Sashe 23
Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Su ko a nan zariya, Abba ya tabbatar ma da Mamanmu cewa batun aure gaskiya ne haka ne. Ya kara kwantar mata da hankali su da Umman mansura. Sun tafi kan cewa sai gobe in Bilkisu tazo zai zo a fito da kaya a duba.
***************************
Wayarsa ta soma ruri,Chelen ta mike ta dauko masa wayar,yana ganin number Magaji yace,Allah dai yasa lafiya?Ya daga sun gaisa sannan Magaji yace,mai martaba ne yace a tambayeka yaushe zaku samu hutu?Yayi shiru,sannan yace,sai nan da sati kila bakwai,yace ok,zan gaya masa.Yarima yace,lafiya Magaji?I think so.Yarima yace,naso ma nayi hutuna anan.Magaji yace,ok,ka iya yin waya ka gaya masa.Kai fa,bazaka fada ba?Inji Yarima.Magaji yace,No.Ya kashe wayar tare da cewa kada ka fada din,ni zan masa waya.Chelen ta matso kusa tana lasar kirjinsa da yayi laf da suma,tace tana son ya koya mata Hausa tana son yaren,yace bashi da time,kuma shima ba iyata yayi sosai ba,don shima Hausa fulani ne.Idanu ta tsura masa tana gaya masa cewa bazata gaji da gaya masa cewa yana da kyau ba tace shiyasa take kara son sa harma takan kirasa da One in town.Shi ko ce mata yayi yana sonta ne kawai irin na sha‘awa,yace shi fa bai ma gama yarda cewa akwai wata soyayya ta No one but you ba.Shiru tayi don tasan yana nufin abinda ya gaya mata ne,kuma ya jima yana gaya mata haka,tasan bazata taba tursasa zuciyarsa ta so taba,kuma tasha yin fushi dashi,sai ya share ta sai dai ta dawo da kanta don shi bai iya lallashin mace duk da yanda takai da ji da kanta.Shiyasa kawai ta hakura da yin fushi dashi. Sun iso zaria misalin sha biyu,kai tsaye gidansu Mansu suka nufa,sun iske Umma tana shirin fita.Abba kuma ya dan fita shima,tace su zauna tana zuwa,Bily tace bari ta leka gida Umma tace a‘a su dai jira gidansu Maman ta nufa,ta samu Mamman a dakin yace,yauwa Hajiya,shigo kinji fama nake da baiwar Allah nan za‘a kawo kayan nan dakin tayi wa ‘yan uwanta waya suzo saboda mutanan nan zasu zo ne su kaita gidan ajiya,an jima kamar yanda nayi muku bayani jiya,duk taki ta bani hadin kai. Umma tace yanzu dai gata nan sun iso suna gidanmu,bari inyiwa Mansu waya ince suzo nan din ko dan tasan halin da ake ciki?Mama tace nima damuwata kenan,gaskiya in maigado bata son abin nan nima bazan so sa ba,dan fari ba mahaukaci bane,koda nake kauda kai kanta ba don bana sonta bane,ina dai kara ne,wulakancin dakayi ta mata cikin gidannan,ko tsinto ta akayi ba‘a mata haka ba,shikenan haka rayuwarta zata zama cikin bakin ciki.Nan bata huta ba kuma tayi auren kudi can ma taje taci gaba da fuskantar wulakanci?Sam bazan lamunta ba,yaja tsaki ai kinji ki da wani zance,ba‘a tuna abinda ya riga ya wuce,batun aji ra‘ayinta wannan ba dole bane tunda ko ashari‘a mune masu zaba mata miji.Mamanmu ta kalli Umman Mansu tace,kirasu dai muji zabinta shine nawa nina san wahalar da nasha kan ‘yayana.Bily ta rasa dalilin dayasa suna nufowa gidansu taji gabanta yana ta faduwa,ta dubi Mansu tace,ko dai wani abu ne ya samu Mamanmu?Mansu tace,me kika gani?Ta kama hannu Mansu ta saka akirjinta tace kinji fa kirjina.Faruk yace,ba komai insha Allah.Suna shiga da sauri ta nufi dakinsu,ganin Mama zaune yasa tayi ajiyar zuciya har duk ‘yan dakin suka dubeta,ganin Mama hankalinta ya kwanta,sai dai tasan da magana don banza Baba ba zaizo ya rashe haka ba.Ta shiga ta zauna kusa da Maman,tace Mamanmu har naji dadi dana ganki lafiya domin na zata wani abu ne ya sameki.Umma tayi ‘yar dariya tace,‘yar Mama kenan Mama kuwa cewa tayi lafiya lau maigado.Su Mansu suka shigo,Bily ta kara shimfida wata tabarmar,sannan aka shiga gaisawa,ta gaida Baba wanda zuciyarsa ta tafi ga tunanin yanda ‘yartasa ta nuna halin ko in kula dashi yau ne kurum abin ya fara masa ciwo,don da baya ma so ta nuna ta damu dashi Bayan gaishe-gaishe,Umman Mansu ta dubi Bily tace,kin san Yarima?Gaban Bily ya fadi,ko dai yasa anci ma iyayanta zarafi ne?Ta tambayi kanta,Umma ta katseta kin sansa nace?Bily ta girgixa kai alamun a‘a,tare da cewa ni sam bansansa ba.Yace nayi masa wani abu ne?Umma tace,a‘a sannan ta dubi Malam Mamman tace,malam bani kudin nan.Jiki yana rawa ya ciro ya miko mata,ta amsa sannan ta aje agabanta.Wannan sadakinki ne,Bily ta zaro idanu tare da dafa kirji,Umma taci gaba ga kaya can yanzun za‘a shigo dasu na zance,bikin bazai fi wata biyu da sati daya ba,me kika ce? A rude Bily ta juya ta kalli Mamanmu,sannan ta fada kan Maman tare da fashewa da kuka,tana cewa Mamanmu menene zabinki?Ki fada min zabinki shine nawa.Amma ina so ku sani Yarima zai aure ni ne ba domin yana sona ba,sai domin ya idar da wani nufi nasa na cin zarafina.Malam yace,ke dai kawai kice kinfi son kici gaba da zama agari babu aure,mutane suna zagina,amma ina kika san Yariman da har zaki wani ce yayi ne don yaci zarafinki mutumin da aka ce yana kasashen Turawa?Mama tace,tashi ki share hawayenki,in har ba kya son sa babu matsi,don ba akan kowa kike ba.Malam ya fita fuu yana cewa,ni dai ya rage naku.Uba ke bada aure kuma na bada ta.Sadaki kuma gashi nan a hannunku,in zaku ja da sarakuna ne bismillah.Ya sake lekowa,kada ku manta yau zasu zo su kaita su adana,sai ku shirya abin ce musu in sunzo ni kunga tafiyata,ya shuri takalmansa yayi waje.Umma ta dubi Bily dake kuka Mama nayi,ta waiga gurinsu Mansu inda sukayi shiru tamkar ruwa ya cinyesu,sai Mansu dake kuka,tace ku tashi kuje can gidanmu,ke Mansu har kai Faruk ku bata shawarar data dace,sai mu saurari hukuncin Ubangiji.Mansu ta kama Bily suka fita suna kuka,Faruk yana cewa suyi shiru kada su shiga cikin jama‘a da kuka waton awaje in sun fita.
[4:01AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 42ðŸµ