← Book details Rumana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 34

Sashe 28

Rumana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusan kwana mukai hira kunsandai yanda ake baje hajar hira idan an hadu da 'yan uwa,kusan hirar tamu duk na irin daular da Allah ya kawoni cikine,Musamman da hidimarnan tatashi Haidar yaimin akwati set daya na kayan lefena daban gakuma na haihuwa hakama yaran saida na cika gado da kayan arziki kala kala wa inda dangin umma Dana Abba suka kawo ga abokan Abban haka na haidar din ko Harun saida yayo akwati guda na kayan yara.
Kai abubuwan damuka samu gaskiya sai godiyar Allah.
Shinefa kowacce ke fadin albarkacin bakinta nidai dadi yagama kasheni Sabida farinciki harbansan kalar godiyar da zanyima Allah ba Sabida tako ina sai inga tayi kadan,Sai intuna lokacinda aketa Neman kai dani babu Wanda zai iya rikeni Sabida kawai kadda dawainiya ta karu ma mutun yau gani cikin wannan daula,Allah yabani miji me sona na nunawa asa'a ga surukai na gari, yaukuma ga yara har guda biyu kumafa duk nawa ne lallai Allah shine mabuwayi gagara misali.
K'ara rungumar yarana nayi jikina inajin kaunarsu cikin zuciyata kamar yadda nakejin mahaifinsu.
Nidai bansan sanda barci yai awon gaba daniba yo dama ga gajiya da hayaniya su Kansu anshasu.

** ** **

Tun safe muke kintse kintsen abinda yakamata intafi dashi ga soye soye Wanda damma Allah yasa 'yan uwana da yawansu sannan gana shi haidar sunkama aikin sosai yanda yakamata Dan bamazaka gane wa innena nawan ba.
Amma duk da haka sai bayan azahar sannan akagama shirya komai tuni yaran nawajan Abba ya rungume jikoki yanata gayamusu zaiyi kewarsu sosai da sosai yayinda umma ketamishi dariya Sabida tana tunanin ko abban ya mance da kwanakinsu aduniyane da yaketa musu magana.

Yana nanike jikina Dana motsa saiya bata fuska ni kunyama duk tagama kamani daga zuwa sallama kuma sai aga najima shiyasa inna saitaita fada wai indaina likemishi indai bawani cikin nake bukata da wuriba.
Cikin yanayi na shagwaba nace ya haidar lokacifa yana shigemana ko so kakeyi muyi dare yaranka suyi mura?

Sassauta rikon da yaimin yayi kamin yace"OK muje amma nidai gaskiya ankwareni wallahi dannasan bazan iya jurewaba.

Nidai lallabawa nayi mukai sallama duk da cewa shine da Harun zasu kaimu amotoci biyu sai guda daya da zatakaimana kayanmu,Nidai gudun surutun mutane motar harun nashige nida dijee sai matarshi dake gaba Sabida hadda ita za a rakiyarmu.
Har mota umma na nanata insha Allah sati nasama suna hanya zatazo ganin angwayenta.

Tafiyace mukayita mecike da farinciki da kwanciyar hankali ina rungume da abdulrahman itakuma dijee na rike da Abdurrahim hira mukeyi sosai wadda ta dauke hankalina daga tunanin oga dannasan yananan yacika yabatse banshiga motarshiba.

****

Zuciyata cike da zullumin inda inna zata saukeni Sabida nasan dakina Nada bawani girmane dashiba gakuma baki duk da bawani jimawa zasuyiba Sabida dare yariga yashiga.

Shida tayi lokacinda muka isa bakori, Abinda yabani mamaki shine ganin yanda aka gyara gidan gabadayanshi,Sannan dakin baba nan ne yakoma amatsayin nawa, dakin yasha gyara naban mamaki domin hatta gadon jarirai saida aka saka ga wajan kayansu da kuma kayana dakina saikace na gidan Abba.
Salla kawai sukayi suka juya ko sallama haidar be bari munyiba sabida be huceba.

Nidai nabisu da addua tunda nasan duk damuwarshi.

Suma dangina na maska alokacin suka wuce sabida dare.
Gida yakoma dagani sai inna da dijee itama tanagama tayani gyara kayan taimin sallama bayan nacikata da shatara ta arziki Dan sosai naji dadin zuwanta wajena wlh.

