← Book details Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 60

Sashe 34

Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Suka yi dariya taja jakarsa ta kai dakin Yarima sannan tazo ta soma dafa masa taliya,shi kuma ya mike don yin sallah.Suna gun cin abinci ne yake tambayarta shin ko abokina ya canza?Bily bazata iya boyewa Magaji ba,don tasan shi mai gyarawa ne a kowane lokaci,don haka sai tace ya dai canza kila nan gaba,tacigaba Magaji bazan baka aboye ba,ina nadamar zamana da Yarima,munanan halayensa sunyi yawa.Yarima mazinaci ne kuma mashayi.Magaji ya mike tsaye tare da dafa kirjinsa yace,innalillahi wa‘inna ilaihir raji‘un!Me Yarima yake sha?Tace giya.Zufa ta soma tsattsafowa Magaji,yace a ina yake sha? Tace kana duba kowane fridge na gidannan zaka gani.Ya soma dana kitchen,duk jus ya gani sannan ya koma na daki nan ma bai gani ba ya dawo yace,ban gani ba.ta mike ta ciro masa kwalba daya na jus,tace wannan ba ita bace?Magaji yayi ajiyar zuciya sannan yayi murmushi ya mika mata,gashi ki karanta. Zama tayi ta karanta rubutun dake jikin kwalbar tare da ganin nau‘in ‘yayan itatuwan da aka hada jus din dasu,sannan sun rubuta cewa babu giya aciki.Kunya taji kuma ba boye-boye tace,niban san irin wadannan jus din ba,kuma ban karanta ba,amma ai ahaka za‘ace giya ce ko?Magaji yace ga wanda bai sani ba?Ni nasan Yarima baya shan komai na maye,sai dai batun mata yana dan tabawa,kuma zuwa yanzun da kika zo ya dace ace matsayinki na mace kinyi duk yanda zakiyi kin rabasa dasu,tayi murmushi tace Magaji kenan kana yi kamar baka san Yarima ba.Yaushe ya bani darajar yin haka?Ba sai ya maida ni mutum ba sannan zai kula ni,har ma na hana sa abinda yayi niyya?Ni tsoronsa ma nake ji, kai atakaice ma ni nafi karfin wata uku ban gansa da idanuna ba.Yace ba gidan yake kwana ba?Tace anan yake kwana mana, kuma duk ‘yanmatansa nan gidan suke zuwa wai da rashin tsoron Allah irin na Yarima har da mata biyu yake kwana?Shine dalilina na kaura ce ma ganin wannan bakin cikin.Ta soma hawaye,Magaji ka taimake ni Yarima ya sakeni,yanzu haka rabona dana gaisa da mahaifiyata na dade banda kati banda kudi kullum tana raina ni ina nan cikin bakin ciki bazan iya ba.Magaji yace kiyi hakuri wata rana sai labari,gidansu Yarima ba‘a saki inba kin aikata wani mummunan laifi bane kamar zina,Allah ya kiyaye shine za‘ayi saki,yanzun yana sakinki abinda kowa zai dauka kin aikata kenan.Sai dai kiyi hakuri sauki yana nan zuwa bada jimawa ba,wata rana sai kince ma Yarima ya fita sannan zai fita.Magaji ya fada cike da tsokana tace tabdijam,Yarima ne mace zata juyashi?Lallai kuwa kace wata rana jaki zaiyi kaho.Magaji yayi ‘yar dariya sannan yace,ai gara kema da tawa matsalar. Ta dubesa me ya sameka?Yace ai kin san Sumayya ko?Kanwar su Faruk mijin kawarki? Tace na santa,yace ita nake so tamkar in mutu, ita kuma bata sona wani daban take so,ta gaya min na kasa hakuri.Bily ta tuno hirar dataji Sumayya suna yi lokacin da Mansu ta haihu,sai tayi murmushi tace,nasan Sumayya Yarima take so.Magaji yace yaya akayi kika sani?Tace sun taba hirar a gabana ita da ‘yan uwanta.Magaji yace,to yanzu na rasa inda zansa kaina,kwanaki ta zo Bauchi gidan anty Salma ta