← Book details Raino Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 30

Sashe 11

Raino Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba ɗayansu suka ɗago kai suna kallon bakin ƙofa domin ganin wacce take sallama,yayinda A.j ya lumshe idonsa tare da gyara kwanciyarsa bisa cinyar Hajia,wata matashiyar yarinya suka gani wacce a zahiri face ɗintane na yara but a jikin kam zaka iya bata 20years,hannunta ɗauke da wata red trolly ta mata fiya,idonta sai sharning yake sabida fari tamkar zata zubar da kwalla sabida yadda idonta yake da matuƙar haske da girma har wata colour ne cikin kwayar idonta,sosai shape ɗin jikinta ya bai yana cute pink lips ɗinta mai kyauri ya fito sosai sabida yadda jikinta yake dark black, duk cikin 2min Mus'ab ya gana ƙare mata kallo yasu ya gane ko wace but baya iya tunawa hakan yasa yayi ƙasa da kansa yaci gaba da danna lapton,dariya Hajia tayi sannan tace"Oyoyo my beby finally an gana makaranta"ɗan kwaɓe fuska tayi ta kasa cewa komai sai Hajia da take kallo sai kuma ta kalli cinyarta,jinjina kai Hajia tayi kafin tace"bebyn come to me"ɗan bubbuga ƙafarta tayi lokacin da take turo bakinta gaba,da gudu tazu ta faɗa jikin Hajia tayi masauki a cinyarta"auchii"yace jin anbiki kansa."bebyn enmata yaya school"shuru tayi bata ce komai ba wajan 2min tace"Hajia"murmushi Hajia tayi sannan tasa hannu ta zare beby hijab ɗin jikinta nan take gammun da tayiwa gashinta ya warware ya zuba har bayanta haɗe da rabin face ɗinta sannan tace."wat wrong?"hannu tasa tayi mata nuni da A.j wanda gaba ɗaya surutunsu ya dame shi sam bai fiya son magana ba sai yana tare da Hajia amma gashi wannan staranger zata addabe shi,kallon A.j Hajia tayi sannan tace."Meyayi maki?"turo baki gaba tayi sannan tace"Hajia ya tashi daga cinyata"gaba ɗaya Najwa da Mus'ab ne suka ɗago suna kallonta ya salam shine kawai abinda Mus'ab yace lokacin daya gama tuna Anusha,Hajia ce ta kalli A.j wanda yake kwance a cinyarta sannan tasa hannu ta shafi gashin kansa kafin tace."dr tashi mai waje ta dawo"juyowa yayi fes idonsa ya sauka kan Najwa wace take zaune ta lumshe ido sai lokacin ya samu damar ƙare mata kallo,Sosai take fara harta kosa ɗarasa a fari,lips ɗinta black ne maimakon pink hakan ya kara fito da face ɗinta,ganin zata buɗe ido yayi saurin lumshe nasa idon,Anusha kam da baƙin ciki ya kamata ganin A.j yaƙi sauka daka kan cinyar Hajia yasa ta fashe da kuka tare da kai hannunta cikin sumar kansa tana turasa,hakan yasa yayi saurin tashi zaune zuba mata ido yayi kafin yace"black girl"turo baki tayi haɗe da ƙara sautin kukanta kafin ta zabga masa harara tace"eh naji haka Allah yasu ya ganni"ta faɗa tana turo masa baki gaba,zaro ido yayi waje sannan ya girgiza kansa ya miƙe tsaye yabar wajan,Mus'ab ne yasa dariya ya miƙe tsaye shima sannan ya kalli Anusha yace."sorry beby gal,amma da kuɗina da hankali nima ban iya auren black gal wallahi"shuru tayi ta zuba masa ido kafin tayi tsalle tasha gabansa tare da riƙe waist ɗinta rolling sexcy eyes ɗinta tayi tare dayin fari tace."ohh hello ko a dream bana fatan auren farin mutum,than da kake cewa meza kai da baƙar mace insha Allah baƙar macen itane matarka,than waye ya fara gabatar da kiran sallah,ba bilal bane kuma inajin shima baƙine ko?"tana faɗin hakan ta juya tayi shigewarta ɗakin Hajia,baki Mus'ab ya saki galala yana jin rashin kunyar da take zuba masa,babu shakka data tsaya sai yayi mata mugun duka wani irin baƙin ciki ne ya kamashi haka kawai yaji yana son shiga sabgarta kodan yaji ubanta da wannan tunanin yayi cikin ɗakinsa.
A.j na shiga ɗakinsa ya fara cire kayansa saida yayi naked sannan yayi hanyar bathroom,yana shiga ya sakarwa kansa shower sosai ruwan yake dukan kansa zuwa naked body ɗinsa numfashi ya shiga saukewa a hankali,sosai ya kejin damuwa na sauka zuwa zuciyarsa wanda ya rasa dalilin hakan koda Hajia tayi mai zancen Aure bai shiga wannan damuwar ba,amma yanzu duk yana jinsa a bad mood he don't know why,wajan 30min ya ɗauka hannu yasa ya kashe shower wani light blue ɗin towel ya ɗaura a waist ɗinsa ya fito daga toilet,a gaban mirrow ya tsaya ya fara tsane ruwan dake sauka akansa,sannan yasa cump ya tashe gashin sosai ya shafa wani man gashi mai kyau ta kuma ƙamshi,cikin few minutes kansa ya shiga sheƙi