Sashe 6
Rumana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Toh ai babu komai ni sai muje dakai har can garin domin neman izini amma yanzu dai ka kiramana ita innar tata taji daga bakina kasan halin mata.'' Cewar alhaji Yahaya.
Tare suka dawo da ita cikin zauran jikinta duk yai sanyi musamman data hangi wata dalleliyar mota daga k'ofar gidan, ga manyan mutane zaune a cikin zauren wanda ya gama bud'ewa da kamshin Alhaji Yusuf domin tasan sai dai shi d'in domin alhaji Yahaya anriga an saba dashi.
Bayani sukai mata dalla-dallah yanda zata gane kafin shi Alhaji Yusuf d'in ya d'ora da fad'in.
"Kamar dai yanda yaya na yai miki bayani yarona yana kasar waje karatu amma ya kusa gamawa abinda yasa nai mishi sha'awar Rumana gaskiya na yaba da tarbiyyarta sannan nasan kowa zaiso ace ya had'a iri da ita, ina fatan zaku amince domin Haidar shi kad'ai ne yarona ina so ya samu mace ta gari.''
Wata zufar farin ciki ne ta zubowa Inna ta ko'ina daga jikinta kafin ta d'an muskuta ta kuma gyara mayafinta tace.
"Toh shikenan insha Allahu komai ba zai gagaraba tunda ba ayi mata mijina ba, sannan ga malam komai nene sai kuji daga gareshi.''
Cike da farin ciki Alhaji Yusuf yabar garin BAKORI bayan yayan shi yai mishi alkawarin cewar a cikin satin nan zaija malam Sulen suje maska domin nemowa Haidar auran Rumana din. (To ruma da auran mahaukaci🤭)
Sai dare ya shiga cikin katsina hankalinshi kwance bakinshi cike da adduar Allah yasa abinda yake son shiryawa ya zama alkhairi garesu baki d'aya.
Mudi yayi murnar ganin shi duk da cewa har sun kwanta bacci lokacin, sai da ya gama duba jikin Haidar d'in yaga babu matsala sannan ya wuce d'akin shi wanda aka gama fesheshi da asirirrika kala-kala.
Da bismillah ya jefa kafarshi tare da bi da ayatul kursiyyu da falaki da nassi domin haka kawai ya farajin fad'uwar gaba lokacin da ya dumfaro d'akin nasa.
Kwance take saman gadon shi tayi dai-dai tana kwasar baccinta, wankanshi ya wuce yayo ya gyara jikinshi sannan ya rab'a gefenta ya kwanta bayan ya gama tofe jikinshi da addu'a.
*******
"Oh gaskiya rikonki ya zame min alkhairi Ruma, Allah ya jikan iyayenki, zanzufa makka zanje sannan ga wannan alhaji da yake so ki auri d'anshi kinga shikenan muda talauci munyi hannun riga ko?''
Turo bakina gaba nai ce. ''Kai inna nidai wallahi bana sonshi kin dai san duk yaran da ake kaiwa kasar waje karatu a iskanci suke dawowa, kuma shikenan saiki aura min wanda bazai tab'a sanin darajata ba?''
"Innalillahi na bani ni Suwaiba, Ruma kina da hankali kuwa? Toh wallahi ahir d'inki da yimana bakin ciki, gobe idan Allah ya kaimu zamuje maska gaba d'ayan mu, saura idan an tambayeki ki musa Allah saina yankaki aikin san zan iya ko?''
Kuka na saka mata nace. ''Inna duk ga masu sona nan a garin nan ga Mansur ga K'asim ga malam Umar kullum nacin tambaya suke yi zasu turo kinaki sai wannan daga zuwa wama yasani ko d'an fillan kai ne.''