Saidama zamu kwantane sannan baba kemin bayanin ai haidarne yazo da masu aiki akayi wannan gyaran yau kwana uku kenan,Sannan kayan abinci babu kalar Wanda ba ajiyeba.
Nidai sainabishi da addua kawai Dan gaskiya haidar mutunne kuma yaimin halarci fiye da yanda nazatama.

Dagani har yaran kwanciyarmu mukayi Dan angaji gajiya duk ta bugar da kowa.

****

Ranar danayi sati guda agida saiga umma da Abba da uban gayyar domin shine ya kawosu.
Saiwani ciccin magani yakeyi sabida kawai takalen fada,Dama tun tafiyarshi saidai yakirani ya yaranshi danace lafiya lau shikenan saiya kashe.
Nidai bandamuba tunda nidai nasan bawani Abu naimishiba.

Suna rungume da yaran suna mamakin kuma wayansu kamarsu sai kuma fitowa takeyi da ubansu.
Inna kebasu labarin ai yanzu kukan dare sukeyi gabadayansu.

Dariya Abba keyi kamin yace to da alamadai basuson zama dake gidansu sukeso.

Duk dariya akai kiran sallar azahar yasasu barincikin gidan da baba Dan zuwa masallaci daganan su wuce gidan yayan Abban.

Saida nai wankana dayake da wuri inna kesamin ruwan shiyasama bancikayin na yammaba sabida sanyi, Sabanin wasu da zasuyi wankan jego amma sai bayan magriba ko daf da yinda sannan ashiga wankan.

Yaran barinsu nayi wajan inna tunda sun koshi nikuma idan nai salla in kwanta indanyi Dan yanzu sungane rikicin dare.

Ina cikin yin sallar naji sallamar haidar cikin dakin,Kirjina naji yai wata irin bugawa kamar yadda shima abangarenshi hakanne lissafin kwanakina da haihuwa yafara kamin yafara sakin wani munafikin murmushi.
[4/2, 3:09 PM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 51

Kwance nake akan gadona yayinda na Dora abdurrahman saman cikina ina Dan jijjigashi sama sama yau yatashi da ciwon ciki shiyasa rigimarshi tai yawa.
Wayata dake gefe ta dauki ring babu wani jinkiri na dauka sabida nasan waye.
K"asa kasa nakumayi da muryata kamin na rangad'a sallama.

Wata ajiyar zuciya ya sauke kamin ya furta"Nayi kewarki babyna"

Cikin yanayi na lallashi na furta sorry!! Dadynsu ai munkusa dawowa gareka insha Allah danagama yawon Arba'in kamar yadda iyayenmu suka tsara ko?

"Hummm,Shine abinda ya furta kamin ya Dora da fadin" aikema haka kikeso kuma wallahi duk wannan wahalar danakesha saina famshe abuta akanki tunda kinaji kuma kinagani amma yanzu ko yaranama anhanani zuwa gani sabida kadda naimiki wani abu, Sabida anmaida Dan iska ko?

Muryata har rawa take na furta Dan Allah kayi hakuri haba mana kai yanzu shikenan haka zamu dingayi dakai kullun ka kira bazamu rabu cikin dadin raiba sabida fitina irin taka Dan Allah da wanne kakeso inji? Da kai kokuwa da yaranka ?

Tashi yai daga zaunen da yake cike da mamaki lallai Ruma tagama rainashi shi takema fada haka?
"Ke dakata kadda kimin shirme Dan kinga ina binki shine zaki nemi ki tainamin wayau ko? To bazan dauki rainiba idan kuma Dan wannan abun naki kike Neman ki wulakantani to ki rike abinki dan Allah karma ki dawo saiki kwada ki cinye.
Kashe wayar yayi yanajan dogon tsaki toma da wanne zaijine? Amma ai laifin dukna umma ne tamaidashi wani bunsuru ta toshe duk wata hanya dazaibi yaje ga iyalinshi gashi itama yanzu tana nema tafara biyemishi suyita masifar kullun.

Kwantar da yaron nayi gefena ganin yai barci sannan nasaka kuka,Sai yanzu nake kuma sanin halayen haidar,Ashe masifaffene na nunawa ataro ga bak'ar zuciya da fishi Wanda zamana dashi ba haka yakeminba amma yanzu kullun zai kira kuma bamu rabuwa lafiya hakan kuma bazai hana gobema ya kiraba ko bayan wasu awoyi,Narasa kalar lallashin da zanyimishi yaranshi su hanani sukuni da nutsuwa shima ya addabeni da fitinarshi ai shikenan saiku hadu ku kasheni ku huta kuma wallahi tunda kace in kwad'a abuna incinye zanga yanda zaka kuma rabarshi.

