← Book details Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 60

Sashe 21

Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga Bily itama tuni ta saka damuwarsa gefe ta shiga harkokinta.Takaicinta daya shine yanda har yau ta kasa yakar mafarkinta,don har yau tana mafarkin Yarima.Kara zage damtse tayi gurin addu‘a,Allah ya rabata da mafarkin Yarima,ta tattara komai nata ta barma Allah,ta kuma sha alwashin tabar kara zuwa gurin Modibbo tunda suna da alaka da Yarima,duk da yanda zuciyarta ke son tsohon
Kai ko Faruk sai taji tana jin haushinsa domin tasan dole ne yafi son Yarima da ita,tunda Mamansa da Maman Yarima uwa daya uba daya,wata kusan kuwa ai tafi wata.Wani sashe na zuciyarta ma har yana zargin koma shine ya gaya ma Yarima wacece ita?Amma ta kasa yarda don tasan Faruk bazai mata haka ba. Kawu yayi sallama ya shiga wurin Modibbo,cikin girmamawa ya zauna gaban mahaifin nasa,sannan ya sunkuyar da kai yace,ina yini Modibbo?Lafiya lau,ka dawo lafiya?Yaya kasuwa?Kawu ya amsa da Alhamdulillah.Modibbo yace,to madalla.Ka shiga ciki inka gama harkokinka sai ka fito zan aike ka gidan mai martaba kayo min iso,gobe in muna cikin masu rai zanzo gurinsa.Kawu yace,yanzu bana komai bari naje inna dawo sai na shiga gidan gaba daya.Modibbo yace,to shikenan,in baka gajiba.Amma da kadan huta,kawu yace,ban gaji ba,bari in tafi kawai.Ana shirin tashi daga Fada,kawu ya isa.Ya nemi iso aka shigar dashi Fada.Nan ya isar da sakon Modibbo ya dawo.Mai martaba sam baya son Modibbo yana zuwa da kansa,yafi son ya aiko masa cewa yana nemansa,shiya dauki Modibbo mahaifi ba suruki ba,don haka misalin karfe tara ya fice ta kofar baya inda Magaji ke jiransa cikin mota.Duk gidan babu wanda yasan ya fita,sai ko Magaji da suka fita tare,shima bai san inda zasu je ba,ya dai kirasa awaya yace masa ya amshi mota ya jirasa bakin kofar baya.Sun hau titi sosai,sannan yace Babana gidan Modibbo zamuje,Magaji yana mamakin mai martaba sosai,sam shi bashi da girman kai,sannan duk inda zaije aboye shiya zaba don ya rakashi.Magaji ne ya shiga yayo iso,babu kowa sai Modibbo yana ta jan carbi.Mai martaba ya zauna daura dashi,Modibbo ya mika masa hannu da suyi musabaha kamar koyaushe,mai martaba ya noke hannunsa suka gaisa.Modibbo yace,kai da nace zanzo?Mai martaba yace,Allah gafarta nine yakamata nazo donni danka ne.Modibbo yace,to amma kuma ai kai shugaba ne.Mai martaba yayi murmushi yace,amma Allah gafarta Malam,maganarmu bata shafi mulki ba,don haka in an bar batun mulki an dawo gida ni da ne,kuma duk da nagari dole ne yabi iyayensa Murmushi Modibbo yayi,yasan gaskiya ce mai martaba ya fada.Don haka kai tsaye yaje da fadin dalilin son haduwar tasu game da zancen takwarana ne yace Malam Shehu yazo min da sakamakon binciken dana sa shi.Yaci gaba,Malam Shehu Almajirina ne tunda dadewa,shi dan Zaria ne musamman nasa aka kira minshi awaya na sakasa yayo min bincike menene asalin Bilkisu?Kuma naji komai game da duk wani abu da shari‘a ta nema asali ga mace,sai dai yarinyar ba masu hali bane yace sai muce Alhamdulillah ,don haka sai atashi ‘yan neman aure su tafi.Mai martaba yace,to Alhamdulillah, talauci kam sam ba abu bane da zai hana aure ina son zan tura Fadawa zuwa ga mai martaba sarkin Zaria,daga nan sai su nemi dagacin ko hakimin unguwarsu sannan kuma shi sai ya nemi mahaifinta.Modibbo