Sashe 53
Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Duk wannan satin Bily rigima takeyi ita tana son taje Zaria,ta jima tana naci yana cewa son bai saba da iska ba,baya so a debo masa sanyi,ta hakura amma yau ta tada daru. kallonta kawai yakeyi duk taki cin abinci yanzun ma da zasu kwanta sai ta saka kanta gurin kafafunsa komai tayi sai yaji birgesa takeyi,ya tashi zaune yanzu beauty ba zaki ci abinci ba?Ta tashi zaune tana shasshekar kuka,don Allah yaya zanyi in iya cin abinci?Ni dai in kana son inci ne sai dai inka yarda inje inga mahaifana. sun jima suna son ganina kuma su suna min kara ne irin na ‘yar fari bazasu iya zuwa gidana ba,sai yaji tausayinta yace to naji zakije,amma shine kika juya min baya,alhalin kin san na tsani hakan ko?Ta fada jikinsa to yi hakuri yaushe zan je?Yace jibi amma kwana nawa zakiyi?Tace sati ya zaro idanu,to wallahi a fasa tafiyar,ta kankamesa sorry,to kwana nawa zanyi?Yace zan daure kiyi daya,tace haba dai yaushe muka gaisa?Ta turbune fuska ta ja baya,indai daya ne na hakura,yace to naji biyu,tace ina laifin uku don Allah,shima a maneji, yace to naji amma gida nawa zaki bana sonki yawaita fita ana kallonki, tace to ina zanje ma daga fa gidanmu sai gidansu Umman Mansu,sai ko makota sai gidan Mansu din,ya zaro idanu Kaduna?Tace eh,ya girgiza kai ina hauka nike in barki kije Kaduna mutanan da aka ce suna kwace matan aure?Yanayin yanda yayi maganar sai data yi dariya, tace duk ba gaske bane fa ni dai iyakata gidan Mansu,sai kasuw... ya katseta da cewa kasuwa? Tabdijam, ki fasa zuwan ke nan salon kije maza suyi ta kallonki bazan iya ba,tace to shikenan na fasa zuwa kasuwan kaji?Amma fa gobe zanje gidan Umma muyi sallama da kuma Modibbo,yace goben sai da daddare na kaiki.ta shirgi tsaraba ga kudi da Yarima ya jibge mata, sirikanta ma sun hada mata tasu. su Mama sunyi murna da zuwanta, wannan karon ranar data zo tasa babansu ya kira masu aikin gini sukayi mata lissafin kudin da gidan nasu zai ci,fulastan bangon tsakar gida da kuma yin barandar waje tare da siminte bangon waje,Nan ta cire kudin ta bada ga abinci lodi-lodi sannan tabawa Umman Mansu kudi in an gama gyaran ta siyawa Mama kayan daki.itama ta bata nata.su Ladiyo duk sun zama ababen tausayi, suma ta basu kudi dama kowace bashi yayi mata kanta,nan sukayi ta godiya,da dare tana kwance Umma tana shafa‘i da wuturi,Yarima ya kirata yace waton yau an sami Mama an manta dani ko?Ta dan dubi gefen Mama,sannan ahankali tace,haba nawa komai na keyi kana raina,ban manta da kai ba,shine kaima kaki ka kirani yace ina sane na zata zaki kirani ne,tace to ya aiki? Yace lafia ina son dina?Tace gashi nan kusa dani yana bacci yace Mama fa?Tace gata can tana sallah,yace a‘a kice ba hira to bari muyi text to tace ina jira.sai ga Yarima yana kwance ya dage yana rubuto ma beauty maganganu masu dadi da nuna kulawa akan mutum, itama tana bashi amsa.Mama ta idar sai Bily ta ari bakin Yarima tace Mama ya kira ku gaisa kina sallah,yace yana gaisheki,tace ina amsawa haka sukayi ta text har nisan dare.kafin suka hakura.dangi da makota sun san Bily tazo,dan kuwa sun sha tsaraba,washegari kuma Kaduna ta diba zuwan bazata ta yiwa Mansu,sai da suka zo kofar gidan ta kira wayar Mansu tace Mansu kina gida?Tace ina zani Bily,menene?To ki fito kisa abude mana gate. Mansu tace bana son wasa fa,na taba maki wannan wasan?Inji Bily,ta fito da gudu tana kiran baba maigadi,har ya tsorata tace leka ka gani muna da baki Yana bude kofa sai ga zungureriyar Jeep din Yrm wadda ya bada aka kawosu ciki suna shigowa ana tsayawa ta fito da murna suka rungume juna.Asabe ta fito dauke da son yayinda Atika ta fito da jaka da kuma wayoyi,Bily kenan an zama manyan mata,daga kin ganta kinsan matar manya ce, tayi ‘yar kiba tajin dadi,ga wata gogewa da fatarta tayi, ita kanta tasan tayi. Nan suka shige ciki,hira ta balle labarin daddadan zaman da su Bily sukeyi ne take labarta wa aminiyarta,nan Mansu ta shiga tsokanarta da cewa,da ko kin raina masa wayo ke ya miki yaro,Bily ta rufe mata baki da cewa,yi shiru an daina wannan zancan tuntuni tunda na gane halittarmu