← Book details Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 60

Sashe 42

Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Su ko su Sakina suna ta aikinsu girka wancan dafa wannan soya wannan har suka gama suka share gidan suka gyare dakin auta wato dakin Bily na da suka cire gadon suka shimfida babbar tabarma,suka jera abincin ciki.misalin karfe uku sai gasu Bily sun shigo birnin zazzau,jinta take tamkar anyo mata wahayi cewa an mata gafara.Sai da suka bita masarautar zazzau sannan suka wuto,ita daya ce sai kuyangi biyu Atika da Asabe,dayar motar kuwa dogarawa ne sai tsaraba,tunda suka shigo cikin unguwarsu take ta kalle-kalle,unguwar tana nan yanda ta santa,wasu gidajen sun kara lalacewa, wasu gidajan kuma sun samu gyara,daidai kofar gidansu motoci ne suka tsaya gidansu shima ya kara lalacewa sai dai duk da haka an share kofar gidan tas, yayinda mahaifinta da kannansa da kuma shi kansa mahaifinnata duk suna kofar gida suna ta alwala,nan suka tari su Bily da dogarawa aka bude ma Bily mota ta fito,subhanallahi,ganinta sukayi tamkar ba mutum ba don kyau,ta kara fari fatarta shar,duk da bata kara kiba ba daka ganta kaga hutu,durkusawa tayi tana gaida iyayanta suma kuyanginta haka sukayi, Asabe tana rike da jakarta suka shiga cikin gida, matan gidan suna nan gurin da suke suna sakawa suna kwancewa game da girkin da suka ga anyi an turasa cikin dakin auta,yanzun sun karkata tunaninsu kan cewa kila mazansu ne zasu zo shine akayi wannan girki,Karima na cewa wallahi bari zamuyi sai mazajan sunzo suna cikin cin abincin muje gurin Fatimar mu tada masifa muce sai an bamu hakkinmu, kunga mun kunyata ta gaban surukai.Ladiyo tace don surukai ba sufi surukai ba,namu surukan ko fiya wata ya taba sai musu?Sallamar Bily da kuyanginta ne ta tsaidasu daga hirar da sukeyi,cike da doki ta shigo tana cewa,sannunku Gwaggo,mamaki hade da firgici suka hanasu magana,bata kula ba ita dai burinta tayi arba da Mamanmu,tun kafin ta isa dakin ta soma kiran Mamanmu!Mamanmu!!Su Sakina ne su uku suka fito da gudu suka rungumeta suna oyoyo anty Bilki.Nan take hawayen farin ciki suka soma zubo mata. Mama tana zaune abakin gado cike da fara‘a,Bily taje ta zube jikinta Mamanmu tace menene haka?Nan suka zauna aka shiga gaggaisawa,su Asabe ma suka gaishe su daga nan sai dakin auta,nan suka zube suna cin abinci.Dogarawa kuwa sun wuce sallah ne tare da su malam ,suna dawowa yasa suka shiga dakin Sani,nan kofar gida ya shiga ciki ya amso musu nasu girkin.Nan kuma jikinsu Ladiyo yayi sanyi,sunma rasa me zasu tattauna ne akan wadannan mutanan. Mama ta kira auta tazo tace amso kwanukansu Ladiyo azuba musu mana,su Sakina ne da gaddama tun dazun ina cewa su zuba musu suna cewa baza‘a basu ba,auta ta samesu jugun-jugun tace,Mamanmu tace ku bada kwanuka asa muku abinci.Salame ce kurum tayi karfin halin nuna mata kwandon kwanukan ta dauka taje ta kawo musu ta aje su dai suna nan yadda suke.Bily ko bayan sunci sun sha sunyi sallah, sannan tace Mamanmu bari naje gidan Umman Mansu.tace to ki shiga sauran sasan gidannan ku gaisa,duk da nasan sunji kinzo,amma Gwaggon sasa ce kawai ta shigo wajan nan, sannan duk makotan nan ki