Sashe 40
Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Komai me lokaci yana da iyaka,su Yarima anyi jarabawa cikin nasara an gamata a sa‘a,ya zama cikakken likitan mata gwani,Doctor.Ana gobe za‘a tabbatar musu da zamansu likitoci,su Magaji suka iso tare da mai martaba,da kuma wasu daga cikin yayyansa,tunda Umma ta sanarda Bily zuwan bakin nasu,suka je kasuwa don shirin tarbar bakin,sun kammala komai,sannan bakin suka iso.Su anty Fulera sai ‘yan harare-harare akeyi,Bily dai ta kula da take-takensu amma ta share ita farin cikinta daya, kammala karatun Yarima zata gida taga Mamanta da ‘yan uwanta,ranar rantsar da likitocin rana ce mai mahimmanci gurin Yarima da mahaifinsa guri yayi guri,manyan mutane daga nahiyoyi sun halarta. Yarima shine dalibi mafi kwazo cikin daliban da suka hattama karatun,don haka hukumar ilmi ta kasar ta bashi lamba ta farko data yabo sannan ta bashi dama ya zabi duk kasar da yake so cikin jerin kasashe goma don yin wani course na daban har na tsawon shekara daya ko biyu,wannan nasara da Yarima ya samu tasa shi farin ciki shida masoyansa,sun shirya ‘yar kwarya-kwaryar party shi da abokansa. Can gida kuma suma suna tasu walimar.Mai martaba dai yana can masaukinsa,tun ranar suka so,a nade kaya farin ciki gurin Bily ba‘a magana, a daren ana gobe zasu dawo gida Yarima an samu nutsuwa,tunanin shi daya inya koma gida babu mata kenan, Allah sarki,Ashly yarinyar da suka hadu babu dadewa tana masifar ji dashi, shiyasa ma yake matukar sonta don shi yana son akula dashi,ko bai sallama da kowa ba dole ne yayi sallama da ita,suna hira ne da ‘yan uwansa amma ya mike can gefe ya kirata ya kuma sanar da ita cewa su hadu guri kaza. Ashly irin black american din nan ce,tana da tsawo da kiba,amma kibar ta a mazaunai ne da kuma kirjinta,tana son Yarima musamman data fahimci shi mai sha‘awa ne,tana matsa shi sosai kuma ba tsararsa bace,zata girmesa,kafin yaje gurin ta rigasa,sun lalace son ransu sannan ya tile mata kudi sukayi sallama,kuma ya mata alkawarin indai ya ga da sarari zai mata kwatance tazo Nigeria itama harda kuka,nan Yarima ya kara susucewa danshi yana so yaga mace ta mutu kansa. Sanda ya dawo suna ta hira da Bily,yana shigowa ta kallesa ta kauda kai tasan me yaje yay,haka nan Magaji.Washegari suka hau jirgi sai gida. Abuja suka sauka,Bily tana shakar iskar kasarta sai taji tamkar an sakata cikin gidan aljanna,nan suka hau wani jirgin zuwa Kaduna,Bily taji tamkar ta sauka zaria lokacin da suka dauki hanyar Bauchi. Lifaya sosai aka shirya musu,sunci sun sha ana ta hira ita dai Umma damuwarta rashin ganin Bily da tsini agaba,haka sauran kishiyoyin Umma sai da sukace amare har yau anata amarcin tukunna?Anty Fatima tace,mu bama son wani amarci,‘yaya muke bukata,mun gaji da sai dai aci ayi kashi.Umma tace kadaku matsa mata, haihuwa aita Allah ce,ni damuwata ma ko kiba banga ta kara ba ‘yar tawa. Anty Saliha tace, amma Umma aita murje,dibi yanda fatarta ke sheki,sai kace tarwada?Bily dai tana jinsu,ita dai matsalarta daya tana son ganin Mamanta,zata gwada tambayar Yarima ta gani ko zai barta?Da safe ta shiga gurinsa ta samesa zaune yana kallon(BBC)ta zauna dan kusa dashi tace ina kwana?Ya dubeta dama kin iya gaisuwa?Tace