← Book details Rumana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 34

Sashe 2

Rumana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana sona sosai yana kuladani sannan duk abinda ya shige min duhu yana k'ok'arin haska minshi domin shima yana da ilmi sosai kayan miya yake sai dawa a nan cikin kasuwar bakori.

Ayanzu inada shekara goma sha takwas da wata hudu, ni d'in bawai fara bace amma kuma baza akirani da bak'a ba ina da fata mai kyau sosai, fuskata doguwa ina da dogon hanci da idanu masu kyau kuma madai-daita wanda mutane da yawa sukan yaba su, bani da irin tsawon nan amma kuma ban kasance gajera ba, kirar jikina ta fita sosai alhamdulillah da baiwar da Allah yayi min, na gama secondary d'ina tun watanni uku da suka wuce sai dai har yanzu ban daina zuwa makarantar islamiyya ba kasan cewar ilmi zurfi ne dashi musamman na addini da kullum baka gajiya da neman sa.

Inna da kanta take korar duk wani wanda ya nuna yana sona sabida tsabar kwad'ayin ta tuni ta daina zuwa dani maska sabida ana mata fad'an taki barina nayi aure. Ita kuma tace duk masu sona basu yi mata ba sabida tsabar kwad'ayi irin nata.

Hidimar inna da duk wahalar da take bani sam ba ta cika damuna ba domin idan nai wani tunanin sai naga ai itama tana kuladani kuma dan ta isa dani ne shi yasa amma shi baba yana nuna sam baya so domin kusan kullum sai ya tuna mata da illar cutar da maraya.

Kubiyoni......

*MAMAN KHADY*🙇🏻‍♀
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: 💞💞💞 *RUMANA* 💞💞💞

Na

*MAMAN KHADY*🙇🏻‍♀
(Mk)

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert and perfect writer's)

Page 3

Ina kwance tunanin da nake yi wanda yai nisa naji saukar dundu a bayana, a zabure na mike ina neman kallabina ina cewa.

''Inna banji kina kirana ba wallahi.''

''Dallah kyaleni ina aiken da nayi miki gidan su Dije?'' Idanuna harsun kawo ruwa sabida tsoro baki na rawa nace.

''Wallahi mantawa nayi inna lokacin da naje bata nan sai dai su Dijen.''

"Amma shine dan Iskanci kikai min shiru bakije kin sanar min ba? Toh saiki tashi muje ki wanke kayan can kafin lokacin islamiyyar ku tayi kuma kice ke islamiyya zakije.''

Binta nayi da kallo kai inna ko ta maidani sai kace injin wanki kullum sai nayi wanki ko basu taru ba, koda yake ai nakoyi tsafta wajanta tursasawar ai.

Sai wajan uku na gama wankin a gaggauce nayi wanka tare da alwalar la'asar sannan na shige d'akina wanda babu komai sai wani k'aramin gadon bono da jakar kayana a gefe, ko kayan kwalliya na azo agani bani dasu koda yake koban yi kwalliyar bama akan yaba kyauna, dan kallo d'aya zai wadatar da kai akan cewa lallai ni d'in mai tarbiyya ce domin haka Allah ya halicceni kalar tafiya ta ma kawai mai matukar d'aukar hankali ce.

"Kai Ruma wai da wucewa zaki yi?'' Cewar Dije.

"Yo da jiranki zanyi ke da kullum saikin makara kike jin dad'i, shi yasa zan wuce na barki kawai.''

"Toh Allah ya kamaki wai ya maganar taron da makaranta ta shirya ne? Nifa tunda naji ance wad'anda suka gama hadda za'a yaye naji raina baya so dan idan an yayemu sai a kaimu gidan wa?'' Dariya nayi har kumatuna suka lob'a sannan nace mata.

''Ni wallahi matsalata dake garaje, yo ina kuwa zasu kaimu, amman dai ina tunanin zamu fara tallafawa sauran malaman ne kota b'angaren kula da yara ne tunda kinga ana ta samun dalibai amma ba malamai da yawa sannan kinga duk girman makarantar nan mune manya tunda mune na farkon wad'anda zasu yaye.''

