← Book details Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 60

Sashe 36

Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk suna zaune gaban asalin bokansu,Ladiyo ta gyara zama tace,gaskiya boka duk yanda kace muyi haka mukayi amma duk ba wanda yaci,yanzun da haka suna kasashen turawa ita da mijin. Salame tace sannan shima na maigidan munyi kuma yaci amma tamkar ma mun kara masa masifa ne, Karima tace ga ‘yayanmu nan dake gidajan mazajansu suma mun amsar musu duk abinda ya soma tasiri sai kuma ya tsaya.Boka ya dubesu daya bayan-daya sannan yace,ance muku kullum ake kwana agado?Amma dai kun san ba yau muke tare daku ba ko?Sau nawa ina muku aikin yana ci?Duk sukayi shiru,Ladiyo tace to yanzun yaya za‘ayi? Yace yanda za‘ayi kenan kuje kuyi hakuri danni nan da kuka ganni da zaran mutum yayi min korafin aiki baici ba to aljanu sun daina masa aiki don haka yanzun ku tashi tun kafin su iso keme cikin nan su cire dan su saka miki kwado.ai da gudu suka tattara yanasu-yanasu suka tashi,suna tafe suna jimami har gidan wani malamin, a takaice ranar yini sukayi garari gidan malamai da bokaye.A hanyarsu ta dawowa suna cikin mota ciwon haihuwa ya kamo Ladiyo suka rasa yanda zasuyi,mai mota yayi parking gefen titi yayi ta masifa yana cewa ku karata can nidai ku saukar min daga motata,in banda bala‘in yawo mace kina da ciki wata tara in banda asibiti ina zaki? Amma ke kin fito shegen gantali ai gara ki haihu a titin kila zai zama darasi ga mata masu shegen yawo irinki,su Karima suna cewa,malam don Allah ka barta taji da damuwarta, shi dai ya sauke su yana cewa ku karata dai. Gyaluluwansu suka cire tare da taimakon wata Bayerabiya suka tare ta har ta haihu,saidai ga maza masu saide-saide a gefen titin ga kuma yara sun taru ta haihu da kyar uwar ta biya,sannan suka rufe jinin da kasa suka nado ‘yar agyalan uwar suka nemi shatar mota duk da babu mai sisi cikinsu sai bayan magariba suka zo gida,lokacin malam mamman yana tsaye kofar gida ransa bace yana son yaga ta ina matannan zasu bullo ne? Karima ce da girki tun safe suka ce zasuje gaisuwar mutuwa har yanzun ga yaran duk yinwa ta ishesu,suna ta kuka,Mamanmu ce ma data gama girki ta zuba ma kananan ta soma sa musu su duka to amma bata yi da yawa ba,don bata san sun fita ba sai da bata ji duriyarsu ba,ta idar da sallar magariba kenan tana tasbihi sai kawai ta jiyo muryar maigidan yana ta zazzaga masifa,yana fadin dukku nemi hanyar gidajanku,badai gidana ba tun safe kuna ina?Yau gari ya waye?Da sauri Mama ta fito ko hijabin bata cire ba,sai taji ashe ma akofar gidane ake diramar,don haka sai tayi waje.Karima da Salame sunyi tsuru-tsuru,malam Mamman nata zabga