yace,to,Allah ya shige mana gaba,zamu taya ku da addu‘a.Kwana uku da wannan magana,mai martaba ya tashi Fadawa da sako zuwa Zaria.Sun samu tarba ta karamci irin na Zage-zagin asali.Sannan suka sanar da sakon mai martaba nan mai martaba yaji dadin wannan batu,sannan yasa aka nemo masa dagacin yankin,ya umarcesa daya nemi mai unguwar Ojo suzo fada gobe.Washegari suka amsa kiran sarki,nan yayi musu bayani,sannan akace su nemo Malam Mamman mai rini,suna dawowa mai unguwa yasa akira masa Malam Mamman.Sakon ya samesa lokacin yana zugama Mamanmu rashin mutuncin nasa,yana cewa karuwancin ya isheshi haka,dole yana son Bily ta dawo gida ya gaji,kilama shi yana tafiya mutane suna nunasa bai sani ba.Shiru ta masa yayinda su Kariman da suka zugosa,suka hada dan dandali suna shewar dariya.Cikin haka ne aka kwada sallama,baiji ba yana sababi sai da aka sake sannan ya shuri takalminsa ya nufi hanyar waje,yana cewa ai wannan yarinyar da haihuwarta gara barinta.Yarinya ta balaga ta balage min agida ta zamar min kaya?Daidai nan ya isa kofar gida,ya mika ma dan sakon me unguwa hannu suka gaisa,dan sakon ya shaida masa cewa mai unguwa yana nemansa.Malam Mamman yace,lafiya dai ko?Lafiya lau,yace dai muzo tare.Suka rankaya gidan mai unguwa.Gefen tabarma suka zauna yayi gaisuwa,mai unguwa yace,Malam Mamman ka samu sakona ko? Mamman yace,kwarai,shine ma dalilin zuwana
[8:48AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 34🏵

20-Mai unguwa yace,to nima hakimi ne yayo min aike naje,shine yace lallai muzo tare da kai.Idanun Malam Mamman ya shiga zarewa tare da cewa mai girma hakimi kuma ranka ya dade?Mai unguwa yace ,shi don haka yanzu sai kaje ka shirya mu tafi.Jikin Malam Mamman yayi sanyi,yace cikin in-ina,badai wani abu nayi ba ko?Ranka ya dade nifa ko hakimi ma ban sansa ba.Mai unguwa yace,to ina zaton dai kan ‘yar wajenka ce ko Bilkisu ne sunanta?Sai dai munje kaji saboda shima hakimi ina zaton sakon daga samane,can gurin mai martaba sarki,don haka kaje ka canza tufafi.Jiki yana rawa ya nufo gida,yana tafe yana surutai ni wannan yarinya ta zame min bala‘i,ni in za‘a kasheni banace ga kamannin dagaci ba,amma yau sanadin wannan ‘yar iskar yarinyar gani wai har gaban sarki zanje,ko wane bala‘in ta jono min?Oho!,yanzu haka labarin karuwancin nata ne yaje kunnansu.Daidai nan ya shiga gida yana tsaki,matan suna gindin murhu suka dubesa har suna hada baki,lafiya malam?Yace ina fa lafiya,waccan ‘yar iskar taja min wai yanzun gidan sarki ake nemana.Suka ce,wace?Yace,Bilkisu mana.Mamanmu dake daki ta jiyo,don haka da sauri tayo waje don jin me Bily taja masa?Ta fito daidai sanda yake cewa kurum zataja min fitina,yanzu haka ma sunji labarin gantalin da takeyi ne shine aka kirani ahukunta ni.Ladiyo tace,a‘a karka yarda malam,ai ba kaine ke karuwancin ba itace ko kaje karka yarda acutar dakai.Salame tace,ko ko sunji har yau ba a mata aure ba ba.Karima ko cewa tayi,nidai da zakaji tawa,da ka ki zuwa saboda ina tsoron kadasu daure ka ba da hakkinka ba,in haka ta faru mu aka cuta masu kananan yara.Ladiyo tace hakane,ya shiga dakin Salame yanasa kaya,yana cewa, wa zaiki zuwa kiran sarakai?Ai sai azo da dogarawa akamaka.Daya fito ya kalli gurin da Mamanmu take,ki shirya kayanki,domin inna dawo da wani cin zarafin kema zaki samu naki rabon.Ya fita nan Salame ta yafa mayafi ta shiga