ba daya bace. Namiji komai kankantarsa indai ya balaga to namiji yake, suka sa dariya,tace bare nawa gara kowa dashi baya gajiya nan suka koma hirar kayan gyara jiki dana kwalliya.kwana dayan da Bily tayo gidan Mansu tayo guzurin tsarabarta mai yawa tare da shawarwari,itama kuma dama ta cika Mansu da tsaraba da kuma kudi har Mansu taso taji haushi.Bily tace,nasan ba don baki dashi bane na baki don kawai kullum burina in kyautata miki,suka dawo Zaria washegari suka dauki hanyar Bauchi. bayan ta cika iyayanta da kudi. shiko Yarima duk bayan mintuna sai ya kira waya ya kosa yaji tace sun iso gida,tazo da tsarabar su doya ne, dankalin turawa da dai sauransu,tasa aka gyare musu gida ta turare shi da turaren kamshi tayi gayu cikin riga da wando shigar da bata taba yi ba duk da Yarima na son haka, Mansu ce tasa ta lallai ta ringa yi tunda yana so,kuma yanzun babu kalolin matan da ba zai gani ba masu kuma kalolin dressing dama ta gyara kanta ta shiga kitchen ta shirya girki masu dadi koda Yarima ya shigo sasan nasu sai kalolin kamshi suka masa sallama,kan kujera ya ajiye jakarsa ya nufi dakin beauty kwana ukun nan a daddafe yayi su baya son ya dawo idanunsa basu ganta ba,amma me?Yana shiga bata ciki,sai gashi yana ta nemanta,kitchen ne toilet ne ya nufi sasan sa basa can,ya sauko falonsa na kasa ransa ya sosu ya ciro waya yana neman layinta,sai kawai ji yayi an rungume shi ta baya,tace oyoyo nawa!Yayi ajiyar zuciya sannan ya birkitota gabansa tsayawa yayi yana kallonta sannan ya jawota da karfi ya matseta a kirjinsa,kinyi beautyna I love....da sauri ta dago tana kallon bakinsa,shi kansa bai san lokacin daya soma furta kalmar ba,tace da gaske kakeyi? Ya lumshe idanu tare da jan numfashi yace ban sani ba beauty ta kwantar da kanta laf cikin kirjinsa sannan tace don Allah ka soni kaji? Shine kawai abinda na rasa a rayuwata. ya dago fuskarta yana kallo tace,tana kallon kwayar idanunsa zuciyata zata so ka,don ta aminta dakai tana girmamaka tana darajaka,kila ma tana tsananin sonka.Ya manneta har sai da ta kasa numfashi,sannan ya nemi bakinta,kukan son ne ya dawo dasu cikin hayyacinsu,ya fadi daga kan kujera inda yake zaune,babansa ne yayi zafin naman cafko sa ya daga shi sama
Haka suke gudanar da rayuwarsu kowa yana kaf-kaf da dan uwansa tare da gudun bata ma dan uwansa Yarima yana zaune cikin office dinsa marasa lafia suna ta shiga da fita kowace mace tafi son ganin doctor Yrm,a cewarsu yasan aikinsa,da yawa sunce in sun gansa kuma ya rubuta musu magani ko yace aiki ne in anyi suna samun salama, wasu ‘yanmatan kuwa son ganinsa ke sa suyi ta ziyarar asibitin,nurses har ma da wasu daga cikin likitocin mata su kan so ko da hira ne ya dinga yi dasu,amma shi sam baya sakin fuska,ko tiyata ce ya shiga yana gamawa yake kame kansa,shiyasa suke shakkar shi tare da ganin girmansa.wata nurse ta shigo da kati ahannunta tace,likita ga Emergency an kawoma doctor Salihu yace akawo maka,ya dago ya dubeta idanunsa cikin farin glass shi me ya hanasa dubata?Tace yace ka fishi sanin wannan matsalar,ya dan taba baki gami da daga kafadu shigo da ita na gani,bai san lokacin daya mike tsaye tare da cewa,oh my God!Ganin yanda fuskar yarinyar yayi caba-caba duk ta lalace da ruwan batir,ya dubi nurse din ita da matar dake tare da mara lafiyar yace,kuje gurin doctor Salihu kuce nace yayi mata abinda ya dace ya bata gado zan dubata inna tashi,kuje dai zan kira phone dinsa.‘yar wani hamshakin dan siyasa ne aka batawa fuska kuma ‘yarsa daya ce shi baya nan ma yana saudi anyi masa waya dai kuma yace zuwa gobe yana kan hanya.kafin Yarima ya shige gida sai daya dubata,tana bukatar aiki ne sai dai akwai karancin kayan aikin a nan kasar,shi yana dasu amma ko fara amfani dasu baiyi ba,domin asibitinsa ya shigo dasu.hankalin mahaifin yarinyar yayi mugun tashi da yaga ‘yar tashi.doctor Salihu ya samu a office yana cewa don Allah ataimaka masa ko nawa ne zai bada ya sani anyi haka ne don kawai abata masa rai a daga masa hankali,Dr. Salihu ya dauke su zuwa office din Dr. Yarima .
[8:42AM, 12/28/2016] â€?+234 814 912 1821â€?: ðŸµMEKE FARUWA 87 ðŸµ