← Book details Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 60

Sashe 22

Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi ko nan jama'a suka yo kanshi, uwarshi ta soma da cewa mamman me ka je yi gidan sarki, wannan kayan fa? Cike da doki yace, Goggo ai arziki ne ya kira ni. Ya shiga raba idon ina zai gano Mamanmu cikin matan dake gurin amma bai ganta ba, sai yace INA Fatima ne? Fatima ki zo ga ikon Allah. Tana tsaye daga kofar dakinta amma bata ko kalle shi ba. Ya ce Goggo daga Masarautar Bauchi ake son Bilkisu. Yasa hannu cikin aljihu,ga sadakinta dubu Dari cif haka ya dinga nuna komai yana washe baki jiki yana rawa sai kace a wasan kwaikwayo,

Makota suna ta sambarka yayinda matan gidan suka shiga zare idanu.gwaggo kuwa ko kunya, murna ta shiga yi tana cewa lallai mun haye, sai godiya. Karima tace, ka ko ji da kyau? Salame tace shi ne dai anya ma kuwa zancan nan gaskiya ne? Ladiyo kam kasa magana tayi.
[8:48AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 35🏵

Mamanmu cewa tayi.
Mlm gaskiya ban yarda da wannan zancan ba,in dai ka saida ita ne ka sanar dani, don nasan dama neman yanda zaka rabu da ita ka ke yi, don haka ni bana neman kai da ita,haka kawai bata ga mutum ba bai ganta ba ace an biya sadakin ta naira dubu dari? To ban yarda ba ka ji na ma gaya maka tun wuri ka maida musu kudinsu.

