← Book details Raino Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 30

Sashe 25

Raino Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Jini ne kawai ke fita ta ƙasanta wanda yake gudu sosai akan carpet ɗin bedroom ɗinta.
Najwa na fita daga ɗakin beby ta daka uban tsalle tare dayin wata shewa ita ɗaya ta fara rawa a tsakiyar babban parlour wanda yake ma rarraba da flat fin kowannensu,hannu tasa ta riƙe waist ɗinta sannan and she stand talking,"wannan shegen cikin da kowa yake ƙaunarsa nasan duk ranar da yazu duniya tuni lokaci na yayi,yanzu nayi maganinta idan wancan uban rawarkan yazu saita gaya masa abinda tasha har cikin ya zube nasan daga nan zai sallameta tunda ta nuna mata sonsa da zuri'a"
Dariya ta ƙarayi tare da juyawa tana faɗin"bani da damuwa ko guda cikin raina..saurin ja baya tayi tare da gwalo ido sabida ganin A.J da tayi ya fito daga ɗakinsa,murmushi ya sakar mata tare da faɗin"sannu da rawa"ɗan murmushi tayi kaɗan sabida gaba ɗaya a tsurace take kallon idonsa tayi wanda ya gama komawa red ga yadda jijiyoyin kansa suka fito sabida azaba.
Wajansa ta ƙarasa tare sunkuyawa tana kallon cikin idonsa tace"hope lafiya kake naga mood naka ya sauya"gaba yayi tare da faɗin"A dey fine,kawai na kaɗe wata mata ne abun tausayi"yana faɗin hakan yayi gaba tare da nufar ɗakin beby gaba ɗaya baiji motsin taba.
tura ƙofar ɗakin yayi a hankali yana shiga ya kalli bed yaga babu kowa,hanyar toilet yabi ko wanka take tsayawa yayi cak sabida karo da yayi da abinda ya gigita shi abu mafi muni cikin abubuwan da suka faro dashi,rana mafi baƙin ciki da kuma takaici a cikin ranakun rayuwarsa.
Idonsa ne ya fara fitar da kwalla mai zafi kana ganin Ahmad kasan yana cikin mawuyacin hali,ko mus'ab zai wahala yace A.J ya taɓa kuka a gabansa amma yau Ahmad da kansa ke zubar da hawaye tabbas wannan abun ba ƙaramin baƙanta masa zuciya yayi ba.
Da sauri ya miƙa hannu ya saɓi beby wacce ke kwamce cikin jini,gudu² sauri² ya fara haɗawa,daret wajan motarsa ya nufa yana zuwa ya buɗe motar sannan ya shimfiɗe beby wacce take kanwar matacciya.
A guje yaja motar zuwa babban asibitiɓ dake garin abuja wanda ya kasance mallakin Dr Ahmad Tijjani Asasa ne.
Akan idon najwa A.J ya fita da beby,wani mugun murmushi ta saki tare da faÉ—in"yaro baisan wuta ba saiya taka,shegiya Æ´ar tsintuwa Allah yasa daga nan ki mutu kowa ya huta".
Cikin makirci ta fita a guje zuwa flat É—in hajia domin ta shaida mata abinda yake faruwa,gaba mata ganin gabanta sabida farin cikin da take ciki yau komai zaizo mata da sauki.
Wayyo rashin yasa najwa ta daki wani ƙarfe nan take ta faɗin ƙasa,yayinda cikinta ya sauka akan wani ƙaton dutse har saida jini ya fita ta hancinta nan take ta suma a wajan babu numfashi.
Wajan 30min tana kwance saman dutsen babu wanda yazu,a hankali hancin motarsa take shigowa cikin gidan,tun daga nesa yake hango mutum a kwance fuskar mus'ab É—auke da mamakin wanda yazu waje ya kwanta cikin sauri yayi parking motar.
Tattara riga yayi yasa gudu ganin najwa ce kwance saman wani ƙaton dutse wanda yake ta tunanin ɗaukeshi Allah bai bashi iko ba.
Yana zuwa yasa hannun ya janyeta akan dutsen nan idonsa ya sauka akan hancinta wanda yake fitar da jini,da sauri yasa hannu cikin wandonsa ya É—auka wayar yayi darling number A.J har sau biyu amma bai É—auka ba,nan ya kira hajia ya shaida mata dukkan abinda ya gani,umarni ta bashi yasa najwa a mota gata nan fituwa.
5min hajia ta fitu cikin sauri tare da salati a bakinta tana zuwa ta fada mota nan mus'ab yaja motar da gudu yayi waje kasan cewar get a buÉ—e yake.
Jikin sane ya fara rawa lokacin daya gama tabbatar da urbon ɗinsa ya zube,zabewa yayi a ƙasa tare da kifa kansa a tsakin laps ɗinsa ya fashe da kuka,ta cuce shi ta cuci rawarya tayi masa abu mafi muni da kuma baƙin ciki baisan matakin dazai ɗauka akanta ba.
Turo ƙofar ɗakin da akai shine ya sashi saurin goge hawayen face ɗinsa sannan ya ɗago da kansa a hankali nan yayi tuzali Hajia tayi jingine a jikin bangon ɗakin,bayanta kuma Mus'ab ne tsaye idonsa ya sauya yayi red.
A kasalance ya tashi yayi wajan hajia yana zuwa ya faÉ—a jikinta yana sauke ajiyar zuciya,kansa ya É—ago nan suka haÉ—a ido da Mus'ab É—an juya bayan hajia yayi inda ta koma baya suna parcing juna da mus'ab shi kuma ya koma gaba inda ya bawa mus'ab baya,sai lokacin ya samu damar fitar da wasu hawaye masu zafi,saukar hawayen taji a shoulder É—inta tayi saurin runtsa idonta ta najin wani ciwo a ranta hannu tasa ta É—an bubbuga bayansa tare da faÉ—in.
"innallaha ma'ar sabirin"ka ɗauki wannan kasama zuciyarka komai na Allah yana da iyaka daman Allah ya riga daya rubuta hakan wannan cikin bazai taɓa zuwa duniya ba,idan ka yarda da Allah kuma ka yarda ƙaddarar inason kayi hakuri kada ka ɗauki kowanne hukunci akanta itama taji da abinda yake damunta,yara kuma zaka samesu masu Albarka kada kayi gaggawa.
Ajjiyar zuciya ya sauke tare da zare jikinsa yana É—an murmushi.
"soo bad bro na Allah ya kawo masu albarka"cewar mus'ab.
Hajia ce ta kalli A.J tace"Ahmad yanzu wannan matar daka kaɗe naga taji sauƙi yaya za'ai da ita?".
Lumshe ido yayi ya najin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri almost 5min sannan ya waro idonsa akan Hajia yace"zata bimu gida,hajia bata da kowa fa"ayya Allah sarki zanso na ganta.
Wai me kukazu yi a hospital haka?numfashi hajia taja kafin tace"munkawo najwa ne,bayan fitarku ta samu tsautsayi,babban tashin hankalin ance mahaifarta ta fashe ba zata taɓa samun haihuwa ba.."sai kuma ta haɗe ɗai tace"Ahamd ashe ni hauka na nake ko,wato rayinyar haryau bata da ƴanci a wajanka,dr ya tabbatarmin da haryau najwa budurwace wannan wanne irin abu ne,babu shakka hakkinta shine ya shafi shibewar jikin beby,ita kuma beby bata da hakkim najwa shiyasa Allah ya saka mata da sakayya mafi muni domin rashin haihuwa babban tashin hankali ne,kuma ni ban aura makasu domin wata rana na raba auran kwara ka gyara domin itama matarka ce"takai ƙarshan maganar rai ɓace.

