← Book details Rumana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 34

Sashe 1

Rumana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ruma[4/2, 11:15 AM] Re@l💍 K@usy🌹: 💞💞💞 *RUMANA* 💞💞💞

Na

*MAMAN KHADY*🙇🏻‍♀
(Mk)

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert and perfect writer's)

Page 2

Bayan kwanaki biyu da misalin karfe biyar na yammacin ranar alhamis Alhaji Aminu ya dira a kofar gidan abokin nashi zuciyarshi cike da d'okin kawo mishi wani albishir da yayi. Wayarshi yasaka ya kira alhaji Yusuf d'in tare da gaya mishi cewar gashinan a k'ofar gida yana jiransa.

Wata farar jallabiya ya saka sannan ya fito hannunshi rike da k'aramar wayarshi wacce ita ce yafi amfani da ita akan sauran wayoyinshi.

"Alhaji kacika matsala wallahi kashiga tunda kasan ina ciki shine sai ka wani toge a nan kace min gakanan waje, toh na ganka ai zo mu shiga daga ciki.'' Tare suka jera harda wani mutum wanda tare suka zo da alhaji Aminun.

"Yauwa dama zanda zai kula da Haidar ne kamin wani lokaci aka samu kaga namijine sannan kasan dole d'awainiyar Haidar sai dai namiji maiji da karfi, gashi nan sunansa Mudi d'an maigadin gidana ne ya amince zai kula da Haidar tsakanin shi da Allah amman fa na wani d'an lokaci domin yana zuwa nijar wajan mahaifiyarshi.'' Numfasawa Alhaji Yusuf d'in yayi kafin yace.

"Toh alhamdulillah nagode sosai Allah yabar zumunci tsakanin mu, amman kayi mishi bayanin halin da haidar d'in yake ciki ko?''

"Eh nai mishi ya kuma fahimta sai dai muyi mishi fatan Allah ya bashi juriya.''

"Eh hakan yayi toh muje in nuna masa d'akin nashi, aikin naka zai kasance bashi abinci ne da wanka sai gyara mishi jiki idan ya b'ata. Kuma zakai aikin ne idan bana nan amma idan ina nan to zan amsheka saika huta kaima, amman dan Allah karike min amana idan ka cutar da Haidar lallai Allah yana ganinka kuma da sannu zai saka mishi, ban yadda cikin matana wata ta kawo masa abu tace kabashi ba kaji ko?''

"Naji alhaji kuma insha Allahu zan kiyaye.'' Cewar Mudi.

"Toh alhamdulillahi duk karshen wata zan baka dubu d'ari ammafa idan naga yanda kake yin aikin naka idan yayi min.''

Wata sufa Mudi yayi a gaban alhajin tsabar jin dad'i da farin ciki, godiya yake yi kamar bakin shi zai yage. Tare suka shiga d'akin Haidar d'in yana rakabe can wajan labulen toilet ya takure kanshi kamar wani maraya, kanshi a k'asa yana ta faman murzar yatsunshi kamar wanda aka yiwa dole.

"Ah Abban Haidar wai dama yana nutsuwa irin haka?'' Cewar alhaji Aminu.

"Eh yana yi wani lokacin ko kuma kaji yana ta sambatu babu kai balle k'afafu, wani lokacin yaita kuka wani lokacin kuma yaita bige-bige amma idan yai wannan nutsuwar sai kaga inama ace haka lalurar take wallahi wani lokacin sai naga kamar ya warke ni bige-bigen da yake yine kawai bana so domin wani lokacin kana gani duk sai ya jiwa jikinshi ciwo.''

Mudi dake tsaye bayan su yana jin duk abinda suke cewa tuni ya shagala da kallon kayataccen d'akin wai wannan ne dakin mahaukaci lallai dukiya na inda take, amma shi aganin shi wannan lalura ai maganin gargajiya ya dace ai mishi bawai na asibiti ba. Nan dai sukabar Mudi suka fice.