Ya zaburo ke Fatima ahir dinki, 'yarki CE ko ko 'yata? Dama ina neman wanda zan ba na rasa sai kuma gashi an zo nema har gida? Daina wannan zance, to ni ina ruwana da wani suga juna? In anyi auren sun ga junan. Gwaggo tace, kai barta me kashin tsiya,in bata yarda ba fasawa za'ayi? Kwaso kayan ina yara kai Ku kira almajirai,. Sukai can sassan gwaggo amarya, ita kuwa gwaggon sasa cewa tayi, haba Amarya komai fa yana son bincike, Ku bari a bincika a ga wanene duniya fa ta lalace, da masifa gwaggo Amarya tace, ke rufe min baki bana son bakin ciki, idan jikarki ce ai ba za ki ce ayi bincike ba, binciken banza? Allah ma ya hana bincike. Gwaggo sasa tace Allah sarki, ni na San in dai mutumin kirki ne ni na ma fiki murna, kema ganin kudi ne ya gama zagin yar da uwarta? Tasa kai ta fita a sasan,
Mamanmu tace, lallai yanzu ne kasan yarka ko?Ni dai naga yanda za ayi wannan aure.Yace,Oho kya ja da sarakai,danni na riga na amshi sadaki,gara ma kiyi mata waya tazo don gobe zasu zo su tafi da ita.Salame tace,to ko dai har an daura auren ne?Ya fita yana cewa,ke kuma ina ruwanki? Sarakan bakin ciki! Salame tace,ai yau kuma mune yan bakin ciki.?Yace,eh ku ne mana.tamkar wani zautacce ya fita yana cewa,bari in kira yara su kwashe kayan sukai sasanki gwaggo,kada cikin dare a kunna musu wuta.mutane duk suka tafi suna cewa,ko dai mutumin nan ya saida yarsa ne,tunda dama ba sonta yake yi ba?Wasu kuma suna cewa,Aa gaske ne zai aurar da ita ne ga sarakuna don yaga kudi,kilan dai tsoho ne mijin su ko su gwaggo karima da salame da ladiyo dakin ladiyo suka shige suna jajanta ma juna tare da neman mafita. Ladiyo tace,ni duk ji nake yi ma duk zazzabi ya rufe ni, wato mlman nan kudinmu suka yi taci basa komai?Karima tace A'a dan yifa aiki yayi, tunda ai babu saurayin da ke kula tan kamar yanda muka bukata Amma sai dai muce yanzu dai aikin ya baci an samu akasi,ai bamu makaraba,sai muje a wargaza al'amarin.Salame tace. To ko cikon kudin nan ne da bamu bashi ba yaki mana aikin?Nan take suka yarda cewa haka ne,kuma suka yanke shawarar cewa zasu je goben nan. Dan ma kada su fita yau nd a gane dama gashi lokaci daya mlm ya canza har dayi musu habaici.ta ajiye hijabin sannan ta koma ta zauna tunani yasha kanta.Ta rasa wa zata tunkara.Zaraf ta mike tace bari naje gidan Umman mansura. Mamanmu tayi sallama a gidan,ta shigo daidai sanda umman mansura ta ajiye hijabinta tare da amsawa.ta fito taga mamanmu,tace,Aa dama ke ce?Shigo nima yanzun nan nake cewa kwana biyu ba mu gaisa ba,da safe in zan je aiki zan biya.Mamanmu tace,uhum!Ke dai bari, nima yanzun zuwa nayi ki kira min maigado,kira min lambarta.Umman mansura tace,lafiya? Mama tace,ina fa lfy, babansu ne da rikicinshi kin dai san halinshi, wannan karon kuma dazun fa ina zaune da rana ya same ni cikin daki,wai shi ya gaji da ganin maigado tana yawon karuwanci Yarinya ta zama annoba,menene wanene?Ta inda yake shiga bata nan yake fita ba.Can aka yi sallama dashi yana dawowa kuma sai cewa yayi in hada kayana,gashi nan an aiko nemanshi daga gidan sarki,wai suma sun ji labarin gantalin da maigado take yi. Yana dawowa zanga cin zarafi.to in dai takaita miki umman mansura, yana dawowa sai gashi da kaya niki-niki da kudin masu yawa wai sadakin maigado ne, akwatuna kashi-kashi, wlh ni sai ma tsoro ya kama ni,na soma tunanin ko dai ya saida ta ne tunda nasan baya kaunarta?Umman mansura tace,ikon Allah to a ina ya samo mata mijin?Mamanmu tace. Oho,ni ko sauraron shi ma ban yi ba,kila ma sun daura auren ne don naji yana cewa wai gobe zasu zo su tafi da ita. Umma tace,Ikon Allah. Ina zuwa bari in kira Abban su mansura muje mu same shi a ji kan zancen.amma ai ba akira Bilkisu yanzun ba a ruda ta,gashi kin san ta bata iya rudewa ba.yana gida ko?Mamanmu tace, yana nan kofar gida ya tara makota da yan uwansa mazan sai lbrin yake basu,sai ka ce wani zararre.. Umma tace,kije gida in anyi sallar isha'i zamu zo yanzun insha Allah. Mlm Mamman ko ana idar da sallar isha'i ya shigo dakin mamanmu tana zaune kan abin sallah,tayi tagumi ya zauna yana 'yar dariya. Abin al'ajabi wai yau malam ne yake min fara'a cikin zuciyar mama kenan take sakawa.yace fatima cire tagumi ai kin daina tagumi,ki kwantar da hankalinki muyi magana,sallamar umman mansura ne ya tsaida shi ya amsa tare da cewa,ku shigo.Tace yauwa kana ciki ba? Nima ni da maigidan ne dama gurinka muka zo, yace bismillah ku shigo, shimfida tabarma fatima. Umma tace bari in kira shi to. Sun zauna bayan gaishe-gaishe,sannan Abbansu mansura ya soma da cewa,mlm mamman,mai dakinka ce tazo mana da wani batu na game da yarinyar nan Bilkisu,shin me yake faruwa ne?Mlm mamman ya gyara zama,ya shiga rattafo musu yanda abin ya faru,daki-daki.cikin jin dadin shi gashi lbrin baya gundirar shi,hakan baya gajiya daba lbrn. Babu wanda ya katse shi sai da ya kai aya. Abban su mansura yayi gyaran murya sannan yace Maman Bilkisu in dai abin da ya fada haka ne, to wannan abin farin ciki ne da murna, ki kwantar da hankalinki, zan yi waya gidan su mansura yanzu, kuma zan sa a darennan shi mijin mansuran ya bincika min ta hanyar buga waya mu ji gaskiya lamarin, tunda ai Yariman da ake magana kani ne a gurinsa, dole zai San komai, mlm mamman yace, ita dai ta sani ni fa na riga na bada 'ya, ke ko dan wa'yancan sakarkarun matan masu nuna bakin ciki ba kya ware asha daula ba. Mamanmu ta ce, kai dai ka sani kun fi kusa da su. A yau ne kasan sakarkaru ne? Umman mansura dariya ma ya bata,a ranta tace, namiji kenan.

