Sashe 44
Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Dubi fa ki gani tafiya nayo ya dace ace ya kirani yaji shin yaya muka sauka?Mansu tace bari kiji.Duk abinda Yarima ya miki ke kika so,sufa maza ayau suke daukar kai saboda suna kallon matan dake yawo a titi kowane haki garesa inba shirka yakeyi ba to kiyi kokarin rike abinki in kin ki na waje su sa rike miki,shawarata gareki lokaci yayi da zaki aje batun so ko rashin so,ki jawo mijinki gareki ki hada da addu‘a sai kiga Allah ya shirya miki shi,batun kice karamin yaro ne bai taso ba,Bily ta katseta da cewa nifa don wadannan matsalolin naso in auri babba mai shekaru wanda sai dai in hakurinne shi zaiyi dani,ya ririta ni amma yanzun duba fa nice zan ririta shi,Mansu tace ke ba gara wani yaron ba yanzu akan wani babban?Manyan nan masu budurwar zuciya kinsan Allah ki kama mijinki,musamman yanzun da babu ‘yanmatan a gabansa gashi mai nacin son mace,sannan yanzun duk ‘yanmatan nasa basa kusa sai kace ba mace ba?Haka Mansu ta zauna tana tsara ma Bily yanda zatayi tasamu Yarima akarshe tace bani wayarki a kirasa, sai ki nuna masa kin damu dashi.Bily tace,kinsan Allah in kin kirasa kila ma wulakancin zai min.Mansu ta dubo numba din sai taga wai Bily ta rubuta(Y)a numba din tace to kalla fa don Allah,numba din mijinki ne kika rubuta(Y)to me yake nufi?Bily tace(Y)Yarima kenan,farkon sunansa na doka masa.Mansu ta goge tasa sweetheart,Bily tace su sweetheart anji jiki nan dai Mansu ta kira layin yayi ringing har ya katse ba‘a daga ba,Bily tace kin gani ba? Mansu tace an masa uzuri,ta sake kira nan take ya daga tare da cewa hello wanene?Mansu ta mika mata,nan duk Bily ta daburce lokacin da yake sake cewa wanene?Tace nice,baka ma san me numbar ba ko?Yace,kece wa?Haushi ya kamata tace lallai Yarima to nice Bily matarka,shine saboda tsananin rashin so ko numba na ma baka da ita.Ya gyara zama to ke in banda abinki me numba dinki zatayi min bayan ban taba ganin kin kira ni ba,ko kina nufin sai na ajiye ta cikin phone dina alhali bata da wani amfani gare ni?Yaci gaba da bana yin haka duk numba din dake phone dina masu amfani ne. Nan Bily ta gane laifinta don haka sai tace shikenan zan rika kira sai kayi savin dinta ko? Yace lafia kika kirani?Tace lafia lau na dai kira ne naga kai baka kirani kace yaya muka sauka ba? Yace,to kun sauka lafiya?Ban zaci zaki so kiran nawa ba ai I hope kowa lafia?Tace,lafia lau,yanzun ma ina gidan Mansu ne,nace bari na shaida maka bance zanzo ba kada nayi laifi,yace No,ba wani laifi kina da ‘yancin zuwa duk inda zakije,ni mutum ne wanda yasan ‘yancin dan Adam, tace na gode sai da safe. Ya rigata kashewa ta kalli Mansu wadda itama taji duk abinda suke cewa saboda sun sata a handsfree.tace kin soma gano laifin ki ko?Yaron yasan abinda yakeyi don haka ki gyara takunki da safe ma sake kiransa ki gaishe shi.Bily tace,ni duk komai ina ganinsa banbarakwai ne,anya zan iya?Mansu tace,zaki iya sannan sai ma kinsha gyara zaki bar nan,da kin koma kada kiji kunya ki saki jiki ki jawosa ki mantar dashi matan banza ya zama kafin ma ya koma kin dasa kanki garesa,Bily tace,to Allah yasa