****

BAYAN sati daya Mudi yana matukar k'ok'ari wajan ganin ya taimakawa Haidar domin har addu'a yake tofa mishi yana bashi yana sha ba tare da sanin alhajin ba, kuma sosai yake ganin cigaba amma wani idan abun ya tashi sai kaga kamar ya k'arasa haukacewa gaba d'aya.

Cikin d'akin Haidar babu wani abu me sunan makami domin hatta gado babu shi cikin d'akin sai dai k'atuwar katifa kayan sawarshi kuwa like suke a bango.

Sosai Mudi yake k'ok'ari wajan kula dashi, da kanshi yak emai wanka kuma ya gyarashi kai shi har gyaran fuska yake mishi da hammata da gabanshi idan yana bacci shi yasa nan da nan Haidar d'in ya kuma kyau sosai duk ya canza.

Satin alhaji Yusuf uku da tafiyar da yayi zuwa k'asar China, sosai yai farin ciki da yaga yanda yaron shi ya koma, sai dai aranar ya tadda Mudi da rauni agoshinsa wai wajan yima Haidar d'in wanka ne ya had'ashi da bango dan yaki bashi sabulu yaci.

Naira dubu d'ari cif ya bawa mudi tare da tsara ba na kayan sawa da sauran bukatu, ai kuwa sai da yaji kamar zai mishi sujjada tsabar godiya.

Da dare....

Mudi na kwance gefen Haidar bayan alhaji yai musu sallama ya tafi wajan iyalin shi jiyai Haidar d'in yana lalubarshi tare da sakin nunfarfashi kamar dai wanda yake cikin matsananciyar sha'awa.

Da mamaki Mudi ya kunna hasken d'akin ya kura mishi ido yana kallon juye-juyen da yake yi ga abun nashi ya wani cika gaban wandon shi. Wasu irin hawaye ne suka shiga zubowa Mudi tsabar tausayin da yaji yana neman rufe shi.

''Allah ya kawo maka sauki Haidar, Allah ya kawo maka iyakar wannan lalura da kake ciki, duk wanda yai maka wannan abun Allah ya maida mishi da aniyar shi inda lafiyarka lau ai da yanzu kana nan da iyalinka amma yanzu babu wacce zata yadda ta rabeka wallahi, Allah yabi maka hakkinka.'' Addu'a yai ta tofa mishi har saida yaji saukar numfashinsa alamar yai barci.

Da safe...

''Alhaji an tashi lafiya ya gajiyar tafiya?''

"Lafiya lau Mudi ya mai jikin ya kuka kwana?''

''Alhamdulillah alhaji, amma jiya dai gaskiya ya kwana babu dad'i domin inaganin sha'awarshi bata samu nak'asa ba dan ni dai naga jiya ta tashi kuma da kyar ya samu bacci.'' D'an murmurshi alhajin yayi yace.

''Eh hakane Mudi tana tashi wani lokacin to kaga babu yanda zanyi dashi musamman a halin da yake ciki yanzu babu wanda zai yadda ya bada d'iyar shi ta auri mai irin larurar Haidar, amma kwannan zanje gida can bakori insha Allah zan kuma cigitawa idan Allah yasa an samu saina aura mishi.''

"To to Allah ya zab'a masa ta gari kuma mafi alkhairi, shi kuma Allah ya bashi lafiya.''

*****

Asalin su Rumana, malam Habu shine mahaifin Rumana d'an garin maska ne ta jahar katsina kagabada, a nan aka haife shi kuma a nan ya taso yana sana'ar sai da itace matar shi subanta Habiba itace kuma mahaifiyar Rumana itama 'yar nan cikin garin ce tare take zaune da surukanta kasancewar sam malam habu bashi da ikon siyen gida balle ya saka matarshi a ciki.

Iyayen malam habu sam basa kaunar Habiba ba kuma dan komai ba sai dan mahaifinta ya kasance babban malami wai kadda su saki jiki ashanye musu yaro duk da cewa matsalar tafi yawa daga wajan ita mahaifiyar malam habu d'in. Daga baya ne sai ya dawo cikin garin funtuwa ya fara sai da kayan gwanjo kuma alhamdulillah sana'ar ya farata cikin nasara.