Dariya tayi kamin tace. ''Yaro man kaza, to kodai tukunyar tsafince shi gaba d'aya dole shi zaki aura garama kisawa zuciyarki salama, haba Rumana dama fa wallahi ke matar manya ce kinga ban tab'a haihuwa ba ya kamata ki sharemin hawaye na kinji ko? Yauwa Rumana Allah yai miki albarka ai insha Allahu nasan zai kasance nagari domin Allah baya wulakantar da bawan shi musamman ma kuma marainiyan Allah.''
Ina rungume a jikinta ina magana cikin zuciyata. 'Inna ai Allah ne yaga abinda ya gani har ya hanaki haihuwar, dan da yanzu kin tashi BAKORI da tashin hankalinki musamman na san sai kin addabi kowa, ji duk kalar wulakancin da kike min amma yanzu sai wani lallashina kikeyi sabida tsabar son duniya kai Allah ka rabamu da wannan kalar rayuwa.'
Dije ce tashigo gidan da sallama bayan ta gaida innan muka wuce d'akinta ita kuma ta sab'a hijabi tai gaba abinta, domin ita in dai zuwa unguwarta ya tashi toko baban sai dai yazo ya tarar bata nan, na sha nuna mata babu kyau amma inaa wani lokacin ma makemin baki take yi wai tunkafin a haifi uwata takejin wa'azi kai inna ko...!
Labarin walima muka dasa nida dije kafin in kuma matsawa jikinta nace. ''Ke dije kinsan meya faru kuwa?''
Hankalinta na kan kayan sawar dana samu tace.
''A'a sai kin gaya min.''
"Humm kin tuna mutumin da ya bani kyautar kudi da kujerar makka?''
Dariya tayi kafin tace. ''Ai dama na sanshi yana da kirki sosai a katsina yake mai kud'i ne sosai uwar su d'aya uban su d'aya da alhaji Yahaya ya aka yi?''
"Dije kindai san bani da k'awa garinnan saike kuma dake kawai na yadda dan Allah kibani shawara wallahi tun shekaranjiya nake cikin tashin hankali jiya ko baccin kirki banyi ba, kinji wai shine yazo yana nemawa yaron shi aurena kuma wai yaron nashi yana kasar waje karatu.''
Batare dana sani ba naji ta wani rungumeni tana murna kamin tace.
''Alhamdulillah! aiko maganar malam ta tabbata daya ce ked'in matar manya ce, Allah ya tabbatar da alkhairi Ruma wannan ai abin farin ciki ne domin kowa yasan alhaji Yusuf mutumin kirki ne yaron ne dai ban sani ba gaskiya domin sau d'aya na tab'a ganin wata mota tazo gidan Alhaji Yahaya ni kuma zan wuce naji wasu na cewa yaron alhaji Yusuf ne yazo gaida yayan mahaifinshi, kumafa shi kad'ai ne d'an shi, ai kinga dole ya hau manyan motoci, toh ni dai iyakar abinda na sani a kanshi kenan. Amma insha Allah babu wata matsala ki kwantar da hankalinki ki dage da addu'a shawarar da zan baki kenan.''
Ajiyar zuciya kawai na sauke amma sam bana cikin nutsuwata. Kayan da ta gama gani nace.
''Toh ki d'auki ko kala biyu ne dije.''
"Waaa! ni? a'a wallahi wancan hijab d'in dai zan d'auka sabida yayi min kyau shima dan naga kina da kalarshi ne amma da bazan d'auka ba.''
Sai yamma lis sannan muka rabu da ita sabida an bamu hutu na sati d'aya a islamiyya sabida kacaniyar da aka sha.
Washe gari... Kamar yadda aka tsara Alhaji Yusuf ya aiko da mota da direba wanda zai kaimu maska kuma ya dawo damu. Duk irin yanda nake jin jikina da zuciyata hakan be hanani sakayawa fuskata murmushi ba musamman dana lura baba yana ta kallona da alama wani sauyi yake son gani daga gareni, ba kamar inna ba wacce take ta harkar gabanta a cikin motar.