"Eh haka ne na gane.''

Cewar Dije lokacin da muka shiga cikin makarantar. Kusan duk karin bayani akai mana akan abubuwan da zamu gabatar ranar asabar domin ranar ne za'a yi gagarumin taron da aka jima ana shiryawa.

"Ke Rumana kinsan cewa kece shugaban d'aliban makarantar nan, sannan karatunki yana fita ta yanda ake so sabida haka ki shirya duk wasu addu'a da za'a yi domin kece wacce zaki bud'e taro da addu'ar. Sannan zaki yi karatu kuma zaki mana fashin baki akan wasu hadisai wanda za'a aiko miki dasu gobe ko kuma yau ki wuce dasu gida dan ki sake dubawa."

Malam tijjani yai maganar idanunshi kur akaina wanda hakan ne ya tilasta min sunkuyar da kaina kasa.

Agajiye muka koma gida ga jikina yai wani irin mugun sanyi musamman da naji ana fad'in irin manyan mutanen da aka gayyata kuma wai nice mai bud'e taro na san ma kila jikina rawa zai tayi sabida farga ba.

Innan na samu da maganar duk yadda muka yi da malaman tayi farin ciki sosai a wannan lokacin sannan ta k'arasa maganar da fad'in.

''Allah yasa kafin a tashi kisami miji a wajan na nunawa sa'a, Kinga anjima da daddare aka ce aje a anso d'in kin ki, toh amma ki bari sai da safe ki amso sannan ki yanko yadin hijabin da zaki saka, takalmin kuma gashi can Allah ya bada sa'a, amma sai kin daure idan ba haka ba kunya da idanun mutane baza su barki kiyi abin kirki ba wallahi.''

Oh yau wace rana inna namin magana cikin sanyin rai bada tsawa ba....

*****

Bige-bigen da ake yi a cikin d'akin sai kai tunanin wasu mutane ne masu yawa cikinsa amma ina shi kadai ne cikin d'akin amma tuni ya can zama d'akin fasali sabida tashin ciwon shi. Mudi ne ya shigo da sauri yana nanata kalmar.

''Subhanillahi Haidar wannan lalura taka Allah yai mana maganinta.'' Alhajin ya fita nemowa a waya ya sanar dashi halin da ake ciki ya kira likita wanda dole sai da aka mishi allura sannan suka samu sa'ida.

Sai yamma lik'is sannan alhajin ya shigo garin kasan cewar dama yana garin abuja yaje gano wani kamfaninshi. Kai tsaye d'akin Haidar d'in ya shiga nan ya tarar dashi kwance yana bacci, yayin da Mudi ke zaune a gefenshi yana gyangyad'i.

Ganin kamar Haidar d'in ya rame a yau ya kuma tashin hankalinshi tare da hanashi nutsuwa ya fara tambayar Mudi.

"Kai Mudi.!'' Cewar alhajin yana taba kafad'ar Mudin.

"Na'am alhaji barka da sauka.''

"Yauwa wai cewa nayi ya naga Haidar ya fad'a ko akwai wata damuwa ne?''

"Babu damuwar komai alhaji amma jiya ciwon ya bigeshi sosai yauma hakan, dan kaga nan wannan kululun da yai min wallahi had'ani da bango yayi, ni sai naga kamar ma ciwon neman yin gaba yake yi.''

"To Allah ya kyauta daman ranar asabar zanje bakori insha Allah kome muka yi da yayana zan sanar maka ya gayyaceni wani taron yaye dalibai da zamu yi shawarar yanda za'ayi tunda dama nine naki yadda ayi mishi na gargajiya.''

"To shikenan alhaji hakan shine dai-dai gaskiya domin yaron nan yana cikin wani hali wallahi gashi yana da karfin sha'awa sosai, in ta taso mishi har hawaye nake yi sabida nasan babu dad'i gashi besan yanda zai yi ba.''