bala‘i,Ladiyo ko tana cikin mota bai ma san ta haihun ba don suna tsayawa yaga sun fito yako hau ruwan bala‘i. Mama ta matso tana cewa,lafiya malam duk makota suna jin muryarka? Yace ba dole aji muryata ba,inna yi fada ace na cika masifa,Allah ya hadani da matsiyatan mata,ace macen arziki ta fita gida tun safe tana gantali ita ba ma‘aikaciya ba,ba ‘yar kasuwa ba,yawo kawai shiga nan fita nan?To duk suyi gida dama nina gaji da halinku. Mama tace a‘a malam ka bari kaji uzurinsu mana. Yace basu da wani uzuri, Salame tace malam wallahi muna da uzuri,dai dai nan mai motan ya karaso gurinsu yana cewa,ku bani kudina ina sauri ne,Karima tace malam kaba mai motar nan dari hudu,wallahi Ladiyo ce ta haihu ahanya dalilin dadewarmu kenan,Allah ya tsareni ai ko kudi zasu kasheni bazan baku ba,ai yanzun don wulakanci a titi ta kware gaba ta haihu? Amma Allah ya isa tsakanina daku.Yayi ciki,Mama tace ina Ladiyon?Suka ce gata nan cikin mota,mai mota yace ku bani kudina sannan ku dauke ta na taimaka muku kuna ta bata min lokaci,gashi motata sai karnin jini Allah dana sani da ban taimaka muku ba.Mama tace to ku sallamesa a fito da ita mana.Salame tace,um babu mai ko taro cikinmu, gida Mamanmu ta koma ta dauko dari biyar taba mai motan,sannan aka fito da Ladiyo,suka taimaka mata zuwa cikin gida.Malam yace shifa su fita don yayi musu saki dai-dai,Mama tace haba malam,menene haka? Yace ba ruwanki,ki koma daki kada ki kuma min magana,su fitar min daga gida kawai.Mama ta wuce daki,Salame kuwa ta nufi sashen Gwoggo da kuka.Ta shaida mata cewa malam ya sakesu, gwoggo ta saki butar dake hannunta ta zabga salati saboda me?Inji Gwaggo amarya,saboda munje gaisuwa Ladiyo ta haihu can.Gwaggo tace muje gidan an kada an raya da malam yace dole ne su bar gidan nan yau,haka nan sai yayyansa suka ce to su dai je gidan asan yanda za‘ayi,Gwaggo tace ta sani ba haka kawai bane anje ne an kau mata da hankalin da daga kan matansa.Ita ko Mamanmu daya shigo dakinta magana ta shiga yi masa akan cewa ya dawo da matansa don ita bazata iya kula da yara kusan ashirin ba,yace sun cika masa ciki ne amma zai dawo dasu wasa-wasa sunfi sati sannan ya yarda suka dawo,maimakon ya zamar musu darasi,a‘a sai suka shiga tunanin yanda zasu dauki fansa acewarsu Mama ce tayi musu asirin da aka sakesu,don haka itama sai an mata sakin babu ma kamar Ladiyo tace ai gara ku nida na tara uban bashi ina lissafin inna haihu zan dan rage gashi yanzun babu batun suna tunda yace ba wani taron da za‘a masa yasa ma jaririnsa suna dole ne na hakura tunda yanzu an dusashe mana haskenmu daga idanunsa,Salame tace ai ko kun hakura ni sai naga bayan shegiyar matar nan da ‘yayanta.

