Sashe 56
Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Ya kuma samunta da complain shifa bawai tamai abinci yaci ya kwanta da ita ne farin cikinsa ba,yanzun farin cikinsa bai wuce ta saki jikinta ta koma normal ba,data zauna tayi tunani da tayi banzan nan dashi in yayi gaba can zai tare inda kadangarun bariki suke sai yaga dama bacci zai kawosa amma shi yana ta faman binta sai ta kara rikosa tare da jansa jikinta saboda ta samu ta rabashi da kowace,cikin kwanakin suka koma daidai da sharadin cewa inya kara duk hukuncin data ga dama ta masa shi yaja. yaita kokarin ganin bai kuma barin wata baraka da zatasa beauty ta gane yana tare da wata ba.Hankalinta kwance yanzu,damuwarta bata wuce son samun ciki ba,wanda in tayi magana sai yace ta daina damun kanta,kwata-kwata shekarun son nawa da za‘ace sai anyi masa kani?Sannu a hankali ta soma zargin cream din da yake shafawa in zasu kwanta, domin ta kula inya kare komai matsuwar da yayi da ita yakan hakura,don haka sai ta dauko salon cewa ita dai tana jin zafi maimakon ce matan da yayi cream din zai sa su jin dadi,ta tubure tace ita sam bata so ga zatonta zai bari sai taga yayi matukar daukan zafi da ita harma ya fita harkarta, gami da kaurace mata, ita ma ta yarda da hakan suka share juna na kimanin sati uku,su duka sunji jiki domin shima duk da yana da Tina ya gane bawai biyan bukata ne kawai amfanin beauty ba tana da wani matsayi wanda mata da yawa basu takashi ba a cikin zuciyarsa.ita kuma babu abinda yafi kona mata rai yanda ya daina cin abinci agida wani sa‘in ma sai tayi kwana biyu bata sashi a idanunta ba,kuma zuciyarta ta dinga raya mata cewa yana can tare da matan banza.Ganin bazata iya cigaba da wannan zaman ba yasa ta samesa, sai ce mata yayi indai bazata yarda suci gaba da amfani da wannan cream din ba sai dai su zauna a haka Ga Allah ta koma ta cigaba da gaya masa kafin wani tsawon lokaci sai gashi ya soma sakkowa,tana zaune yazo ya sameta yace tayi masa tuwon semo,bata tsaya jan aji ba ta shirya masa tuwo miyar danyan kubewa,sannan tayi kwalliya irin wacce bata taba yi ba,lokacin da yazo cin tuwon sai ta bayyana donta zuba masa tun yana satar kallonta harma daga karshe ya zage da kallon nata ita kuma tayi amfani da wannan damar ta saki jikinta tamkar wani abu bai taba faruwa ba.ganin haka shima yabar cin abincin suka koma wani fanni,sai da suka tausaya ma junansu,aranar lallai sun fahimci sunyi missing din juna daga nan suka ci gaba da harkokinsu. amma kuma sai me?Data samu ciki wata daya biyu sai ya zube kuma ya dubata acewarsa ba wata matsala anyi haka har kashi hudu,inda abin ya soma damun Umma,su anty Saliha kuwa cewa sukayi ita ke cirewa shi kuma tsabar son mace ya hanasa ya gane hakan, tsana suka kuma saka mata tare da zuga Umma akan Yarima ya kara aure, umma cewa tayi babu ruwansu amma anty Salma sai data kirasa tace, lallai ne ya sake aure,sannan sukayi kungiya suka samu Bily suka ce inma tana cire ciki ne don tayi sisi to su karuwa suke so kuma Umma tace dole ne ma ya sake aure.hankalin Bily yayi matukar tashi,jin cewa harda Umma cikin lamarin.da sauri ta kira Mansu ta shaida mata halin da take ciki,Mansu tace mijinki ya canza miki?Tace,a‘a shi yana boye min maganar nema bai san sunzo har gida sun gaya min ba,tace to ko da wasa kada ki canza masa kinji ko?Tace