← Book details Rumana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 34

Sashe 3

Rumana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Page 4

Durkushe take gaban boka domin baza akirashi da malami ba duk da cewa sud'in sun kasance suna lakabawa kansu wannan sunan na malamai nan kuwa babu aiki daya da suke yi na malanta sai dai bokanci.

"Alagafarta malam akan maganar yaron nan ce nace bari na dawo domin gaskiya haukan nashi naga kamar yana nema yayi sauki, Sabida yanzu sai yayi kwanaki biyar kai harma sati d'aya ba tare da ciwon ya tashi ba sai dai yai shiru ko kuma yayi ta bacci, nikuma sai naga ai hakan kamar alamun sauki ne ko?'' Bincike-binciken shi yayi kamin ya kalleta.

''Hajiya maganar gaskiya dama nagaya miki bake kadai kike yiwa yaron nan sihiri ba mata biyu ne gakinan cikon ta uku ke gama wani mutun can gefe shima ba'a zaune yake ba, abin ya yiwa yaron nan yawa, tabbas inda yana da karar kwana da tuni ya mutu.To amma dan yayi shiru ba sauki bane tunda babu uhm bare uhu-uhm, sannan babu wata alama tame hankali a gare shi.''

Zakud'awa tayi ta gyara zama tace. ''Toh ai malam abin ne kadda dare d'aya muga ya warware mu dai ba zamu so hakan ba gaskiya.''

Kudi masu tarin yawa ta ajiye mishi kamin ta juya ta tafi. Da kallo ya bita yana mamakin hali na wasu matan lallai duniya cike take da tashin hankali da masifu kala-kala. Shi dai yana maluntar nan ne kawai dan neman kud'i amma yasan ba dai-dai yake aikatawa ba.

Hankalinta kwance ta koma gida kai ba zaka ce ta kasance mai mugun nufi ba kasan cewar itace zata karbi girki yau ya sata nufar b'angaren alhajin ba tare data nufi nata ba. Ledar maganin dake jikinta ta zaro bayan ta rufe d'akin bata da wani zullumi domin tasan alhajin yau yana Bakori wajan yayan shi. Dakin ta barbad'e tun daga k'ofa tana yi tana fad'in.

''So nake na mallakeka Alhaji, ya kasance sai abinda nace kawai za'ayi domin banki in zauna da kai kad'ai ba kamin kwananka ya kare na kwashi dukiya ta in k'aragaba.''

Anan inda take tsaye tayi zigidir da ita tare da lakato gabanta tashafa akan wani d'an mitsitsin garin magani dake tafin hannunta ta had'e ta yamutse sannan ta mai da shi aleda ta boye sannan ta shige wanka.

D'akin babu datti ba zaka tab'a cewa wai anyi wani abu cikin shi ba sabida tsabar iya taku.

Tajima cikin d'akin sannan ta nufi b'angaren Haidar tana yi tana kwarkwasa sai kace zataje wajan wani bazawarinta. Kwance ta taddashi yana ta baccin shi da gashi sai gajeran wando da farar t.shat sabida zafi-zafin da ake yi a yinin yau.

Kallo tabishi dashi kamin ta yatsine fuska. ''Oh ji dan Allah a haka kamar mai hankali sai hauka fal cikin ciki dama mutuwa kayi da kowa ya huta kadaina wahalar da ubanka.''

Idanunta ne yakai kan cinyoyinshi ta kalli kwanciyar gabanshi cikin wandon sai taji wata irin kasala ta sakko mata. Bakinta ta lashe kamar tsohuwar mayya kamin tace.

''Oh sai yau na lura ashe shima girma gareshi kamar ubanshi, amman dai daga gani wannan tafi ta alhaji girma.''

Hannu takai a hankali ta shafa mishi abar, tsabar dad'i bata san lokacin da ta lumshe Idanunta ba. Motsawa yayi jin kamar ana mishi waiwayi amma bai tashi ba, ita kuma tuni ta fara nisa da shafar da take mishi sai kawai ta jiyo tafiya daga bakin k'ofa.

