Sashe 55
Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni dake da kamarki sanin kanki ne kaf kasar nan ke daya ce kike burgeni,tace um ai so bashi a muni, haka sha‘awa yace wai wanene so din nan ne?Ban fa sanshi ba, sha‘awata kuwa bata zuwa irin nan guraren,don haka kibar damun kanki ni naki ne ke daya,tace to yaya batun koyan motar mu fara yau mana?Yace, ok bari muje ko dana minti talatin ne.an kammala gina katafaren asibitin na Yarima,asibitin katon gaske ne mai dauke da fannoni na kalolin cututtuka,ga na‘urori na aiki irin wanda ake cewa sai an fita kasashen turawa ake samu,ga gefe na musamman saboda tada komada wato gyara fata da sauran abinda yayi course akansu an tsaida ranar bude asibitin,nan Yrm ya shiga yo gayyar jama‘a musamman abokan karatunsa wadanda ke kasashe daban- daban.da kuma abokan course dinsa ciki harda Tina.yaso da zai yiwu daya dauki Tina aiki a asibitinsa,saboda ya samu abokiyar aiki fannin fata domin itama ta kware,amma zaya gwada ya gani indai ta amsa gayyatarsa tun ana jibi bikin bude asibitin baki suke sauka,‘yan Zaria ma sunzo gida da masaukin baki tam da jama‘a banda otal-otal da aka kama cikin katon filin asibitin akayi taron inda manyan likitoci,kwamishinonin lafia,zuwa ministocin lafia,ga kuma ‘yan uwa da abokan arziki. Su Tina an duro domin tana ganin sakon sai taji tamkar yayewar matsalarta ce,don haka bata yi kasa a gwiwa ba,ta amsa gayyatar, domin tana azabar son Yarima.taro yayi taro,bayan yin duk abinda yakamata aka bude asibiti inda mai martaba ya wakilta sarkin musulmi ya bude asibitin mai suna(Dr. Yarima Hospital)an dunguma cikin asibitin don ganin cikinsa,hatta bakin kasashen wajen sun jinjina dukiyar dake cikin asibitin,wato kayan aiki zuwa kayan kawata asibitin kafin sati daya tuni asibitin ya kama aiki gadan-gadan.gashi dama ya tanadi likitoci da kuma nurses kwararru.Tina ma ta yarda da gayyatar da Yrm yayi mata,amma sai taje ta dawo. Al‘amura sunci gaba da tafia yanda yakamata,beauty kam yanzun ta gama yarda Yarima nata ne,yanzun ne ta gane cewa halayan Yrm masu kyau ne in ta cire neman matansa wanda ayanzun take tunanin ya daina yana da kyauta ga sadaka yana da kulawa gami da ibada.girman kan da ada take ganin yana dashi yanzu ta gane shi mutum ne mai matukar saukin kai da kuma tsokana duk da bai cika dariya ba,zaya tsokaneka yayi fuska tamkar bashi yayi maganar ba,tuni ya soma ginin gidansa babu nisa sosai da asibitinsa, son ma tuni ya soma takawa shiko Yarima kudi sun kara zaunawa dama dogo ne ga kuma ‘yar kiba irin ta hutu, azumi yana gabatowa tuni Bily ta cire son daga nono,yana gurin Umma tana son zuwa zaria kafin azumi,amma Yarima yace a‘a. Auta Asma‘u tunda ta gama karatu tana gidan gurin Bily duk dangin Bily daga Asma‘u sai su Sakina, Yarima ya sani sai dai yana musu aike ko yanzu da take hankoron zuwa zaria kafin azumi,tana son ne takai musu kayan azumi,bata san tuni Yarima ya tura musu dashi ba,sai gashi babansu yayo waya yana cewa tayi musu godiya gurin Yarima ,azumi yana ishirin suka nufi saudi, wayewar garin sallah suka dawo.rayuwar Bily abin sha‘awa,yanzun ta manta da komai da duk matsalolinta na baya kuma ta yarda da batun Mansu cewa suna son juna koda Yarima baya sonta ita dai