to inna gaishe kane baka amsawa,ya dan taba baki tare da cewa,kina bukatar wani taimako ne?Tace,em dama ina wannan ne ya dubeta kiyi magana bana son kwana-kwana,tace ina son naje naga mahaifiyata ne,yace yaushe?Tace duk sanda kace,yace shikenan kije sai sanda nace din,tace to yaushe? Yace bana son naci ki jirani tukunna,tace shikenan ta mike ta fita.Satin duk bata da sukuni ba ta zuwa sasan shi shima baya nemanta duk da yana bukatarta,jin shiru ne yasa ta sake nemansa taje da dare baya nan da safe zata shiga kenan tazo falonsa na kasa sai gashi ya sauko tayi sauri tace,ina kwana?Ya amsa da lafiya, zai wuce tace gurinka fa nazo,ya tsaya sannan ya juyo yana kallon lebunanta da matsala ne?Maganar zuwa gida kaga tunda nazo ban taba zuwa ba ka dubi tsawon lokacin?Ya soma tafiya da cewa duk sanda kikaga ya dace sai ki sanar dani,tasha gabansa da sauri yau ko gobe,yace fine ya fita ta tsaya shiru ko dai gatse yake mata?Kai takan rasa gane hali irinna Yrm,shi kullum ana tarasa nan yana botsewa data shiga gurin Umma suka gaisa ta sanar da Umma cewa tana son zataje gida don taga mahaifiyarta,kuma ta sanarda Yrm yace ko yau ko gobe,Umma tace sai dai goben don sai an sanarda mai martaba,tace to data shiga dakinta murna harda tsalle,sai kace karamar yarinya.Ta kira Mansu ta shaida mata cewa gobe tana zuwa,ta kira su Maryam da Sakina duk ta sanar dasu,ta kira Mama tace gobe tana hanya,Mama tafi kowa murnar zuwan Bily,saboda gorin da kishiyoyinta suke mata cewa sukeyi tir da wannan ‘yar ta samu daula ta mant da uwarta,gori harda surukarsu Gwoggo amarya,tace inda kwadayi to da wulakanci,an tura yarinya gidan miji gidan sarauta don kwadayi gashi nan kila ma tana can tana wahala,inba haka ba shekara nawa bata zo ba,kamar an saida ita.haka nan ‘yan unguwar akayi ta surutu,wasu ma sai sun hadu a sha‘ani sai kaji sun ce ina amare?Ana can dai,Mama kance um tana can da an dameni batayi aure ba batayi aure ba,yanzun kuma tayi an koma kan bata zuwa indai tana zaune lafiya acikin dakinta ai alhamdulillah, sai kaji mutane ana cewa hakane fa,Mama tana sa tare da cewa insha Allah maigado tazo garin nan sai nace ta shiga duk makotan nan ta gaidasu. Malam ya shigo tace, Malam gobe fa maigado tace tana hanyar zuwa,murmushi ne ya subuce masa cike da fara‘a yace ikon Allah,nidai dama kullum yarinyarnan tana raina,lallai muna da babbar bakuwa,Allah yasa ta iso lafiya,Mama tace amin.Bily daren ranar batayi baccin kirki ba, saboda tsabar murna,tunda duku-duku ta shiga gurin Umma, umman lazimi takeyi don haka gefe ta samu ta zauna bayanta gama suka gaisa,Umma tana murmushi tace,Bily kin kosa kije gida ko? Tayi dariya tare kuma da sunkuyar da kai,Umma tace to kinyi tsaraba ko?Bily tace,sai dai wadda muka yo daga malesia, tace a‘a wannan tayi kadan tunda kila wasu kika gayyade kika sai musu wannan ko ganin gida zaki je,gashi baki taba zuwa ba,sannan gashi kina gidan sarauta,ina Yariman?Tace am yana daki,ta dai fadane don ita yanzun dai bazata ce ga inda yake ba,Umma tace ya dace ma ace tare kuka je dashi,donsu gansa,tunda bai taba zuwa ba
[6:31AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 69ðŸµ
[6:31AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 69ðŸµ