Da sauri ta gyara tsayuwarta tayi wani kalar tausayi da ita. Mudi ne ya shigo da kayan Haidar d'in a hannunshi da alama daga shanya ya d'ebo su. Kallonta yayi itama ta kalleshi kamin tace.

"Sannu Mudi ya yarona da jikin?'' Kallonta yayi sannan ya kalli Haidar d'in sannan yace mata.

''Da sauki bacci yake yi.'' Juyawa tayi tare da fad'in.

''Dama lekowa nayi in ganshi daga unguwa nake ma sai anjima a kula da abincin shi dan Allah.'' Ficewa tayi tana cewa.

''Allah ya kai damo ga harawa na san ko baici ba zai yi birgima.''

Hajiya Saude kenan mace mai matukar had'arin gaske ta iya fuska biyu kai ita har fuska hud'u ma ta iya. Da kallo Mudi ya bita har ta b'ace mishi kafin ya girgiza kai dan shifa wallahi matan alhajin nan tsoro suke bashi.

****

Bakori.... Taro ya tashi lafiya kowa sai fad'in albarkacin bakin shi yake yi, Yayin da malamai suke ta yin nan-nan dani domin ba k'ananun kud'i suka samuba ta dalilina banda kyautuna wa inda aka dinga bani hannu da hannu ba, Inna na gefena takasa ta tsare sai yamma lis muka koma gida domin bayan taron ya watsema ni hanani tafiya akayi. 'Yan uwan mahaifina dana Ummana da suka zo tuni suka koma gidan zaman jiran dawowarmu.

Wai dadi kasheni yau inna ce hadda kaimin ruwan wanka bayi, har cewa take. ''Ki gasa jikinki sosai danki sami nutsuwa domin wannan jaganiyar da kikai yawa gare ta, Allah dai yayi miki albarka ya jikan iyayenki.''

Ina wanka ina tunanin anya nice kuwa, ashe dama haka mutum yakeji idan har dad'i yai mishi yawa? ni dai yau gaskiya dad'i yayi min yawa, najima a bayin dan tunani yai min yawa, sai da naji inna na kwalamin kira sannan nai azamar watsawa jikina ruwa na fito ina na fito ta.

Gwanin dadi ta washe baki kamin tace. ''Yauwa 'yar albarka zokici abinci dan ina sane duk yau ko ruwa baki sama cikin kiba.''

Ina fara cin abinci sai ga baba ya shigo da sauri yana fad'in. ''Ina Ruma take d'auko hijab d'inki ga baki zaku gaisa chairman ne yayo aike basu iso da wuri ba.''

Kirjina yai wata irin bugawa nan da nan jikina ya d'auki rawa na fara hawaye.

Dariya suka fara yimin ganin yanda duk na rud'e jikina ya d'auki rawa. Da fani baba yayi kamin yace min.

''Ki kwantar da hankalinki gaisawa kawai zaku yi kinji ko?'' K'anin mahaifina baba Rabi'u shima dafani yayi kafin yace.

''Jeki mana 'yar baba.''

Kamar zasu kamani haka na dinga labe-labe Baba na biye dani yana dariya. Duk'awa nayi har k'asa na gaida su, ban tashi a wajan ba sukaci gaba da sakamin albarka, Lokacin ne Baba yake cewa.

''Ai da yake marainiyace babu uwa babu uba shi yasa sam bata da walwala sosai.''

Nan fa suka kuma cika da mamaki tare da tausaya min, musamman da suka kasan ce manyan mutane kowa cikin zuciyar shi fata yake ina ma ace d'iyar shi ce. Wani kunshi ne suka miko min.

''Gashi wannan tallafi ne daga shugaba, Allah yayi miki albarka yai miki jagora.''

Hannu nasa na amsa wanda yake ta faman yin rawa dan dama can ni haka nake maza masifar tsoratani suke yi balle yau duk jina nake yi a takure.

Kasa cin abincin nayi a haka har dare gidan mu bai rabu da mutane ba anata shigo mana barka da Allah sanya alkhairi.