shiga ku gaisa,tace kash!Gashi kuma ban tambaya ba,amma zan masa waya ko gobe ne sai na shisshiga tare da su Sakina da kuma kuyanginta suka nufi sasan,Asabe na rike da jakarta yayinda Atika take rike da wayoyinta kafinsu wuce sai data shiga dakunan su Gwaggo ladiyo suka gaisa, dukkansu jiki babu laka yaransu kuwa sai kallonta sukeyi nan tace,Asabe ban jakar nan ta ciri bandir din ‘yan dari bibbiyu ta mika ma auta,gashi ki raba ma yarannan sunsha alawa.Nan ko suka yance ta suna Asma‘u ni baki bani ba,iyayan suna lekowa suka gani nan kowa ta soma raya abinda zatayi da na ‘yayanta in sun kawo.Ta babban sasa suka fara inda gayyar gidan take,suna ko tsakar gida suna ta labarin zuwanna Bily yaran gidan suna ta bada labarin zuwanta suna cewa taci gayu ga wasu hadaddun motoci masu burgewa,kai kunga masu tsaronta sun rike wasu manyan bulalai, sallamarsu ce ta katse Mairo lokacin da take cewa,uwarsu yau sai ji da kai.Bily ta shigo tare da gayyarta,daki-daki tabi kowa suka gaisa yayinda Asma‘u ta shiga rabawa yaran dari bibbiyun.
Mansu ta kira wayarta, Atika ta miko mata wayar tare da cewa,ranki ya dade an kiraki.Ta amsa ta duba sunan Mansu data gani ne duk ta rude tana cewa mutuniyata kin iso ne?Tace mun kusa na jira dady ne ya taso daga islamiya, tace a‘a aminiyata kina son tafiyar dare,sai kin iso tawan,ki wuce gidan Umma don can zan nufa,tace to sai na karaso,amma fa gidana zaki kwana,ban tambayo ba.Cikin dariya Mansu tace yayi kyau,inna iso aida kawai waya akira itama cikin dariya tace,sai kin iso din,ta kashe ta mikawa Atika,sannan suka cigaba da gaisawa,sai kallonta sukeyi ganinsu salo take musu da iyayi gami kuma da yanga,don haka tana fita suka hau kwatanta yanda take magana.Gurin Gwaggo sasa suka shiga,sun gaisa cikin barkwanci take cewa ina angon namu,shi ba zaizo ba?Bily tace,zaizo yanzun aiki ne yayi masa yawa,daga nan sai gurin kakarsu,wadda tayi wani kici-kici da rai suka shiga suka gaisa,sannan ta soma cewa ke kuma sai yanzu kika ga damar zuwa garin,ance miki aure hauka ne,don kinyi aure shikenan sai ki manta da batun iyaye?Ba‘a tamu kakanni,to da mijin naki kuka zo ko?Tace a‘a mu kadai muka zo shi yana aiki ne,Gwaggo ta turo baki tare da cewa,um ba wani aiki shi dai yace bazai iya zuwa gidan talakawa ba,kila ma ke kanki ba‘a bakin komai kike agurinsa ba,banda haka ace aure shekara nawa amma iyaye ace in mijinki ya gansu bazai sheda su ba?Bily ta mike zata fita,to kin fita mana tunda na dauko batun gaskiya,Bily tace ba haka bane,kwata-kwata yaushe ne ma muka dawo kasar, ai zaizo ne.Gwaggo tace kada ma Allah yasa yazo,wannan ruwansa ne.Sakina ta mike zo muje kinji anty,tunda dai kina zamanki lafia da mijinki kada ma yazo din,Gwaggo tace to shugaban marasa kunya, naci ubanki yanzun ni sa‘arki ce da zaki gaya min magana?Nan dai suka fice suka barta. Bayan sun shiga ko‘ina sai kuma suka koma gida inda malam ya samesu dakin Mama sai sannan suka gaisa yace yaya me gidan naki?Yaya iyayan nasa duk dai kuna lafia ko?Tace lafia lau,to yaya gurin Umma fa?Wato kakarta Umman Mamanmu, tace suna nan lafia
[6:34AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 71🏵
Chapter 42 · 0% Book details