An tare mu sosai domin ansan da zuwan mu ranar, nidai ko hutawa ban yiba 'yan uwana wa'inda muke sa'anni suka dinga jana gidan dangi bamu nan bamu can sabida su koda yaushe kallon wata madaukakiya suke yi min tun iyayena na raye.
Bazance ga abinda iyayena suka tattauna akai ba domin ban sani ba sai dai muna dawowa aka ce baba da mazan su alhaji sun wuce saini da inna kawai aka bari.
Naso na kwana a gidan kakannina na wajan uwa amma iya tayi mirsisi tace a gadonta zan kwana. Humm komai suke nufi da hakan oho.
Dangin Mamana na sona sosai amma sam basu samu sakewa dani sabida wata irin zuciya da dangin mahaifina keda ita duk kusan halin su d'aya tunda basu da 'yan uba duk iya ce ta haifesu dama ance abbana ne kawai bai d'auko halinta ba kamar yadda naji labari shi yasa gashi nan Allah ya dauke shi ya barta da masu kalar halinta.
Hanani bacci suka yi iya da inna wai da sunan bani shawara nan kuwa duk maganar d'aya ce kadda na basu kunya gara na zauna inda zan huta har suma su dangwali arziki. Kai kud'i basu yi ba wani lokacin. Babu ruwan su da wane irin kalar mijin zan zauna ba ko wane hali zan shiga ba sudai kawai na auri mai kud'i kodan su samu kud'i suma.
Can sama-sama na fara bacci naji iya na tamabayar inna.
''Waike me yasa kika ce asa bikinnan wata biyu?''
"Babu komai iya haka dai nace sabida kadda aga kamar neman kai muke yi da ita nifa ta fara bani tausayima.''
Mittsww.. ''Dalla bani wuri, to uban waye yace baya jin tausayin ta? ai jin tausayinta da muke yi ne shi yasa muke so ta auri wanda zata huta a gidan shi, kinga alhajin nan yace kadda akaita da komai sai suturunta komai zai yi mata tunda marainiya ce memakon ayi komai cikin sati biyu ko d'aya kika wani zabi har wata biyu dan iskanci.''
Cewar kakata iya, gashi dai ta manyanta amma hankalinta gaba d'aya yana kan dukiya kome zata yi da dukiya alhalin yanzu tana kan hanya? Eh mana tunda yanzu ko ita ta san da wuya ta nanata koda kwatan shekarunta na baya.
Wasu hawaye masu d'umi suka zubo min ina mamakin halin rayuwar yanzu, bansan lokacin da bacci yayi gaba dani ba.
**** *****
''Alhaji wai lafiya kuwa naga kanata shirye-shirye kamar mai shirin yin wata hidima?''
Ba tare daya kalleta ba yace. ''Ai hidima zanyi hajiya domin kuwa yaronki zanyiwa aure insha Allah.''
Idanunta ta fito dasu tare da dafe kirji, ''Alhaji wani yaron nawa?''
Ganin kalar kallon da yake mata ya sata wayancewa da cewa.
''Amma dai da mamaki Alhaji mai zaisa kai mishi aure yana cikin wannan halin? ai sai naga kamar rashin adalci ne, to ma wani mahaukacin nee ko nace kwadayayyen ne zai bawa mahaukaci 'yarshi?''
Wayarshi ya zara tare da ficewa yabar mata d'akin.
Hannuwa tasa saman kanta tare da budce baki zata saki ihu komai ta tuna kuma sai tai gaggawar rufe bakinta tare da nanata.
''Kan bantan uba..a'a wallahi da sake.''
*MAMAN KHADY*🙇🏻♀
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: Rumana 12
Kwance nake ina
barci bayan gama sallar magriba domin lazumi nakeyi bansan barciv ya kwasheniba.
Jinai ana shafamin k'afafu kamar mage tsabar laushin da nakeji.
Tun inaji sama-sama harna bude idanuna,Manyan idanuna na kuma zarowa ganin haidar kusa dani kuma shine me shafar k'afafuna.
Kauda kanshi yayi gabarin kallona amma bedena shafar kafar ba.