to sannan kadaki yarda ki sanar dashi duk abinda ‘yan uwansa suke miki tace shikenan Mansu tace shawara daya itace ki dage da addu‘o‘i,nafilfilu kiyita gayama Allah,tace to cikin kwanakin shi kansa Yarima ya fahimci tana da damuwa,haka nan inya farka sai ya ganta tana nafilfili,wannan karon data samu ciki bata bari ya sani ba,don tana tunanin da sa hannunsa yawan barin ta tunda bai taba nuna damuwarsa kan cikin ba don ya fita,sai dai ya damu da lafiarta,ita kanta tana son ta sake haihuwa ballantana ga bala‘in danginsa duk da nuku-nukun data ke har cikin yakai wata uku. Nan fa ya farga ya tambayeta kan cewa ciki ne da ita ko?Tace me ka gani?Yace, alamu da dama,tace shine don Allah ka tayani addu‘a wannan karon Allah ya bar min,yace to yanda yake amsa zancan tasan bai kai zuci ba,sai dai zatayi taka tsantsa da duk wani magani da zai bata.har aka kwana biyu bai bata komai ba kuma bai canza mata ba,yana ma taji da ita ne,ashe yana amfani da wani mai ne in yayo wanka sai ya shafashi cikin toilet din a gabansa da zaran ya kwanta da ita sai cikin ya fita wannan karon ma haka yayi bayan ya fita,zuwa asibiti misalin sha biyu sai taje fitsari nan taga jini,da sauri ta fito taje ta shirya ta nufi gurin Dr. Aisha,bayan gama bincikenta ta gano cewa Yrm yana amfani da wani sinadari ne dan fitar mata da ciki,sannan tace wannan cikin ma fita zaiyi.Bily bakin ciki ya isheta,Dr. Aisha tayi mata allura tace taje gida.har zata gida sai kuma taga ba zata iya daurewa ba sai taje asibitin ta tabbatar masa ta gano komai kuma zata shaida ma Umma komai,tana zuwa baya office nan nurse din dake kula da marasa lafian dake shiga gurinsa ma‘ana mai kai masa katuna tace yanzun nan ya fita gama marasa lafia suna jiransa zai dubasu da yake sun san ita matarsa ce,tace ina to yaje nurse tace,kila suna wani aiki ne a cikin gidan Tina,har zata shiga office din ta zauna sai kuma tace am nurse ina ne gidan?Tace gashi can bari in nuna miki suka fita ta kaita har bakin gate din gidan kai tsaye ta shiga ta ratsa dan tsakar gidan mai kyau da furanni ta isa kofar da take zaton ta falo ce,ta tura sai taci sa‘a abude ne ta tura ta shiga ta shiga falon mai kyau ta waiga ko‘ina babu alamun mutum sai dai taga kofofi guda uku.ta juyo da nufin ta fito sai taji maganar TV cikin wani daki ta nufi gurin har zata kwankwasa sai dai ta fasa ta kama murfin kofar ta murda sai taga kofar ta bude,duk da gargadin da zuciyarta ta rika mata kan cewa ta fa yi gangancin shigo ma mutane gida,hakan bai hanata leka dakin ba,TV ta hango sai ta cusa kai,take numfashinta ya soma zarya da kyar ta iya furta Inna lillahi wa‘inna ilaihi raji‘un da karfi. Wanda hakan yayi sanadiyar jawo hankalin Yarima da wanda kamu ta masa irin wanda ake cewa turmi da tabarya, da kyar ta lalubi hanya ta fita,tana mai data sanin wannan zuwan da tayi. data jirasa ya koma gida ta zauna acikin mota ji tayi jinin yatsunko mata gaba daya da sauri ta ciro wayarta ta kira direbansu tace dan Allah ya hau mashin ya sameta asibitin Yarima tazo ne bazata iya dawowa ba,babu jimawa sai gashi ya jata zuwa gida,dakyar takaicin gidan yasa ta isa dakinta ganin halin da take ciki ne direban ya shiga gurinsu Umma ya shaida musu.lokacin da jakadiya ta iso ciwon baya da mara sun tirnike ta,nan take jakadiya taje tana ya mutsa baki tana cewa