******

Ranar asabar kamar yadda aketa jira tare da tsara yanda taron zai tafi daidai tazo, sun shirya komai kuma alhamdulillah komai yayi yanda ake so. Gaba d'ayanmu wad'anda za'a yaye mu sha takwas ne maza takwas sai matan mu goma, muna cikin ankon wata dalleliyar shadda me ruwan sararin samaniya tare da farin hijab da farin takalmi.

Mazan ma shaddar irin tamu ce sai farin takalmi da farar hula, Hakika munyi kyau munkuma bada kala tun a wannan lokaci manyan mutane suka fara yabama tsarin da muka yi.

Munsami halartar manyan mutane wa indama bamu zata ba sannan iyayen mu da dangin mu kowa burinshi ace ga nashi shima ya samu wannan d'aukakar.

''Ki daure Rumana dan Allah kadda ki badamu a wajan nan, kiduba kiga yanda manyan mutane suka zo gurin nan kadda ki kalli fuskar kowa kedai kawai kiyi abinda ke gabanki bana san wannan rawar da jikinki keyi ki dake sosai kilama daganan ki wuce saudiyya insha Allahu.''

Malam Aminu kenan shine shugaban makarantar yau haddashi wajan lallashina. Yana gaba ina bayan shi duk inda ya cire kafarshi nan nake maida tawa sabida kadda na d'ago kainama na kasa aiwatar da abin arziki.

Wata irin kabbara wajan ya d'auka lokacin da na dai-daita tsayuwata akan mumbarin da aka tanada. Tsigar jikina duk sai da ta mike sabida wannan sauti na girman Allah daya shiga kunnuwana ya ratsa jikina.

Muryata itace ta katsema kowa hanzari tare da sa kowa nutsuwar dole lokacin da sautinta ya karad'e ko'ina dake wajan. Bayan doguwar addu'a tare da fatan gama taro lafiya saina gabatar da kaina tare da yima bakin mu barka da zuwa. Wata kabbarar aka kuma d'auka lokacin da na koma gefe na zauna inda aka tanadar mana.

Nan manyan malamai sukaita fitowa suna tofa albarkacin bakinsu tare da jin dad'in yanda addini yake ta k'ara samun d'aukaka tare da jinjinama malaman dake jajircewa dan ganin an d'aukaka kalmar Allah. Sannan muka fito domin gabatar da karatuttuka kadan daga baiwar da Allah yai mana.

Nice ta karshe kuma nice wadda aka gabatar amatsayin shugabar d'alibai mai tsananin kula da dukkan abinda ya shafi addini, Haka zalika karatuna yafi na kowa fita wannan kuka baiwa ce daga Allah.

Lokacin da na gama karatuna na fara fashin baki akan hadisan dake magana akan hakkin 'ya'ya akan iyayensu tare da hakkin iyaye akan 'ya'yansu sai naji wani kuka yazo min a raina ina cewa, inama iyayena na raye yau suga d'iyarsu suyi alfahari da baiwar da Allah yai musu.

Lokacin da na d'ago idona saina sauke su akan inna wacce take ta share hawaye wanda na rasa kona menene na d'an uwanta ne data rasa ko kuwa dai itama tana yine kamar yadda na lura mutane da yawa awajan suna share kwalla.

Fad'in irin kyaututukan dana samu b'ata lokaci ne sai dai kyautar data gigitani itace lokacin da naji wani kamilallan mutun yana cewa.

''Na bawa Rumana kujerar makka tare da kud'i naira dubu d'ari uku Allah yasawa rayuwarki albarka.''

Nanfa waje ya kuma bud'ewa da kabbara yayin da kaina ke duk'e awajan ina hawaye, wanda bazan ce ga kukan me nike yiba. Mai gabatarwa ne ya tashi yayi godiya sosai tare da yiwa wanda ya ba da kyautar da tafi ta kowa wato ALHAJI YUSUF.....

*MAMAN KHADY*🙇🏻‍♀
[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: 💞💞💞 *RUMANA* 💞💞💞

Na

*MAMAN KHADY*🙇🏻‍♀
(Mk)

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert and perfect writer's)
Chapter 2 · 0% Book details