Sashe 38
Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Ya daga kyallen tebur din ya watsa mata a jiki ya fita daga gidanma.Tsaye Bily tayi tana tunanin dama Yarima ya iya ihu haka?Allah ya kyauta.Shi kuma tun daga ranar ya bude mata sabon daure fuska,wani bari na zuciyarsa yana zugasa kamar sa Yarima dan sarki wannan zatayi ma wa‘azi? Lallai ta samu sake,duk da cewa kasan zuciyar nan tasa tana masa zogi,tare da hura masa wutar sha‘awarta, cikin wannan halin azumi ya kai ashirin mai martaba yace,lallai su zama cikin shiri,Magaji yana nan zuwa su wuce saudi tare,su gobe zasu wuce,don haka su samesu can.Bashi da amsar data wuce to duk da suna karatu,yasan tafiyar bazata shafi karatunsa ba,matsalarsa daya itace mata,zaije ibada ne.Ya tsaya neman mata? Sannan ma zuwan Magaji yau din nan zai sa dole ya hakura da kawo mata,shima gaskiya ba sansa bane kawo matan nan da yakeyi cikin wannan watan,amma da zarar yasha ruwa sai yaji su kurum yake bukata, daren ranar yayi niyyar hakura har sai sun dawo amma bazai iya ba,shida kansa yayi ma chelen waya tazo.Suna tare ne a falo sai ga vicky suna jin haushin juna amma ba sa gwadawa a gaban Yarima,domin sun san sa suna soma ‘yan harare-harare zai sallamesu,kila kuma ya zama shine karshen alakarsu,kuma in har kikayi fushi kika tafi,to in zaki shekara nawa sai dai fa ke ki dawo.Shiyasa kullum yake ma kansa kirari baya bin mata sai dai su bi sa.Vicky ta zauna adayan gefen tare da dan tsikarinsa ya dubeta da guntun murmushi,sannan ya duketa a kirji,irin dai wasa na gogaggun matasa.Sun sashi a tsakiya kowace burinta taja ra‘ayinsa kanta,suna tayi masa wasanninsu na jan hankali,musamman da yake sun sansa yafi son wasannin fiya da ya kwanta da su don haka sai suka kuke dayi.Sha biyu da rabi Bily ta farka daidai lokacin da take tashi kenan,tunda aka shiga goman karshe tsayiwar dare takeyi har asubahi,in tayi sahur sai ta kwanta bayan tayi sallar asubahi kenan.Don haka inta tashi takan ajiye komanta na sahur ne akusa,kitchen ta fito don nufin dauko ruwan zafi tana fitowa falon sai me zata gani? Yarima ne da matan nan duk basa a hayyacinsu,batasan sanda tace,A‘uzu billahi minash shaidanir rajim.Sannan tace haba don Allah haba Yarima,kaji tsoron Allah kana tuna mutuwa kuwa?Kana tuna kabari?Kana tuna ranar da zamu tsaya agaban Ubangijinmu?Watan Ramadan cikin goman karshe kuma karshen goman ma da duk wani musulmi yake rage bacci,don kwadayin daran nan na (Lailatul kadari)kuka ne yaci karfinta ta juyo da gudu ta koma ta fada kan gado,sai kuka a dhekarun baya ko watannin baya,tayi kuka tayi addu‘a tayi tsayuwar dare duk roko take Allah ya bata mijin aure.Yau ga miji yaro sharaf mai kyau ga ilmi da ake tunkaho dashi a yau ga kudi ga mulki gata cikin daula taci wanda take so tasha kuma wanda take so, amma hakan bai mata rana ba,hakan baisa ta farin ciki ba,zamanta ada gaban iyayanta yafi mata alkairi,zamanta cikin kunci da kiyayyar mahaifinta yafi mata auren Yarima shin dama haka matan da mazansu ke bin mata suke ji?Lallai ta jinjina musu don suna cikin ukuba,jin