sauka in naje bata fitowa,sai dai Momy ‘yar gidan Salman ce ke fitowa tana bani hakuri.Bily tace, ni dai nawa ganin kayi ta addu‘a,amma ka barta zaifi inko kaci gaba da naci zaka yi ta shan wulakanci,don ko na lura tayi zurfi a son Yarima. Shiru Magaji yayi yana auna yanda za‘ayi ya rabu da ita,shin wane hali zai shiga?Yace to zan kwatanta, kuma a nata gefen ma bazata samu abinda take so ba,don Yarima bashi da ra‘ayin aje mace biyu.Bily tace ko ma ta nace ta auresa me zata tsinta gidan Yarima in banda bakin ciki?Magaji yace ai kuma baki sani ba,ita tunda tana sonsa zatayi duk yanda zata samo kansa,kinsan namiji shi tamkar yarone wani sa‘in ballantana Yarima mai son matan tsiya, shi yasa nace kema inda zaki rike masa wuta tsaf zaki samo sa.Bily tace ba irinsu Yarima bane,shifa wani irin hali garesa duk da ba dogon zama nayi dashi ba na lura da halayyarsa,sannan ko ‘yanmatansa kar kaga yanda yake gara su. Magaji yace Yarima kenan,ni dai hakuri kurum zan baki wata rana komai zai canza,tace to Allah ya kawo mana sauyi na alkairi,yace amin Yarima ya shigo gidan kusan biyar na yamma kamar cikin mafarki yaga Magaji,cikin dariya yace,waton ni har yau ba za‘a daina min zuwan bazata ba ko?Magaji yace sai ranar da ka soma hankali,Yarima yace na gode.Ya shiga dakinsa bayan sunyi sallar isha‘i ne kusan karfe takwas saura Yarima da Magaji suna zaune a wani gurin shakatawa hasken fitilu tamkar rana kowa yana abinda yake so mata kuwa suna ta shawagi ko Yarima zai taya amma yaki ko da kallonsu.Magaji ya dubi Yarima yace,abin na bani mamaki,na me fa?Inji Yarima,yana magana yana danna waya.Yanda mata ko ina ka shiga suke sonka kamar kafi sauran maza.Yarima yayi murmushi to kai me ka gani?Shine ai nake son jin dalili,Yarima yace dalilin kenan, nima ina sonsu. Magaji yace to ai ban gani a goshinka an rubuta Yarima mai son mata ba,sannan in kun hadu bakai ne ke kallonsu ba,sune ke kallonka. Yarima dariya ce sosai ta rike shi yace wannan daga Allah ne,Magaji shima ya dara,sannan yace muyi zancan daya kawo ni garin nan.Yarima ya gyara zama,ina jinka magaji yaci gaba da cewa,Umma ta damu nata ganin ba kwa zaman lafiya da matarka, dalilinta shine duk sanda ta bugo waya ka dauka sai kace kana makaranta in kuma Bily ta kira sai tace ka fita in ko da daddare ne sai kace tayi bacci,shine tace inzo in duba,shi ko mai martaba da bai san abinda ke faruwa ba,yace ne in har tana da matsala to ka kawo ta gida a kula da ita,kadai gane matsalar ko?In baka gane ba yana nufin ciki.Yarima yayi dariya sannan yace,old man kenan,shi yanzun har yana sa ran zan haihu nan kusa?Ya taba baki gami da girgiza kai dubeni fa Magaji am still young,just 24yrs,sannan ace ina da yaro haba mana,Magaji yace to batun Umma fa tana son sanin kalar zaman da kuke yi,yace ka samu matar gidan mana ba kuna shiri ba,nasan zata gaya maka.Magaji yace,tsoronka ya hanata fitowa,sannan abubuwan da kakeyi sun saba ma shari‘a har cikin gida kake shiga da matan banza?Yarima yace ok ta gaya maka kenan? Eh.Inji Magaji, gaskiya ka canza tsari,Yarima yace nidai kace ma Umma muna zaman lafiya shikenan.
[4:46AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 59 🏵
Chapter 34 · 0% Book details