← Book details Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 60

Sashe 47

Meke Faruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yanzun ma da suke karyawa jinsa yake tamkar wata rahamace ke sakko masa cikin jiki,ta hura masa iska da bakinta a fuska,sai ya lumshe manyan idanunsa sannan ya budesu kar akan fuskarta tace ka koshi ne?Gira ya daga mata alamar eh.ta mika tafin hannunta ta sakalo nashi ta hada yatsunta da nasa ta matse gam,dim yayi yana jin wani abu yana ratsasa,shin me yasa kullum jikinsa ya hadu da nata sai yaji tamkar ranar suka fara taba juna?Ya mikar da ita tsaye ya zagayo da ita inda yake kan cinyarsa ya dorata, sannan yace jikina ya shaku da naki,tace nima haka har na soma tunanin inka tafi course dinka yaya zanyi?Ta tsura ma fuskarsa idanu,yayi murmushi zanso muje tare,me yasa bamu saba ba alokacin zamanmu a Malesia?Tace kaine kaja sai kayi ta kawo mata bayan gani, yace in kawo su ko su kawo kansu?Kema da kina kawo kanki da mun saba,tace nazo ka min wulakanci ai to mubar wannan zancan,anjima zamu je ki gyara gashinki ko?Nima ina son yin aski duk nayi muni,ta dubesa ni ko bana ganin muninka,ya kwanto da ita kan kafadarsa saboda me?Tace saboda kana da kyau,yayi murmushi. Sallamar Magaji ce kusa dasu tasa suka daga kai yace,tun a bakin kofa nake zuga sallama anyi min shiru,Bily ta soma kokarin silalewa daga jikinsa,ya riketa yana cewa,wane kauyanci kenan?Magaji bakonki ne?Magaji yace yi zamanki,in Allah yaso muma mun kusa shiga wannan ajin. Sunne kai tayi ga kunyar kayan jikinta,gata ganinta da yayi jikin Yarima. magana sukayi akan dinner din ya tafi yana cewa to gimbiya nina wuce tunda yau kam ko gaisuwa babu. Yarima ya mike zo muje daki ki dan danna min bayana,tace da mun gaida Umma mun dawo ko?Ki bari koda yaushe ne ma gaisa,ya zura hannunsa cikin rigarta yana matsar na shanunta tace toh muje. Bikin Magaji ya kacame ranar daurin aure aka kawo amarya,su Mansu kirjin biki,dakin Bily ta yada zango har dasu auta Asma‘u ta biyo Mansu. ranar kuwa aka yi dinner Mansu tayi musu dinkin kayan da zasu saka ita da Bily,da suka shirya gaskiya sun hadu,Mansu ta kalli Bily tace,sai kace kece amarya?Kin tsaru fa. Yarima yana falonsa sun gama shirinsu ya soma kiran layin Beauty kamar yanda ya rubuta cikin wayarsa,amma sai yaji wayar tana ringing nan kusa dashi,ya dauko wayar ya duba sai yaga tasa Sweetheart.ya tsura ma sunan idanu,da gaske ne shi sweetheart dinta ne?Sai kuma ya samu kansa da jin dadin hakan,ya dubi Magaji kaga ita wannan ma anan tabar wayar tata,ina son ince suyi sauri donni bana cikin tsarin nan na African time. Magaji yace hakane, sai gata ma ta shigo, shagala Yarima yayi da kallonta,tayi kyau cikin riga da siket din na wani yadi golden mai walkiya dinkin ya fito da surarta tsan-tsan ga kuma net da aka nada shi dan daidai,takalmi mai tsini ne Magaji yace,gaskiya Bily kada fa kufi amaryata kyau,tunda Yarima yake sai yau yaji ya taba jin kishin mace a ransa, domin ji yayi baya son kallon da Magaji yake yiwa Bily,don haka sai yace,me yakai idanunka kan adon matata?Fita ka jirani ina zuwa, Magaji ya fita yana dariya tare da jin dadin yanda ‘yan kwanakin nan abokin nasa ya soma hawa kan layi. Yarima ya dubeta ina ta kiran waya ashe ma nan kika barta,tace eh wallahi mun gama shirin.ya sake kallonta sama da kasa,tayi murmushi nayi?Kai ya daga kawai, sannan yace muje tace bari in dauko jakata in sanar da Mansu taje ta fito da amarya. Mota daya suka shiga da amarya su Yarima kuma da ango,sun riga zuwa sannan amaren suka iso,shi Yarima sai ya samu kansa da zare idanu yaga ta inda Beauty zata bullo domin kwalliyar datayi yana ganin kallonta kawai mazan gurin zasuyi,ita ko tunda suka rako amarya sai suka koma gefe ita da Mansu suna labarin kayan harka tana ce mata sai in mun natsu zan baki ai naga acan keda Yarima naki,tace wallahi wani sa‘in in kin gammu zaki zata tun dama can mu masoya ne,Mansu tace,zama kuso juna ne,Bily tace ina ai nayi rashin wannan kalmar har abada,bazan taba samun mai sona ba wanda zai dubeni yace,Bily ina sonki.wannan tunanin ma tuni na ciresa cikin raina,tunda na riga nayi aure,mijin kuma bawai yana sona bane bare ya dinga gaya min.Mansu tace ke wata rana zai so ki ne.
[8:33AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 77🏵

