← Book details Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 60

Sashe 50

Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda Umma tasa aka yi mata kiran bilkisu, ta tambaye ta ko lfy wayarta take ana ta nema ba a samu? Sai bilkisu tayi karya da cewa, batirin wayar tata ne ke da matsala, amma ta aika yanzu za siyo mata wani, Umma tace to dama maigidan ki ne yake ta nemanki, tace zan kira shi in nasa batir din.

Bayan taje daki sai ta kunna wayar ta cikin sa'a yana neman ta sai gashi ya samu wata irin ajiyar zuciya ya yi tun kafin ta dauka sai ya ji wani sanyi cikin zuciyar shi, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta daga. Da sauri yace, beauty, beauty, kina jina? Ta soma shassshekar kuka,sai kurum ya samu kanshi da cewa innalillahi wa inna ilaihin raji'un, wai beauty me ke faruwa ne? Cikin kuka ta ce dole mana ka ce meke faruwa? Ka min ciki sannan ga wulakancin ka har da cewa baka damu da bacin raina ba to ni ba zan iya zama ba gidanmu zan tafi. Yana son yace ki tafi din mana, amma sai zuciyar shi ta ki furta haka,sai kurum ya ji bakinshi yana cewa, haba saurare ni ki ji.in ji wa ya ce ban damu da ke ba? Da kin tausaya min. Don Allah kiyi hakuri. Sai kuma yayi shiru yana mai jin haushin kanshi, yaushe ne yake baiwa mace hakuri amma zuciyarshi murna take yi musamman da taji bilkisu tana cewa shi kenan ba zan kara kashe maka waya ba, to kana son cikin? Yana tayi maganar cikin sigar shagawaba sai da tsigar jikinshi ta tashi, sannan nashi ra'ayin shi ne ya ce mata A'a amma ya kasa fadin hakan, sai ya samu kanshi da gudun bacin ranta, don haka sai yace ya ya zan yi ni dole in so shi tunda ni na diga shi, sannan shakuwarmu dake tasa ba zan guji duk abin da ke jikinki ba, tace kana nufin yanzun ka damu dani? Yace, ke baki damu dani ba? Tace na damu mana, sosai ma. Har fa tunanin ka nake fa zama in yi da baka nan.
[8:39AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 82🏵

Ta marairaice murya,kai fa kana tunanina? Yace inna ce miki banayi ai zaki musa ko ban tunoki don komai ba ai na tunoki ko don hutu beauty,ina bukatarki kusa dani,tace kilama ka samu wata,da sauri yace haba dai ni yanzun naki ne ke kadai taji dadi sosai sannan tace nima haka,yayi dan murmushi na sani beauty tun ranar farko dana soma kwanciya dake nasan cewa nayi dacen mata,Allah yayi min baiwa,bai duba halina ba,bai hadani da ‘yar uwata ba wato mazinaciya, sai ya bani mai kofa a rufe nina budeta, tace ni ko kaga bana son in tuna wannan rana,yace don me?Dan wulakancin dakayi min, yayi ‘yar dariya niko abubuwa da yawa sun tsaya min a rai ranar,zan gaya miki in nazo,tace shikenan sai anjima?Yace kin kosa muyi sallama ne?Tace a‘a nace kona tsare maka aiki ne,yace shikenan zamuyi waya da dare,tace sai naji ka kenan itace ta fara kashe wayar shi ko tsayawa yayi tamkar wawa,yana son tuno tabargazar da yayi shin me ma yace mata?Kasa tunowa yayi sai ma wata annashuwa da zuciyarsa keyi,hira tayi dadi tamkar acigaba sam ya manta me yakeyi ne,ya nutse cikin tunaninta.Tina ce ta dafa kafadunsa da sauri ya dubeta tare da fatan Allah yasa beauty ce ganin Tina sai yayi tsaki, jikinta babu kwari ta sakesa ta zauna tuni itama ta soma sabawa da halinsa,sai dai Allah ya jarabceta da sonsa,shiko duk sanda yake kan begen beauty yakan manta da komai da kowa baya son a matsa masa,wanda nasa ganin shakuwa ce duk ta kawo haka.Bily kuwa yanzun hankalinta kwance ga tattalin da surukanta suke mata, labarin cikinta ya yadu ko‘ina,don ko su Mamanmu da Mansu ta sanardasu sunyi murna, sannan gashi Yrm duk ya birkice kanta,don da taba Mansu labari Mansu cewa tayi Allah sonki yakeyi Bily tace a‘a duk hirar da mukeyi bai taba cewa yana sona ba,yadai nuna kulawarsa gareni,so kam ai na riga nayi rashinsa bazan taba samun wannan kalmar ba,Mansu tace shikenan za kuma ki gane nan gaba.