A lokacin da ya maido da Habiba funtuwa sai da akai d'an k'aramin yaki da mahaifiyarshi musamman daya kasance har lokacin ita Habiban bata haihu ba, tunda har an fara yi mata kiran ita juya ce bata haihuwa.

Malam habu irin mutanan nan ne masu tsananin hakuri da kauda kai haka itama matarshi Habiha sam basu da hayaniya. Allah ya basu haihuwar Rumana kusan lokacin da basu zata ba domin sai da cikin yai wata hud'u cikin na biyar sannan suka farga akai ta taya su murna sosai fiye da tunani kowa. Cikin iko na Allah suka raine shi Allah ya basu Rumana mahaifinta yasa mata sunan sabida yana kaunar sunan sosai Ummu Rumana sai dai tuni Rumana ya bita.

Tataso cikin kula sosai ta uwa data uba sannan kakanni domin idan sukaje maska kowa nan nan yakeyi da ita, Basu kuma samun haihuwaba kuma hakan be zama damuwa ba a gare su.

Akwai tarin ilmi mai yawa awajan Rumana kasan cewar makarantar kud'i ya sakata islamiyya da boko sabida ta samu ingantaccen ilmi, sannan yana ganin basu da yara da yawa balle dawainiyar su tai mishi yawa.

Sannan kullum dare mahaifiyarta takan d'ora mata karatun addini amatsayinta na d'iyar babban malami tare da addu'o'i musamman wad'anda suka danganci na neman tsari tare da karya lagon makiya.

Shekararta goma dai-dai, wani mummunan al'amarin ya faru domin wuta ce takama d'akin da iyayenta suke kwance har sai da ta cinye su tas! dalilin maganin sauro da aka kunna. Mutane suka cika gurin masu temako amma babu wani abu da yayi saura balle ataimaka musu kasancewar Rumana na tsakar gida. itama kuka take yi irin kukan nan mai tsananin azaba da tashin hankali.

Kowa yaji wannan mutuwa musamman wad'anda suka mu'amalanci malam Habu da matarshi Habiba, sannan kuma iyaye wad'anda suka kusa zaucewa sabida jin mutuwar.

Rikon Rumana sai ya koma hannun kakaninta na wajan uba dake nan madai, sun kula da ita da dad'i babu dad'i ana tare har Allah yasa tayi shekara uku a nan gurin su, daga baya sai yayar babanta wacce ke aure a bakori ta amshi rikonta sabida ita Allah bai tab'a bata haihuwa ba amma mijinta yana da yara har guda biyar duk mata kuma sunyi aure, ya tab'a auran wata matar sai dai daga baya ta rasu,.

Gwaggo Suwaiba irin matan nan ne masu tsananin ganin kyashin tsiya sam bata iya gani ta kauda kai ga uwa uba zalinci babu ruwanta amaimakon tunda ita bata haihu ba tasamu ta kula dani amatsayi na na d'iyar kaninta kuma uwa d'aya uba d'aya amma ina kullum wulak'ancin yau daban na gobe daban kai yanda ma malam d'in yake jin tausayina kuma yake kula dani saika d'aukama shine d'an uwan nawa bawai ita ba.

Inda Allah ya taimakeni sam bata hanani neman ilmi na ba kuma dai-dai bakin gwargwado tana min sutura sai dai akwaita da masifa da jaraba dan sam bata da hakuri.

Tun ina da shekara goma sha biyar nai saukar alkur'ani daga baya ne na fara hadda wadda alhamdulillah ina da sani sosai musamman ta b'angaren addini har larabci na iya sannan har yanzu duk karatun da Ummana tayi min yana nan akaina kuma kullum ina musu addu'a suma.

Malam sule shine mijin gwaggo Suwaiba amma ina ce mata inna sabida duk haka 'ya'yan malam d'in suke kiranta, sannan shi kuma malam d'in na kan kirashi da baba kamar yadda naji ana kiran shi.
Chapter 1 · 0% Book details