"am sorry hajia"shine kawai abinda ya iya faɗa,kafaɗa ta ɗaga alamar ita babu ruwanta duk da itama rashin cikin beby yana matuƙar damunta"muje ka kaini wajan waccen baiwar Allah inajin tausayinta"ok kawai ya faɗa sannan ya juya zuwa wajan beby wscce take kwace akan bed ɗin marasa lafiya tayi haske chocolate skin ɗinta ya ƙara fituwa,yana zuwa ya manna mata kiss a lips ɗinta sannan ya shafa kanta cikin sassarfa yabar ɗakin.
Yana fituwa ya shiga wani É—aki wanda yake parcing na beby,baya suka rufa masa zuwa É—akin.
Tura ƙofar ɗakin yayi a tsaye ya ganta sosai kunnansa yake ɗauko masa sautin kukanta,gaba ɗaya suka tsaya suna kallonta kasan cewar ta juya masu baya basa iya ganin fuskarta.
A hankali Ahmad ya motsa bakinsa tare faÉ—in"Assalamu Alaiki" a É—an razane ta juyo domin ba taji shiguwar mutum ba sai sallama taji.
A razane hajia ta shiga nuna matar da hannu itama kallonta tayi,kafin hajia ta fasa ƙara tare da faɗin.
"Khaleesat"

Pls ba sai kunyi Comments na yafe,domin ba'aimin wanda zai wanken zuciya kamar yadda nake maku kawai zance maku ngd maku sosai bisa abinda kukemin.

Wattpad ina gdy sosai aci gaba da vote and Comments pls

~Sarauta👑~

*🤱🏻RAINO ne SILA🤱🏻*
_ADOPTION IS THE BEHIND_

*NIMCY LUV*
_S@r@ut@👑_

Follow on istagram
Nimcyluv
Follow on wattpad
Nimcyluv

*STOP INTERUPT..🤚🏻*

*73-74*
Chapter 25 · 0% Book details