Umma wannan mata ta Yarima bata da dabi‘a to gata can ta kuma yo allurar zubar da cikin tana ta murkususu jini yana zuba,Umma ma haushi ne ya kama ta, amma duk da haka sai tace jeki kula da ita jakadiya,ba laifinta bane laifin mijin ta ne da tun farko ya nuna mata bacin ransa daga na daya ai bazata kuma ba,bari in kirasa yazo ya dubata su dai suka sani,ni menene nawa Allah na tuba jika wane iri ne ban gani ba.lokacin da Umma tayi masa waya ya zaci ko tazo ta fada ne a tsorace ya daga wayar,tace masa sai kazo ga matarka nan kila barin zata kuma yi ta kashe wayarta,lokacin daya iso tama sume bata san wanda ke kanta ba a firgice ya dauke ta zuwa mota Asabe ce kurum ta bisu suna isa asibitin a gigice ya sureta zuwa Emergency su uku ne kanta shi ya kasa yi mata komai ma,cikin ya fita sukayi mata wankin mara sannan suka kaita daki na musamman ta farka ne ta ganta a dakin asibiti. kwananta biyu duk babu wanda yazo dubata kaf dangin Yarima ance sai Umma lokacin tana bacci su Salma cewa sukayi bazasu zo duba taba tunda tana sani.Yrm ne ko yaushe yana dakin sai dai ya kasa ce mata komai kamar yanda ko ganinsa bata son yi shi dai bashi da tacewa ne, sannan ga carin da ‘yan gidansu suka rutsa sa suna masa yayyinsa ne suka tsara shi a gaban Umma sunce matarsa tana zuwa tana cire ciki yakasa yin komai akai saboda ta mallakesa, don haka zasu nema masa aure, Nan take anty Saliha tace ‘yar mijinta Nafisa ta jima tana son Yarim kuma Nafisa tana da hankali sosai,shidai jinsu kawai yakeyi shi damuwarsa daya mummunan kamun da matar tasa tayi masa, yanzun bai san yaya zasu kwashe ba in ta warke, gashi shi ne silan wannan wahalar da tasha duk da yana zaton bata san shi ne sila ba inda ma yake jin da dan sauki kenan.da yamma su Magaji suka zo dubata tace haba Magaji maimakon kabar Sumayya ga tsohon cikin nan?Yace to nace ta zauna tace ita dai zata zo Bily tace shikenan na gode, duk surutun da akeyi cikin gida Magaji yaji sai dai bai yarda wani Bily ce ke cire cikin ba sai dai ko Yrm so yake ta fito daga asibitin yaji komai kuma yasha alwashin sai su Umma sunji. washegari ta fito daga asibiti,Yarima yazo yace an sallameta tazo ya kaita gida,bata musa ba dama kala bata ce masa ba ta shiga mota suka nufo gida. nan shima ya dan zauna shiru sannan ya fita jim kadan su anty Salma suka zo sukayi mata ta tas,har da cewa dama dan talaka bai iya samun guri ba,anty Fulera tace zaki ga tsiya aike baki ma iya abun ba inma cin dukiyar kike so dakin haifa kin tara dakin samu,yanzun kuma zamu kawo wadda zamu karu da ita ‘yar masu dashi, suna fita ta tashi zaune ta ma rasa meke mata dadi duniya,nan ta dauko jakarta ta dibi ‘yan kayanda basu fi biyar ba sai dai kudi ta dauka ta zari makullin mota ta fita.sai data hau titi tama rasa ina zata?Kai tsaye ta dauki hanyar Kaduna, gidansu Mansu taje ita kanta tasha mamakin tukin da tayi domin bata taba fita cikin Bauchi da mota ba,Mansu bata Kaduna suna zaria kuma daga nan zasu wuce Gombe saboda hutun karshen shekara da Faruk ya samu,maigadin ne yace mata basa nan tace ta sani itama wani aiki zata yi a Kaduna ta shiga ta aje kayanta cikin dakin Mansu,sannan ta zauna ta rubuta ma Yrm text kamar haka.
[8:43AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 90ðŸµ
[8:43AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 90ðŸµ