***************************
Umma ta dubi anty Salma tace,ke Yariman ne yace miki yana son Sumayya?Anty Salma tace,a‘a Umma Sumayya din ce wai ashe tana sonsa ta kasa fada ashe ma akansa ne taki sauraron samari.Umma tace,to yanzun ai sai ta sauraresu don kinsan Yarima da yaya ma aka samu yayi wannan auren?Don haka tama nemi mijinta inma da yana sonta baya sonta ba, ai daya yi magana, saboda haka kibar ma wannan zancan,ni na mafi son ya nemo matarsa can wani gurin kamar yanda yayi nan itama sai ta nemi mijinta bana son hadin nan su zo su bata mana zumunci,don Yarima bawai yana da dama bane.Anty Salma tace Umma bada wannan da ba asan asalinta ba ni wallahi matar nan ta Yarima bata min ba. Umma tace, karta miki ai badon ke aka aureta ba,don bata miki ba wata tsiyar ce? Bana ma son ta miki.
[4:48AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 60 🏵

Ta rumtse idanu sannan ta soma balle masa botiran, shi ko fuskarta ya tsurama idanu,xuciyarsa tana fadin,she is beautiful kwadayin lebunanta ya kamashi ya kasa daurewa,hannu yasa ya kamo fuskarta cikin tsananin zumudi ya manna bakinsa cikin nata.Daga nan komai ya cigaba da wakana,Bily dai tamkar gunki ta zamar masa yayinda shi kuma yake duk yanda yaga dama da ita.Bily wanka takeyi tana kuka,ba wai tasha wuya bane kamar wancan karon,duk da dai taji jiki wannan din ma kukan bakin ciki ne ko na menene ita dai bata sani ba,amma wata zuciyar tana gaya mata cewa kukan rashin mai so ne,ita da dai tana son ta san me yasa maza basa sonta?Ta sani Yarima ba don yana sonta suke zaune ba, yama gaya mata kuma lokaci ya kure mata da jin wannan kalmar ta so daga bakin wani tunda tana da miji yanzun kila ita haka Allah yake son ya ganta ma‘ana bai kaddaro ta cikin wadanda zasu samu maza masoya ba.Yarima koda yake kwance cikin bahon wankansa, idanunsa lumshe yana tuno irin halin daya shiga ne lokacin da yake tare da Bily,me yasa yakan fita daga hayyacinsa harma yayi ta surutai,in yana tare da ita?Wanda ko chelen da suke shaye-shaye don nishadinsu shida ita baya samun kansa cikin wannan yanayin,kuma fa wai ma don bada son ran Bilyn bane,in da da son ranta ne zata masa duk abinda su chelen keyi masa yaya zai ji kenan?Tsigar jikinsa ta tashi yarr!A fili yace,kila sai na suma don haka yasa a ransa zaya yi kokari ya gwada yanda zai samu hakan.Ya jima yana tunani kafin daga baya yayi wanka ya fita,yayi mamakin ganin yanda lokaci ya tafi har haka daga yin mantuwa ya dawo dauka shine har kusan awa uku,yayi tsaki kowane lokaci ya bata lokacin sane kan yarinyar nan ce,bai san mutum ya zauna yana tunanin banza ba sai kanta,tun farkon haduwarsu har yau ita kadai ce din dai ke saka sa tunani me yasa?
[4:49AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 64🏵

Yana gaya mata cewa kada ma ta kama cewar yana da aure karta gayama kowa ma azata gaske ne. Chelen tace to yaya kake da ita? Yace kanwata ce bata son ta ganni da ‘yanmata don kinsan addininmu bai yarda ba,tace ai ta yarda ba matarsa bace,tunda ta jima tana zuwa gidan inda matarsa ce tasan da tuntuni zata dauki mataki,yace kin gane ashe.Shi Yarima sam baya so chelen ta kai labarin yana da aure cikin school dinsu,shiyasa yayi haka sam baiyi don ya bata ma Bily rai ba,danne zuciyarsa yayi kawai,ita ko Bily bakin ciki ma ai ba‘a tonawa,ace mijinka ya nuna karuwa ta fika,ko baku son juna ai aure ya wuce wasa,da abin ya isheta da tukuki arai sai ta dauko maganin ciwon zuciya da hawan jini,kai da dukkan wata cuta ma,ta shiga karantawa,wato Alkur‘ani mai girma.Yanzun ta daina zaman dogon tunani,in ranta ya baci Alkur‘ani take dauka sai kaga nan take ta manta da duk wata damuwarta, don Allah kema ki gwada ‘yar uwa,da zaran kin shiga damuwa ki dauko Alkur‘ani ko falaki da nasi kike ta karantawa,sai kinji sanyi aranki in baki manta ba dama shi waraka ne. Yarima ko bayan tafiyar chelen,ya shiga don ya dan watsa ruwa,lokacin sallah ya kusa hankalinsa yana tashe ne,can kasan zuciyarsa tana ta mintsininsa, me yasa zaima beauty haka?Jin damuwa tana son sasa dogon tunani yasashi yin maza ya watsa ruwan, sannan yayi alwala ya fito yana cewa bazai dinga zaman tunani ba,saboda ita amma me yasa kasan zuciyarsa yake mintsininsa? Me yasa zuciyarsa kullum burinta ta ringa kwadaita masa yarinyar?
Chapter 36 · 0% Book details