Sashe 41
Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Bily tace to sai dai inya shigo ki masa magana kiji,Jakadiya ta shigo da sallama,sannan ta zauna ta gaida Umma suka gaisa da Bily,Umma tace Jakadiya a duba cikin store din nan afito min da bandiran zannuwa da kuma shaddodi,tace to ranki ya dade,zamu sha sababbin dinkuna kenan?Umma tace a‘a ba naku bane,Bily ce zata ziyarci mahaifanta. Jakadiya tace, a lallai gimbiya yau sai murna,Umma tace da Yariman ya shigo ai da kunje kuyi ma mai martaba sallama,kafin ta rufe baki sai ga dan halak din nan shikenan ma kuje ta yiwa mai martaba sallama kaima kuma ya dace ace kaje ka gaida surukan naka. Yarima ya dan ya mutsa fuska sannan yace gaskiya sai wani lokaci Umma,don yanzu ina Busy na shirye shiryen Zan je wani course wanda muke matsalarsa anan Nigeria ma‘ana in samu wani horo game da wata cuta wadda babu likitocinta sosai anan gida,Umma tace um Allah ya taimaka,amma ka sallame ta da tsara ba ko?Yace to ai batace min zatayi tsaraba ba,Umma tace to ni nace maka, yanzun ku shiga gurin mai martaba ta masa sallama. Mai martaba yaji dadin wannan ziyarar da zataje, sannan yace ki sanarda mahaifanki duk su biyun zasuje aikin hajji bana,ta shiga godiya,Yarima yana tayata mai martaba yace, babu komai wannan kyautar ya kamata ace tuntuni akayita, kasancewar basa kasar sai abin ya kwanta masa da murnarta take sanarda Umma tana godiya tayi tare da ce ma Yarima babana kadai ji kunya kaine ya dace ace kayi wa surukanka wannan kyautar,Yarima ya mike tare da cewa Umma bari nayi wani aiki cikin computer.Ya fita Umma tace kace dai bari ka gudu baka son fadan gaskiya. Bily tayi shiri sosai ga tsaraba Yarima ko kudi ya zube mata sababbi dal ‘yan dari bibbiyu,‘yan naira dari,‘yan dari biyar zuwa dubu daya,kasa magana tayi ta tsaya kallonsa,yace nace ne ki dauki yanda zai isheki tace ni nafi son ka bani da kanka,yace ni kuma nafi son ki dauka don kina sa Umma tana daukana marowaci,baki tambayeni abu ba yaya zanyi in san kina da bukata?Tace to naga karatu kakeyi shiyasa banason matsa maka, yace wannan ba hujja bace,tunda baki taba ganin don ina dan makaranta yau nace wayyo yaya zanyi bani da kudi ba. Don haka dauka in kika dauka duka ma ba matsala,ya juya zai fita tace,to bari na dauka sai ka wuce dashi cikin kowane dauri ta dauki daya,sannan tayi godiya yace a‘a ki gode ma Allah ya dauki jakarsa ya fita. misalin karfe sha daya su Bily sun dauko hanya ga tsaraba mota guda,farin ciki gurin Bily karki tona yau za‘a ga Mamanmu.Ita ko Mamanmu ba zato sai ga Maryam daga kaduna zuwa jimawa kuma ba sai ga Sakina ba,suna cikin gaggaisawa ne sai ga malam da kaji guda shidda yankakku,yace Fatima gashi ku tashi kuyi azama ku gyarama bakin nan me da me za‘a siyo na cefane?Su Sakina suka fito suna gaidasa tare da cewa,ai ko bari muzo mu kama aikin,cikin fara‘a yake cewa duk yanzu kuke tafe?Yaci gaba sannunku da zuwa,Allah ya shi muku albarka,cikin mamaki suka ce amin,yace kun samu labarin zuwan ‘yar uwar taku ne ko? Suka ce ta kiramu ne ta shaida mana yace to to madalla tunda gaku sai kuyi azama ku shirya musu abinci ko?Ya miko dubu biyu gashi sai kuyi cefane,ya zamana dai an shirya musu girkin mai kyau kan lokaci,suka ce to baba.Mamanmu dai ranta kar,yana tafiya sukace oh abin mamaki yanzu baba kara sonmu yakeyi dibi yanda yake ta rawar jiki,Mamanmu tace to ku addu‘a banza ce ‘yayan nan?Kuna fa gani babu dare babu rana ko yaushe cikin du‘a‘i nake.Sakina tace,kuma muma munayi bamu zauna ba,nan suka hau aiki,auta ma ta dawo daga aike itama nan ta hau aikin.Su Ladiyo ko sun ga shigowar malam da kaji don haka suka kafa dandali suka soma tsegumin nasu,karima tace tunda nake gidan nan ban taba ganin malam yazo da ko kaza guda yace a soya ba,sai yau. kodan su Sakina ne ya siyo?Ladiyo tace kince kaza ko kwai ya taba kawowa?Don haka kan kajin nan sai anyi tsiya,inma dansu Sakina ya sawo mu fa da ‘yayanmu suke zuwa me ya taba kawowa suka dafa?Salame tace,bana zaton donsu Sakina ya kawo nafi tunanin wani sabon wulakancin za‘a fara mana don ko ni ashirye nake dan ko daidai za‘a raba kajin nan,nan dai suka kasa suka tsare kowacce tana cika tana batsewa.
[6:32AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 70ðŸµ
[6:32AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 70ðŸµ