Lalubawar farko Abba ya samu farooq, lokacin yana kwance ya dora 'yar bebynsu sa'adatu a kirji, Mansura ta saka kanta a cinyoyinshi, ya dauki wayar ya duba.yace, kai Abba ne ya tashi zaune tare da dora babyn akan katifa, yace salamu alaikum, Abba ina yini? Suka gaisa. Abba yace, kana da lbrin Yarima dan uwanka zai yi aure? Farooq yace Aa ai baya nan ma.Abba yace, to yi waya ka min bincike yanzu-yanzu, farooq yace, to Mansura da ta tsura mishi idanu tace, meyace? Ya daga mata hannu, inda zuwa, layin magajin Malam ya nema yasan shi ne zai San komai, bayan sun gaisa ya ce magaji shin gaske ne Yarima zai yi aure? Magajin Malam yace, haka ne, har ma an bashi matar a Zaria, kawar matar ka ko? Cike da mamaki yace, Oh dama Bilkisu CE? Magajin Malam yace ita CE mana, yanzu haka an biya sadaki farooq yace, Yarima ya sani? Aa in ji magaji, bai ma san za ai masa aure ba, kuma mai martaba yace kada a sanar dashi. Farooq yace shi kenan, mun gode. Ya kira Abban Mansura yace eh Abba zai yi aure wai Bilkisu ce ma, Abba yace, to shikenan, ina so tunda gobe Sunday kana gida ka zo min da Bilkisun, amma kada kace mata komai ko ta sani? Farooq yace Aa yace kar ka sanar da ita sai kun zo. Ya kashe wayar.....
[8:48AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 36🏵

Cike da mamaki farooq ya zuba ma waya idanu, Mansura a tsorace ta zaro idanu itama, tana kallon shi tare da cewa, wai menene Baban dady? Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce wai Yarima ne zai yi aure. Ta dan ja tsaki, to in Yarima zai yi aure me ya kawo Abba ciki? Ni wlh har na tsorata, zatona babu lfy ne,.Yace. Aa to kin San wadda Yariman zai aura ne? Ta sake zaro idanu tace wa? Yace Bilkisunki ta nan gidan.. Mansura ta mike Bil..... Wa? Yace, Bilkisu. Ta kuma dafa kirji in ji wa? Yace, gashi yanzun na kira magajin Malam ya tabbatar min har an biya sadaki! Sai dai wata tsiyar, shima Yariman bai sani ba, yanzun haka bai ma San za ai masa aure ba, itama nan gashi bata sani ba. Amma Abbanku yace gobe muje kada ki nuna mata kin San komai. Mansura taja tsaki, gaskiya ban so mata Auren Yariman nan mai zafin kai ba, farooq yace, ni ko na mata murna, domin Yarima yana da halin girma irin na gadon gidan su abin da ya faru tsakaninsu wannan shedanne . da zaran sun zauna zama na Auren sunna za su sasanta Kansu, kuma za ya kula da ita. Mansu tace, Allah yasa.
Chapter 22 · 0% Book details