Yarima da Tina an sake dinkewa,a zuciyarsa yana kara shige matane da tsawonta da tsawon gashinta suna tuno masa da beauty, ita ma ta fahimci yana da wata a cikin zuciyarsa domin in suna kwance sunan beauty kawai yake kira.sannan inya shiga wanka takan dauki wayarsa ta masa bincike tana son sanin wacece beauty din nan?Yaya take ne don ta samu matsayi mai girma gurin wannan tsadaddan yaron.Kimanin wata hudu kenan da tafiar Yrm,cikinta kuwa yana wata biyar kenan tana zaune tana cin kwakwa da tasa aka siyo mata, Sumayya ce ta shigo tana sanye da leshi ja da kuma ratsin baki yaune zuwanta na uku gidan,ta zauna tare da cewa Maman biyu,Bily tayi ‘yar dariya tace,Allah amin ya biya bakinki Sumayya tace amin.nan suka soma hira duk data hakura da Yarima amma duk sanda ta gansa ko taga hotonsa sai taji ma kanta haushin rashin samunsa, yanzun ma da take zaune kallon hotonsa takeyi tare da yaba kyansa, cikin zuciyarta. Bily tace,Sumayya kina kallon wuta ne fa,yakamata ace yanzun kin cire Yarima acikin rayuwarki,sannan ki godema Allah daya baki Magaji matsayin miji,tace ai tuni na hakura anty Bily, matsalata daya yanda zan cire shi daga zuciyata,ki dinga addu‘a inji Bily,ki rike mijinki Sumayya so da yawa abinda ka kwallafa rai kansa baka samesa ba to sai kiga alkairi ne rashin samun,ni kaina ban taba tunanin zan auri kamar Yarima sa‘ana ba,babu irin takaicin dabanyi ba game da auren amma yanzun sai ina ganin alkairai da dama acikin aurenmu.don haka ki kama mijinki ki samu ladan aure,Sumayya tace to nina rasa sam sai inga sam Yarima yafi Magaji komai, Bily ta hade fuska Sumayya lallai zaki daina zuwa gidana,domin babu wanda yafi wani gurin Allah face wanda yafi tsoronsa,in dai kina so mu shirya to ki kama mijinki. Sumayya tayi ‘yar dariya ganin ran Bily ya baci,tace na daina anty Bily,shima Magaji cewa yake duk ranar dana zo nan gidan wai bana bata masa rai,shiyasa yake son inzo gurinki,ina aiki da shawararki,nan dai suka cigaba da hirarsu.Wani dare Bily tana bacci sai kawai tayi mafarki wai ga Yarma an kawosa ya rasu,nan take ta farka duk tayi sharkaf da zufa,ta kalli agogo sha biyu da ‘yan mintuna duk da lokaci ba daya ba ne ji tayi bazata iya komawa bacci ba har sai taji muryarsa nan take ta kira layinsa daidai lokacin ya shiga wanka,Tina ce kwance rigingine a tsakiyar gadonsa,don haka wayar tana yin ringing ta dauka ta duba(beauty)taga an rubuta,da sauri ta daga wayar tare da cewa, wacece ke?Cikin harshen turanci. Bily ta tsorata, gabanta na faduwa tace,kiba mai wayar,Tina tace sai ta fada ko ita wacece,ran Bily ya baci dama Yarima yana nan yana harkarsa da matan banza,shine yace mata ya daina?Wani tukuki taji azuciyarta nan take ta kashe wayar cikin tane ya shiga murdawa,ji take tamkar zata haihu Yarima yana fitowa daga toilet din yaga phone dinsa ahannunta,nan take tayi saurin cewa an kiraka amsar wayar yayi ba tare da yace mata kalaba,koda ya duba yaga beauty ce ta kira kuma har ta daga nan da nan sai yaji hankalinsa ya tashi,da sauri ya soma kiran layinta,tamkar kada ta daga amma sai ta kasa tana dagawa sai ta saki kuka ya rasa me zaice,sai yace kiyi hakuri beauty na kasa controlling din kaina ne yau amma insha Allah bazan sake ba,na amsa laifina kiyi min addu‘a kinji?Cikin shesshekar kuka tace, Yarima baka min adalci ba,yaya na tsare kaina a gida kaika dinga bin wasu,ina tsoron kada Ayar Allah ta sauka akaina,domin Allah yace in har kabi matar wani sai anbi taka,in ‘yar wani kabi kaima za‘a bi tak,haka kuma mazinaci baya aure face sai da mazinaciya ‘yar uwarsa,ban kasance mazinaciya ba. Yarima ma jikinsa yayi sanyi yasan gaskiya ta fada ina ma gata gashi ne ya rungumeta tare da lallashinta, duk da haka sai yace na sani beauty ban kyauta miki ba,amma kada kiyi fushi dani zan shiga damuwa kinji?Tayi ajiyar zuciya,sannan tace bazaka daina ba Yarima ,yace ki daina fadin haka,insha Allah zan daina nidai kimin afuwa, tace Allah zaka roka donshi kayiwa laifi,da sauri yace zan rokesa,don Allah beauty kadaki kashe min waya kinji yanayin yanda yayi maganar sai taji dadi,tace bazan kashe ba
[8:40AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 83🏵