da kuma gyalli,cikin sauri yaci gaba da shiryawa saida ya gama komai sannan ya ɗauko body spray ya shiga fesawa jikinsa yana gamawa yayi wajan wadrop ɗinsa nan ya ciro wata shadda dark blue mai ƙanan zane cikin sauri ya saka kayan sannan ya ɗauko babbar riga ta kayan ya saka tare da wata black cap mai zanen blue a jikin sai agowan apple mai black colour with black shoe company adidas,tabbas Ahmad Tijjani Asasa Allah yayi masa baiwar kyau da kuma kwarjini da cikar zati,sam baya da girman kai saida bashi da magana saidai murmushi haka bai fiya zama da mutumin da yake da surutu ba,yana da taimako sosai akan mai buƙatar taimakon,wayarsa ya ɗauka da kuma key ɗin motarsa cikin takonsa na ƙasaita ta kuma taƙama ya fito daga ɗakin nasa zuwa parlour'n gidan kansa a ƙasa yayi hanyar waje yana zuwa compound na gidan yayiwa motarsa key tunkafin ya ƙarasu wajan motar ta buɗe yana zuwa ya faɗa cikin motar saida ya saita waƙar jerusalema ya ɗansa volume kaɗan sannan yayiwa motar key ya fara tafiya cikin nutsawa yake joya kan motar,tun kafin ya ƙarasu getman ya buɗeman dan haka yana zuwa yayi waje kai tsaye Sosai yake sharara gudu akan titi dake bai iya tafiya a hankali ba indai shike drivering motar,few minutes ya isa babban asibitin dake garin Abuja yana zuwa yayi parking a compound na asibitin,tun kafin ya fito wasu ma'aikatan jinya sukayo kansa cikin sauri,shima kallonsu yayi ba tare daya iya ce masu komai ba,ɗan rusunawa sukai sukace."Dr daman tun ɗazu ake jiran zuwanka,wata mace mai cike ce tun jiya bata haihu ba,yanzu ana tunanin aiki zaai mata she is cirtical condition"cikin sauri ya fitu daga motar ya nufi office ɗinsa su kuma suna take masa baya a bakin office ɗin suka tsaya suna jiransa,yana shiga ya cire babbar rigarsa tare da a gogwan dke hannunsa wata safa ya saka a duka hannunsa,cikin saurin ya fito daga office ɗin yana zuwa suka miƙa masa wata green ɗin riga amsa yayi sannan yayi gaba zuwa Emagency room ɗin da matar ke ciki,turus ya tsaya dan tunaninsa zaiga babbar mace sai yaga wata matashiyar mata wacce take da ƙarancin shekaru,da hannu yayiwa sauran ma'aikatan nuni suka kunna na'ora da oxcygen cikin sauri ya shiga aikinsa da kware da kuma zallar tunani irin nasu na manyan likitoci,tunda yazu yasan cewa abinda yake cikin matar ya rasu,cikin few minutes yayi mata aiki ya ciro abinda yake cikin daman tayaya zata iya haihuwa banda abinsu jaririn da bashi da rai tayaya zaiyi yunƙurin fituwa,kabbara sukai ƴan wajen tare da karɓar jaririn,wata ma'aikaciyar jinyace tace."Dr baya motsi jariri"kallonta yayi sannan ya juya ya kalli matar da akaiwa aikin wacce taɗan buɗe ido yace."am sorry to say bebynki babu shi"wani murmushi tayi duk da halin ciwo tace."Allahamdullilah nayi matuƙar farin ciki da kuma jin daɗi mutuwar wannan shegen yaron"a ra zane suka ɗago kai suka kalleta.
*********** *********
Sosai mutane suka cika matsallacin dake nesa da gidansu A.j,a wannan lokacin A.j baya gida yana Asibiti duba marasa lafiya,ta kasance ranar lahadi 4/8/2020 wanda yayi dai² da ƙarfe 11:00am dai², safiya ce mai ciki da tarihi da kuma abin mamaki,gaba ɗaya ƴan wajan fuskarsu ɗauke da murmushi hadda Mus'ab dake gefe yasha ado cikin manyan kaya,a hankali limamin masallacin ya fara addua da kuma gabatar da abinda akazu yi,yayinda da a gidansu Mus'ab kuma kowa yasha kwalliya mai kyau inda Hajia take sanye da wani less mai ɗinki buba mai green colour tana zaune a ɗakinta ita da wasu manyan mutane suna shira,Najwa kam gaba ɗaya ranta babu daɗi domin zuwa yanzu ta tabbatar da ba ita za'a aurawa A.j ba,koma wace tayi ganganci kuma tayi kuskure sannan kuma za tayi ladamar aikata abinda ta aikata,tana zaune a parlour cikin shigarta wacce ta saba wato abaya mai pink colour yayinda tayi rolling ta mayafin abayar,jin anata ɓaɓɓaka dariya yasa na jiyawa ga mamakina sai naga Anusha zaune tana danna wayar Hajia da alama game take,sanye take da wani black siket iya cinyarta sai kuma wata blue t.shirt mai dugwan hannu a gaban rigar an rubuta HAPPINESS anyi mata kitso guda biyu akan wanda ya sauko har gadun mayanta,wata zabura naga sunyi gaba ɗayansu jikinsu na tsuma musamman Anusha wacce idonta ya ciko da gwalla ba komai ya haddasa hakan ba saijin abinda limamin Masallacin ke faɗa.