zan iya,ni kunya ma nake ji inna tuna shekararmu daya dashi, nan gaba yazo yace yarinya yake so.Mansu tace ai sai kiyi,shin haramunne aurenku?To in baki sani ba bari in sanar dake,Manzon Allah (S.A.W)matarsa ta farko ta girmesa,kuma bazawara ce,shin in haramunne haka zata kasance?Bily tace,a‘a Mansu tace don haka saki jiki ki rike mijinki,Allah ne yasan dalilin zaba miki shi, kuma gata Ubangiji yayi miki sai nan gaba zaki gane,ga lada in kikayi sanadiyar shiriyarsa.Bily ta soma yarda da shawarar Mansu,don haka cikin kwanaki ukun da zatayi sun shirya duk yanda zatayi inta koma ga gyara tasha,ta shirya sosai kuma ta dauri aniyar ba sakaci daga yanzun cikin kwanakin sunyi rabon tsaraba,su Sakina ma sun koma gidajansu cike da tsarabobi masu yawa,su da ‘yayansu har ma da abokan zama,Bily ko ranar da zasu tafi ta kara shiri sosai sauran batu zasuyi shi awaya, itama Mansu haka ta juya Kaduna cike da tsarabar da Bily dinta ta cikata dashi. Tun acikin mota tana kwance zuciyarta ta shiga kai kawon yanda zata jawo Yarima gareta. nan take ta ciro wayarta ta soma neman Yarima,sai ta samu kanta da karya muryarta,lokaci daya dauki wayar yana fadin,hello tace mijina ganinan ina dawowa yayi dan jim,don muryar ta dokeshi,sannan yace,to sai kun iso.Tace kana murna kuwa?Yace to murnar me zanyi,me kike min in kina gidan?Tace la,dama kana son inma wani abu shine baka sani?Yace,au,da sai na saki?Ina ce tun kafin kizo gurina an karanta miki zaman aure?Tai ‘yar dariyar kissa,oh yes,na manta ne yace shikenan yanzun tunda kinje ai sai a tuna miki ko,yacigaba da cewa sai kin iso yanzun ina driving ne,ya kashe wayar.Sun iso daf da magariba ta shiga gurin su Umma suka gaggaisa ta kuma sanarda Umma iyayanta suna godiya kafin suzo an shigo da tsarabar zaria,su kuka ne,kubewa da dai sauransu,tunda kowa da sandar hannunsa yake kai duka.Data koma sasansu kuwa,lokacin an gama share mata ko‘ina an goge.tayi wanka ta shirya cikin wani material bulu da ja,tayi kyau bata daura dankwali ba,sai ta daure gashinta da dankwalin.ta nufi sasan Yrm gabanta na faduwa,ta samesa kuwa yana waya da Ashly ta danne zuciyarta har suka gama,ya dubeta fuskarsa kamar kullum, wato gim,ta zauna kusa dashi ta rike hannunsa tana murmushi tace,mun dawo.Ya dubi idanunta kun dawo lafia? Da idanu ta amsa masa tare da daga gira,wani iri yaji ajikinsa, har sai da yayi tsam.ta fito da harshe ta dan lashi lebenta kowa yana gaishe ka.muryarsa ta dan sarke ina amsawa. Ta mike kamar zata fita ya bita da kallo tamkar yace dawo,amma girman kai y hana,sai ta juyo nan take ya wani dauke kai ta dawo, kaci abinci?Kin damu inci ne? Tasa yatsanta daga goshinsa ta biyo dashi takan karan hancinsa har zuwa lebunansa,tana cewa sosai ma,me kake so?Shi kam tuni ya soma sakin layin da yake,don duk jikinsa ya motsu gani yake Bilyn daya sani ce ‘yar kauyen nan mai boye kanta?Ya dai dake yace,na koshi.ta nufi fridge ta dauko jus din dayafi so tazo ta tsiyaya cikin kofi ta mika masa,to sha wannan.
[6:37AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 73ðŸµ
[6:37AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 73ðŸµ