sashen Gwoggo tana hawayen gulma,wai anzo daga gidan sarki an tafi da malam saboda Bily,yawon banzan da take yi yaje kunnansu.Budar bakin Gwaggo sai tace,babu kaico,na mayi murna ga bokon nan,ni nasan dama haka za‘ayi.Ta soma masifa da cewa,ni dai abar min dana suzo su kama uwarta don itace ta tsaya mata.Kafin kice haka,labari duk ya kaima sauran sassan,nan da nan gidan ya cika,sassansu Mamanmu suka dungumo inda take zaune bakin gado cikin daki,ta hada kai da gwiwa.Hankalinta atashe,tasan wani sabon sharrinne za‘a kagawa Bily.Masifar Gwaggo ce ta sakata kuka,tana dai ciki bata fito ba,kowa yana ta fadin albarkacin bakinsa,sai tsinuwa tareda zagi suke yiwa Bily wadda bata san hawa ba bata kuma san sauka ba.Suna isa gidan hakimi,babu bata lokaci suka tafi gidan sarki cikin motar hakimin,anyi musu iso suka shiga duk jikin Mamman yayi sanyi,yana dai binsu ne.A zuciyarsa yana Allah ya isa tsakaninsa da Bily.Suka zube sukayi gaisuwa cikin magana irinta manya sarki ya soma bayani,da farko yace ina mahaifin yarinyar?Hakimi ya nuna shi tare da cewa,gashi nan ranka ya dade.Mamman kamar yace bashi bane,sai dai yasan ba‘a katsalandan afada,don haka yayi shiru,sarki ya gabatar da maneman auren Bily,daga masarautar Bauchi.Idanu ya zaro yana kallonsu,nan suka gabatarda bukatarsu,jiki yana rawa Mamman yace,a-an baku.To hakane ai ba komai,hakimi yace,ka nutsu Mamman.Suka bukaci afadi sadaki,Mamman yace,ni dai na bar komai gurinka hakimi,duk yanda kukayi ni me biyayyane,ko sadaka ne ai zan bada ita kunfi karfin wannan ranka shi dade.Nan dai hakimi yace su bada dubu dari,Allah ya sakama abin albarka.Sarki ne ya bada sadakin,yace tasa gudunmuwar.Sun gabatarda kayan na gani ina so,akwati biyar,ga na uwa dana uba,uku-uku ga kuma wani seti can guda hudu,suka soma bayani kansu,wannan sune kayan da zata koma sawa yayin tsareta ga al‘adar gidan sarauta in dan sarki zai auri yarda bata shafi sarauta ba.Ana boye ta na tsawon wata biyu,babu wanda zai ganta sai Yarima,sai ko shakikanta.Sannan zata daina amfani da duk kayanta sai wannan,wayar hannunta za‘a karba abata wannan Yarima ne kawai zai dinga kiranta,sannan tunda an bada sadakinta,ynzu mune ci da shanta.
yanzun mune ci da shanta har ayi auren. Don haka a kiyaye, kuna da gurin boyeta ne ko mu bada gida! Mai martba yace, ni zan bada guri tare da masu mata hidima har zuwa auren. Hakimi ya matso kusa da mallam mamman yace,to sai zancan tukuici, ana fa badawa. Mlm mamman yace. To.To!Ni me zan ba su? Sai dai sadakin. Hakimi yace Aa,sadaki hakkin yarinya ne.kawai sai suka ji sarkin mai adalci yana cewa a rubuta musu check na dubu dari biyu a buga sterm suje su amsa. in takaita,nan dai suka shirga kaya cike da mota sannan aka kwaso da sharadin cewa gobe za azo a tafi da Bilkisu, ko in ce anuna musu gidan Bilki. Kuji wani lamari.suna isa gidan har yanzu cike yake da yan jaje,don bayan yan sassa har makota sun shigo.
sai dai suka ji tsayiwar motoci, sannan sai ga Dogarawa suna shiga da akwatuna, jiki yana bari yasa aka shimfida katuwar tabarma aka soma Jere kaya seti- seti, nan mutane suka shiga kallon- kallo kowa yana son jin Karin bayani. Mlm mamman babu baka sai yake yi. Ya Ciro kudi ya ba Dogarai yana godiya suka tafi suna mishi murna, lallai ya iya haihuwa, sun so suga wannan yar tashi suga ya ya take?
Chapter 21 · 0% Book details