(tabbas ina farin ciki kuma ina mamaki yadda book ɗinan ke zagawa ko ina,nagode Allah🙏🏻yanzu aka fara wannan book ɗin dan haka ku kakkaɓe zani guys🤟🏻idan baki karanta ba ki nema a wani waje nima kaina bana tarawa a guna taran ake,masu cewa na turo masu daga farko kuyi hkr,masumin barka da sallah nagode duk da ban samu damar dubawa🙏🏻Maman maama gruop zandai na posting sabida naga comments ɗinku yayi ƙasa😕Wattpad ɗina ina maku barka da sallah kuma naga kundaina comments why?😒ina jiran naman sallah na pls😥)

Comments#
Vote#
Shere#

*🤱🏻RAINO ne SILA🤱🏻*
_ADOPTION IS THE REASSON BEHIND_

*_NIMCY LUV_*
👸🏻S@r@ut@👸🏻

@Wattpad
Nimcyluv

*SALON NA DA BANNE🤟🏻*

*👸🏻FADAR NIMCY LUV💘 wannan page ɗin na kune watan zaku ji daɗinsa ina gdy da Comments🤗*

*🌈KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION🌈*

*39-40*

Ƙara sautin kukanta Anusha tayi still idonta naga wayar hannunta amma kana ganin face ɗinta zaiyi showing damuwar da take ciki, ba komai ya haddasa hakan ba sai game over da akai mata sabida duk nacinta na game bata iya game ɗin TAMPLE ba, hakan tasa ta nace shine ta nayi aka cita,wannan dalilin shiya sata kuka dan ji tayi kamar tayi cilli da wayar ta huta amma ba zata iya ba.

Ta rasa maiza tayi domin nuna godiyarta ga Allah daya nuna mata wannan rana mai cike da tahiri da kuma al'ajabi,tabbas idan ba gizo kunanta yayi mata ji tayi Limamin yace.

"an É—aura auren DR AHMAD TIJJANi ASASA da NAJWA FAROUK akan sadaki dubu hamsin cif"
Chapter 11 · 0% Book details