tayi imanin tana matukar sonsa, shiyasa kishinsa yanzun yayi yawa azuciyarta, harma bata iya boyewa, duk da bata da masaniya game da Tina sai dai tana zargin kamar yana neman wata,in tayi magana ya kalallame ta da baki kan cewa shifa nata ne ita daya Ranar wata litinin tana kwance a falonta, asma‘u ta miko mata waya cewa ana kira,tana dubawa sunan Umma ta gani tana dagawa ta shaida mata ta fito suje gidan Modibbo zasu dubashi yanzun nan akayi mata waya kan cewa jikinsa yayi tsanani,ta mike da sauri ta nemo mayafi ta soma kiran layin Yarima ,yanayin muryarsa yasa ta wani zargi tace lafia naji muryarka wata iri?Yace na gaji ne kawai tace to zamuje duba jikin Modibbo inji Umma,sai taji yace umh humh sai kuma taji an kashe wayar.yanayin sautin muryar yafi kama da wanda yake tare da mace, don kada Umma suyi ta jiranta sai ta nufi gurinsu Umman,suna mota ta kuma kiran wayar a kashe, sauran layikan kuma suna ta ringing ba‘a daga ba. zuciyarta tamkar ta fashe don bakin ciki,amma dole tayi hakuri ta shanye.suna isa gidan suka shiga gurin nasa Umma ta tallaboshi lokacin ya dubeta duk sukayi masa sannu yana tayi musu godiya,sauran kishiyoyin Umma sun dawo sun barsu acan ita da Bily,ya dan samu bacci suka shiga cikin gidan, kamar minti goma Kawu ya shigo hankali tashe yana ce musu Modibbo dama ashe baccin nan tafiar kenan?Hawaye ne suka soma zirya akan kumatun Bily,ta sani in zata tuna da tarihin rayuwarta to zata tuna da Modibbo,Allah ya jikansa ba zata gushe ba gurin yi masa addu‘a duk sallah.ta soma neman layin Yarima taci sa‘a an kunna a zuciyarta tace an gama kenan,wani irin takaici ne yasa taji sabon hawaye ya zubo mata ya daga wayar da cewa,hello beauty.wani tukuki taji, itace banza ya raina mata hankali cikin shasshekar kuka tace inka gama ne sai kazo nan gidan Modibbo Allah yayi masa cikawa,ta kashe wayar ta shiga neman ‘yan zaria. Yarima yaji rasuwar sosai,dole yayi wanka kafin ya nufi gidan,don haka sai da yaje gida saboda a cikin gidan Tina dake nan asibitin ya tara da ita kuma bazai iya yin wanka a gidan ba. bayan dawowa daga makabarta su Yarima suka shigo cikin gidan,Bily kam ko son ganin Yarima batayi,tana zaune da carbi kanta na kasa,Yarima ya zauna kusa da Umma yana mata gaisuwa,ya dubi Bily,beauty yaya muka ji da hakuri?Banda Umma dake gurin da sauran mutane da bazata amsa ba Amma duk da haka bata dubesa tace mun gode Allah,Umma tace Bily ta kasa daina kuka shi Modibbo yanzun ai sai addu‘a, a ranta kuwa cewa tayi yaya ma zata iya daina kuka alhalin mai tayata addu‘a akan Yarima yanzun babu,sai yanzun ne data kamu da son Yarima shine zai koma bin matansa,ita kam ta gaji da hakuri bazata iya ba.har ranar da akayi uku Yrm ya kasa gane kan Bily,sam ta fita harkarsa galarin gabanta kawai takeyi ko tana dariya ne data gansa sai kawai ta daure fuska. washegari bazasu je gidan rasuwar ba domin an riga ya anyi sadakar uku,har ya fita sai kuma gashi ya dawo kusan misalin karfe sha daya tana kwance cikin dakinta ya shigo,Asma‘u ya fara gani a falo yace mata ina antynki?Tace tana ciki.ya shiga tayi rigingine fuskarta tana kallon sama tunani takeyi koda iyayanta suka zo gaisuwa Yarima bai ma zo sun gaisa ba har suka tafi,duk da yayi ta kiran waya yana