zuciyarta take tamkar ta fashe don bakin ciki.Shiko Yarima jikinsa ne yayi sanyi,nan take kwadayinsa ya kwanta sannan ya dubi su chelen yace,su tafi cikin daurewar kai suke tambayarsa dalili, tsawa yayi musu tare da cewa su fita mana?Vicky ta mike ta fita abinta, chelen ce ta tsaya son jin me kanwarsa ta gaya masa? Yace ta fita kafin ransa ya baci da ita,haka itama ta figi rigarta ta fita tana gungunai,shiru Yarima yayi azaune tunani ne fal zuciyarsa yasan tuni ta masa amma anasa girman kai yana nufin ita bata isa ta gaya masa ba,nasa ganin ba girmansa bane tayi masa wannan abin ba.Ya mike ya nufi dakinta har lokacin kuka takeyi,kausasa murya yayi yace,ke!Da sauri ta dago tana dubansa,fuskarsa adaure yace,ban hanaki shiga harkata ba?Bance bana son sa ido ba?Ke kin isa ne ki sani nayi abinda banyi niyya ba?To bari kiji karki kuma shiga harkata, nima kaddara ce Allah ya dora min,bata san lokacin da tace daina gaya min kaddara,Allah baya dorama wata rai abinda ba zata iya dauka ba, wannan wani abune daka dorama kanka.
A yau in kaga dama.... saukar marin data ji ne yasa ta dafe kunne,yace ni kike ma ihu?Ni kike gayama magana?Tace bazan gaya maka ba? Kullum ina dana sanin aurenka bazan gushe ba, gara min auren talaka lis wanda sai ya fita yasha wahala ya nemo sannan muci,matsawar ya tsare kansa daga zina nan ya kuma gabza mata wani sabon marin wanda yasa sai da network dinta ya dauke na wucin gadi.Ya nunata in har kina neman zaman lafiyarki to ki cire idanunki daga kaina iyayena ma basu takura min ba balle ke banza wofi kuma yanda kike dana sanin aurena haka nima nake dana sanin ganinki tun farkon ganina dake,kece mutum ta farko data ke min katsalandan arayuwa,bansan tunani ba bansan mugunta ba duk kece sanadi,ban taba marin wani ba ko zagi ke duk kin sani na iya,don haka in kina neman zaman lafiya dani to ki cire idanunki akaina.Kin taba zagina jahili yau kuma kina cemin mazinaci,kece mutum ta farko da kika taba zagina,ko mahaifina lallabani sukeyi,don haka ina gargadinki da babban murya ki fita harakata,in kin manta wanene ni Yarima Al‘amin nake,ni daya ne tamkar da dubu agidanmu, dan haka maida hankalinki ya fita.Kai ta kifa taci gaba da kuka wato yanzu duniya babu gaskiya don kawai ta sanar dashi abinda zai amfane sa, shine harda dukanta?Ranar dai kwana tayi tana kuka ko sahur batayi ba.Wayewar ranar ne Magaji yazo shi kansa yayi mamakin ganin yanda fuskar Bily ta kumbura,idanun suma sunyi luhu-luhu ya nemi jin ba‘asi tace,ba komai aranar suka gama abubuwansu na tafiya.Ana jibi sallah suka tafi,ko cikin jirgi ‘yar shariya akayi.Magaji da suka zauna guri daya da Yarima yake cewa,kai dama bakaje ba,Yarima yace wai saboda kurewar lokaci? Magaji yace,a‘a bama don haka ba,na gane kana gaba da iyalinka kuma zaka gari mai tsarki.Yarima yace ka barni da yarinyar can ‘yar rainin hankali ce ita,tsaki Magaji yayi tare da cewa Allah dai ya shiryi halinka. Sun hadu dasu Umma da mai martaba gidan da mai martaba ya kama musu nan suka same su.
[4:54AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 66ðŸµ