinda kika koyi rikoba Fatima nayi tunanin komai ya wuce zuwa yanzu.

Kallonshi tai tana kokarin saka hijab dinta" Alhaji kenan kadda kayi tunanin komai be wuceminba domin inda hakane kaima kasan bazandawo garekaba to Amma tunda nadawo aikasan komai ya wuce abinda nakeso dai ka tuna shine haidar beda lafiya sannan dagashi sai matarshi ke kwana bekamata ace har sukai goma nasafe ba aji motsinsuba kuma ayi shiru ko?

"Eh hakane kam to kiyi hakuri bari insa Riga saimu ganosu ko lafiya.

Cikinmu babu Wanda yasan lokaci yaja har haka domin barcin yaimana dadi sosai musamman haidar Wanda ya like cikin jikina duk motsin da zanyi saiya kuma shigewa narasa kalar wannan naci ga jikina ko ina banda ciwo babu abinda yakemin.
D'akin dund'un yake Sabida manyan labulayen dake sake saiwani sanyanyan kamshi dake tashi kuma har lokacin cikin bargo muke.
Natashi kenan naji ana kwankwasa kofar amma tsabar nauyin da jikina yayi sainaji ko motsin kirkima nakasa.

Key din dake hannun abban yasa yabude kofar ko wanne kirji sai bugawa yakeyi da fatan Allah yasa dai lafiya.
Nunamata dakunan yai da hannu " idan basu wannan to suna wancan tare suke kwana.

Saida ta lalubi makunni ta kunna haske ya gauraye dakin sannan ta maida idanunta akan gado inda muke kwance.
Wani murmushine ya kwace mata lokacinda taga yanda yawani makalkalemin kamar wani baby.
"Ah lallai su haidar ansan dumin iyali.

Rumana tashi rana tayi haka kuke barci ko yunwar cikinku bakuji?
Chapter 13 · 0% Book details