cewa gashi nan zuwa wai yana duba wanine sai bayan sun tafi sannan yazo.ya zauna gefen gadon beauty tashi muyi magana,ta tashi zaune ba tare data kallesa ba,tace ina jinka yace a haka zamuyi maganar kina kallon wani guri ta juyo ta kallesa sai dai ranta a daure yace wai ni shin menene ya faru ne kika saka ni cikin damuwa?Me yasa kika saba min da kanki da hirarki da dumin jikinki kinsan ba zaki dore ba?Shin ko rasuwar nan ce duk tasa kika koma haka?In ma rasuwar ce niya kamata infi jinta, domin duk yanda zaki damu ni zaki yiwa kara.ta dubesa rai bace, in kana zaton kara nayi ma donna damu da rasuwar Modibbo kayi kuskure, domin duk wanda yayi kukan mutuwa kansa ya yiwa,kuma da zaka ce na saba dayi maka kaza da kaza ina ce yanzun ka samu madadina ce?Ya dubeta ban gane ba?Tace ai bazaka gane ba,bari kaji nifa yanda na juri huldarka da mata da yanzun bazan iya ba,Allah sai in kama gabana. A haka kowa ya ganni zai zata ina jin dadi ana min kallon sha‘awa da hutu amma zuciyata ba hutu?Ya daga mata hannu saurara min,me kike nufi da zuciyarki ba hutu,me na miki? In kana so dole sai na sanarda kai zan iya domin kayi ne dama don inji kana kwance da mace na kira,ai sai kaki daga wayar amma don ka cuzguna min sai ka daga, kana ce min wai ka gaji,saboda ka raina min hankali,ya mike don yin abin nan da hausawa suke cewa tabarmar kunya da hauka ake nade ta.ke ki shiga taitayinki,kin tabbata ina tare da wata ne?Kin yarda Allah ya tsaida ke ranar shaida?Tayi shiru ya cigaba da cewa,shikenan tunda da ina neman mata yanzun bani da damar nayi wani dan kuskure sai ace ina tare da mace,to duk yanda zakiyi kiyi,tace haka kace?Shikenan ya dubeta ko da sanda nake yima baki daga min hanakali irin haka ba sai yanzun? Tace gara da lokacin baka gabana kuma kaima baka damu dani ba,ballantana kasan kona damu ko ban damu ba,sannan ko banza lokacin baka boye gaskiyarka, amma yanzun fa?Shikenan kawai tunda kace duk yanda zanyi inyi ni kuma zan nema ma kaina mafita,ta mike ta shige toilet.ya rike kansa tare da yin ajiyar zuciya sannan ya fita.wasa-wasa rigima taki karewa ranar ya ritsata da cewa wallahi shi bazai iya ba,yaya yana matsayin mijinta zata barshi yana walagigi shi in ta ci gaba da wannan halin zai hadata da Umma, tace zanfi son haka domin sai tasan me kakeyi,kila in tayi maka fada kaji nata,ta cigaba da shafa manta,yace to yanzun naji na amshi laifina shikenan me kike so inyi miki ki huce?Ta dubesa alkawari zaka dauka tsakaninka da Allah cewar bazaka sake bin mata ba,yace naji zanyi amma kinsan mutum yace zai dauki alkawari tsakaninsa da Ubangiji ba karamin abu bane,nasan muhimmancin alkawari nidai ina bukatar addu‘arki kuma zanyi kokarin kiyayewa, kenan ka yarda kanayi?Yace a‘a bawai na yarda bane,don dai ranki yayi fari ki daina fushi shiyasa nace miki na yarda,don Allah kinji? Ta tsura masa idanu,yazo ya rungumeta,don Allah beauty in na sake ki mini duk hukuncin da kikeso, tace shikenan ya wuce, duk da haka tana masa komai amma ta kasa sakewa dashi kamar da, yanda take wasa ajikinsa suyi ta wasa ta bashi abinci abaki amma yanzun batayi.
[8:43AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 89ðŸµ
[8:43AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 89ðŸµ