Jin sautin kukana ya shigo da inna goye take da abdurrahim Wanda yai barci abayanta.
Yaron dake gefena tafara dubawa taga barci yakeyi sannan ta kalleni "Ke rumana lafiyarki kuwa kike kuka haka kawai ko yauma fadan kukayi?

Kaina kawai na dagamata tare dayin wata sheshsheka.

Haba takama tana kallona kamin tafara sababi" To sakarya zauna kita kuka tunda kika ganin kukan shizai zama mafita agareki banda iskanci bance kidaina biyemishiba? Toma ai yayi hakuri yau kwananki arba'in harda uku lokacine daya kamata ace kin koma amma mahaifiyarshi ta rantse saikinyi kwanaki sittin kodan yara sukuma kwari to tunda anyi haka aisaikita lallabashi ki daina biyemishi tunda shima fitinannena amma inba hakaba duka menene akwana 60 Dan Allah?
Yanzu tashi ga wancan tsumin can yadansha iska ka kafa kai ki shanye anjima kadan Laminde zata aiko da ragowar caccabinki ki cinye Dan wallahi sainaimiki shiri sosai akan wancan sarkin zalamar,Gobema kaji zandafa miki dahuwar amare Dan idan bakiyi shirin gaskeba to inaga kina zuwa zaikimiki kwaf daya.

Gwanin kunya natashi nafice bayan Nagoya yaron abayana sabida yamma tayi.

Ni har mamakin irin gyaran da inna takemin nakeyi,Sabida ita gabadaya kallon fitina'u takema haidar.

Hada kayanshi yafara da niyyar tafiya gida dan dama cikin office yake yagama aiki yace bari yakira,Shi kanshi besan abinda ke tunzura zuciyarshi yanamin masifa ba.

Harun ne yashigo da sallama yanemi waje ya zauna yana kallon yanda haidar din duk yagama yamutsewa gawani uban tsaki dayake jerawa akai akai.

"Haidar wai meya farune duk ka yamutse haka? Cewar harun yana kafe haidar din da idanuwanshi.

Wani huci me zafi ya saki kamin ya kuma yamutsa fuska gamida lumshe idanunshi" Harun baby tafara rainani yanzu wallahi,Wai har ita zatacemin nacika fita nida yarana da wanne zataji!!!

Shima harun din numfashi ya sauke kamin yace gayamin dai meya faru?

"Ka ganene harun kewarta ta dameni wallahi ko barcin kirki bansamu inayi sosai,Ga umma ta rantse saitayi wata biyu sannan zata dawo gashi ta hanani zuwa ganin su dan Allah da wanne akeso inji? Itakuma kullun na kirata saita batamin rai sabida wulakanci kalar nata.

" Kaga haidar wannan duk ba abin damuwa baneba indai kasa kanka,Amma rumana bata da laifi gaskiya itama umma bazamuce tanada laifina dannasan akwai manufarta tayin hakan Amma dan Allah ka tausayama yarinyarnan itace abar tausayi yara biyufa haihuwar fari koda tsotsarsu aka barta ai aikine sannan inaji humaira tacemin basu barinta barcin dare sabida rigima yaukuma babban yatashi da ciwon ciki saida takaishi asbt kaikuma ka kirata ka rufeta da fada mezaisa zuciyarta bazata kuntataba harta gayamaka wata maganar daban?
Yakamata kaimata uzuri dan Allah yarinyace karamafa kuma nasan tunda umma tai wannan tsarin wallahi akwai zalamar daka nuna haka haka kawai amaido yarinya kakuma kunsamata wani ko hutawa bataiba.

Murmushi haidar din yayi yanajin yanda zuciyarshi ke kwanciya tare da tausayin rumanan to Amma meyasa shi batagayamishi yaron beda laifiya ba?Koda yake yasan laifinshine tunda betsayawa ya fahimceta.
Tare sukabar office din yana kuma lallashinya tare da nunamishi duka saura kwana nawa yanzu duk tsiyadai bazata kuma kwana ashirinba batare da tadawoba.

*** ***
Chapter 28 · 0% Book details