Zuciyarta tayi sanyi domin lokutan baya Yrm yana neman matansa a gabanta, zai iya kwanciya da mace a gabanta,amma yau gashi wayarta kawai mace ta daga duk ya birkice, ta san ko har yanzun Yrm yana neman mata to ta samu wani matsayi agurinsa tunda yake boye mata baya son ta sani,bugu da kari Yarima ne harda bata hakuri,tayi mamaki domin tasan sa sarai baya daga cikin mazan da suke bawa mace hakuri,baya lallashin mace amma ita sannu a hankali ya soma yi mata abubuwan da yake ikirarin bazai iya yiwa mace ba, zata dage da rokon Allah har Allah ya shirya mata shi. Shi kuwa Tina ya tsirama idanu cike da bacin rai irin wanda bata taba gani ba,don haka ta tsorata har ta shiga bashi hakuri,cewa yayi ta fita kawai.tana fita ya fada kan gado yana rubuta ma beauty dinsa text na ban hakuri, sai daya gama sannan yayi shiru yana mamakin kansa,shine Yrm kuwa?Shine mai ja ma mata aji? Shine wanda mata suke bi bashi ne ke binsu ba? To menene yasa shi rikicewa kan beauty?Yanda ya dade dasu Vicky bai dade da Bily haka ba me yasa zuciyarsa bata shaku dasu kamar yanda ya shaku da ita ba?Me yasa ita baya jin ta gunduresa?Me yasa baya son bata mata rai ne? Domin inya bata mata rai zuciyarsa sai ta ringa yi tamkar zata fashe,bai saba da damuwa ba,don haka baya son zama cikin damuwa,inya bata mata rai sam cikin damuwa zai zauna shiyasa yake kiyayewa.
Chapter 50 · 0% Book details