← Book details Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 60

Sashe 43

Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Bayan mun dawo dana yiwa kawu Aminu waya sai gasu sunzo,inna koma zanje, yace to madalla, tsohon nan fa?Tace Modibbo?Yace,eh ,tace shine dai bai jin dadi ban ma samu zuwa ba,sai dai in mun koma yace,to yace Allah yayi muku albarka, tace amin,ta dubi su Asabe tace kuje su bude a fito da kayan nan a shigo dasu,suka ce to ranki ya dade suka fita nan aka soma shigo da kaya ana jibgewa akofar dakin Mamanmu,cikin dakin kuma Bily ta sanarda iyayannta batun zuwansu hajji a bana,in Allah ya yarda,nan suka shiga murna inda su Sakina suka dauki sowa,har mutan gidan suka kara yin tsirmar-tsirmar dama ganin kayan da ake shigowa dasu ya tsinka musu gwiwa,sai kuma sukaji shewa.ikon Allah kenan,Allah mun gode maka cike da farin ciki malam ya fito yana fadin haka.Ladiyo ta tare sa lafiya malam?Yace,hajji zamuje bana nida Fatima, kunji abin Allah ko?Ada ban taba zaton zanje koda filin jirgi ba sai dalilin Bilki, Allah dai ya shiwa yarinyar nan albarka.Ladiyo tace, mu kuma namu sai ka tsine musu ai,yace ke ni yau rana ce ta farin ciki agurina banida lokacinku, sarakaran bakin ciki, komai naku sai kunyi hassada shine dalilin da yasa bakwa yin gaba banzaye kawai.Ya fita yana shaidawa ‘yan uwansa,daga nan kuma ya nufi gurin mahaifiyarsa Gwaggo amarya.ita ko Bily cewa su Sakina tayi su zo sukama hanyar dakunansu nan suka ce wallahi anty cewa fa mukayi zamu kwana,daga nan suka nufi gidan Umman Mansu,suna fitowa direba ya taso tace,a‘a koma abinka da kafa zamuje,haka suka ratsa ta tsakiyar layinsu, jefi-jefi tana ganin wadanda ta sani suna gaisawa,har gidansu Umma. Rungumeta Umma tayi tana cewa Hajia Bily maigadon zinari,saukar yaushe?Bily tace yanzun nan,Umma tace kinsha hanya nan suka zauna aka hau hira, basu fi minti sha biyar ba sai ga sallamar Mansu tayi kiba,Bily tace lallai aminiyata,dibi yanda kikayi kiba haka?Ina yarona ta dauki dady tana cewa,yarona ya girma,ta ajiyesa ta kama hannun Sa‘adatu tana cewa, Mansu dubi yanda mai sunan Umman Yarima ta zama,Mansu dai kallon Bily takeyi tana cewa na zaci zan ganki da ciki? Bily tace kedai zo muje ciki,ai da hira ta kaure basu san ma lokacin da su Sakina suka tafi ba su kam dai suka yi sallar isha‘i,sannan suka nufi gurin Mamanmu sannan ne ta gaisa da Mansu daga nan Mansu ta matsa mata su tafi gidanta ita kanta tana son zuwa gidan Mansu,sai dai fa bata tambayo ba, Mansu tace dauki waya ki kirasa mana.Bily tace,ina ma da numbersa kuwa,ai ni ban taba kiransa awaya ba.Mansu taja tsaki, sannan ta mike taso muje don Allah na kula kema kina bukatar duka,Bily ta mike tana cewa dukan lafiya?Mansu dai tayi gaba tana cewa sai da safe Mamanmu,nan dai Bily ta bita su Asabe kuwa tare da su Sakina suka kwana nan dakin auta.Sai da suka lallaba su dady sukayi bacci sannan suka zube nan kan kafet suka soma labari.Mansu tace wai kawata wane irin zama kukeyi ne ke da Yarima shekara nawa ko bari ko dai kuna shan kwayoyi ne?Bily tace,ko daya yana can gurin matan banza shi yaushe zaizo gare ni bare inyi ciki?In kin gansa gurina to yayi ma ‘yanmatan nasa wulakancin daya iya kuma yana jin girman kan ya basu hakuri to nan fa zaki gansa yazo ni kuma in share shi yayi kidansa yayi rawarsa ya kara gaba. Mansu tace ai duk laifinki ne saboda iskanci mata har cikin gida?Bily tace wallahi harda mata biyu yana kwana,kuma da zaki ce laifina yaya kike son nai masa?Mansu tace, Allah in kin nuna baki son ya shigo miki da mace cikin gida dole ne zai bari,Bily tace Mansu da kinsan halin Yarima ba zaki ce haka ba,shi fa mutum ne dan ra‘ayin kansa,in yasa kansa abu babu wanda ya isa ya hanasa, ga kuruciya shiyasa bana ma shiga shirginsa,Mansu tace aiko dolenki ki shiga shirginsa, shiyasa nace laifinki ne,aganina da ace kinja shi ajikinki kin nuna masa so kin tattalasa,Allah ko zaibi mata sai dai aboye,ta cigaba da cewa ki tuna kefa mace ce kinada kyau,shi kuma mata yafi so,wallahi zaki iya shan kansa,Bily tace nifa wulakanci ne bana so shi da zaki ga yana wani shasshan kamshi.Mansu tace dubeki sai kace wadda batayi karatu ba,dazun fa cewa kikayi ko number dinsa baki da,Bily tace Allah kedai ina da numb dinsa amma ban taba kiransa ba
[6:35AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 72🏵
Chapter 43 · 0% Book details