Cikin dare ina can ina bacci su kuma suna can d'akin inna ana bud'e kyautukan dana samu tare da makudan kud'i wanda yawan su duk sai da ya firgita su da yake akwai kannan mahaifina dana mahaifiyata wa'inda basu tafi ba nan zasu kwana.

**** ****

Alhaji Yusuf ne a zaune shida yayansa suna kuma tattaunawa akan lalaurar Haidar wacce tuni ta gama danne zukatan su da tsananin damuwa.

''Gaskiya yaya Allah ya sani nidai nayi iyakar abinda zan iya yi mishi amma yanda yake haka yake narasa ta yanda zan bullowa wannan larurar gashi har yanzu neman Fatima nake amma babu ita ba alamarta kuma ni wallahi ban saketa ba amma ta manta damu baki d'aya nida yaron ta.''

Numfasawa Alhaji Yahaya yayi sannan yace.

''To Yusufa nikam a wannan gabar ban san abinda zanyi ba kasan dama da kyar da sid'in goshi aka baka auranta sabida suna tunanin matanka zasu iya cutar da ita, Sannan lokacin da ka turani naje labarin abinda suka bani kayiwa ita Fatiman ai babu dad'in ji kuma sunce sunsan sharrin matanka ne amma kafara d'aukar mataki a gidanka sannan su fara tunanin mai da maka da matarka, idan ma zasu iya kenan dan haka ni abinda nake gani a farabi ta neman maganin Haidar d'in tukunna sannan akoma takan Fatima domin ita nata mai sauki ne tunda ta san cewar akwai aure akanta, ka gane ko?''

"Eh yaya na gane, amman ni wallahi da Haidar lafiyar shi lau dana nema mishi auran wannan yarinyar dan ta tsaya min a rai, gaskiya iyayenta sunyi sa'ar haihuwa ta wallahi.'' Murmushi yayi kafin yace.

''WaivRumana kake nufi? Ai haka Allah ya hore mata wannan baiwar kowa sha'awarta yake yi, amma marainiyace nan dakake gani bata da uwa balle uba malam shi ne yake rikonta, amma ko yanzu bata b'aci ba zan tuntubi shi malam d'in idan har zai iya bamu sai muyi dabarar yanda babu wanda zai gane sai ace mishi yaron na k'asar waje karatu muna sone daya dawo ya tararar da matarshi, sabida gaskiya nima hankali ya karkata ga hakan tana da nutsuwa da hankali sannan tabbas zata kula dashi kaga idan ma anfara maganin itace zata tsaya tsayin daka wajan ganin yasha ko amfani dashi, amma wallahi Yusufa banga amfanin wad'annan ruguza-ruguzan matan naka ba nasan kullum makasarka suke nema.''

Shi dai alhaji Yusuf shiru yayi tare da sunkuyar da kanshi k'asa shi abinda yasa ya kasa d'aukar mataki akan su ya zai yi tunda babu wacce ya tab'a kamawa da wani mugun laifi' sannan ko wacce tana kula dashi, shi tsoran shima kadda yaje ya saki wacce bata da laifi amma yasan yana nan yana saka musu ido akan komai nasu.

Zuciyarshi ta cika da farin ciki jin cewa yayanshi zai tuntubi marik'in Rumana ko zai bashi aurenta, lallai yasan Haidar ya gama morewa idan Allah ya bashi lafiya.

****

Cikin wannan dare Hajiya Saude zigidir take haihuwar uwarta agefen d'an k'aramin wajen shak'atawar gidan, wanka take yi da wani koko da magani a cikin shi tana yi tana sambatu tare da kiran sunan Alhaji Yusuf tana nanata sunan matanshi d'aya bayan d'aya, Itakam bata ta Haidar domin dashi da matacce duk daya ne a wajanta.

Tajima tana wannan surkulle sannan ta yafa zaninta tabar wajen bayan ta d'aurewa wajan gudun kadda wani yazo wajan da safe ya gani ya gane.
Chapter 3 · 0% Book details