Bily tace ban yarda ba,nida shi zaya yi wuya mu so juna,don Hausawa suna cewa in mutum yaki ka da safe sannan da yamma yazo yace yana sonka wallahi karya ne, kuma Yarima bashi da rufi yana gaya min cewa yanda ba so nake ba akayi aurenmu shima haka ne bawai yana sona bane, nidai zaman lafiyan da mukeyi ne yanzun yayi min.suna ta zuba basu sanshi can Yarima ya shiga rudanin rashin ganinta ba,don haka ya ciro wayarsa ya shiga neman layinta zuciyarsa kuma tana raya masa cewa kilama wani namijin ne ya kirata.abinda bai taba yiwa wata mace ba shine ya kirata fiye da daya don inya kirata mace sau daya bata amsa kiran ba ko da bata gani bane to yabar kara kiranta amma yau kira harna biyar,wayar tana cikin jaka batama sani ba sai ana biyar din ne ta an kare da vibration din da takeji,tana ciro wayar call din na yankewa,5 missed calls ta gani,ta dubi Mansu, Yarima na nemana bari naje.Mansu tace nasan tare zaku zauna ni bari mu zauna dasu auta,Bily tace Faruk ya gudu ana gama daurin aure tace shima dole ne kinsan yanayin aikinsu,Bily ta nufi gurin Yarima wanda zuwa lokacin ya cika yayi dam,koda tazo ta zauna bai ko kalleta ba,ta dubesa sai ta samu kanta da shakkarsa,tace gani ya mata banza tace,ina fa tare da Mansu ce,sai ma ya kalli gurin Magaji yana cewa gasu Shettima can da Yakubu Sunusi dama sunzo ne?Yace eh sunzo bamu hadu dasu bane mun daiyi magana ta waya,jin suna hirar abokansu sai taja bakinta tayi gum nan dai guri ya kacame,masu ciye-ciye nayi masu shaye-shaye nayi shiko Yarima sarkin kalkali ana ta faman shan kamshi sai dai zuciyarsa taki nutsuwa,gani yakeyi kusan duk mazan gurin beauty suke kallo,don haka duk sai yaji zaman gurin ya ishe shi. lokacin da amarya da ango suka fita domin yiwa masu waka liki nan Yarima ya tashi yana yiwa amininsa ruwan ‘yan dubu- dubu, Sumayya kuwa sai ta soma zuba ma Yarima Magaji da Bily sun san dalilinta na yiwa Yarima liki amma shi bai san ko me take nufi ba. Ita Bily ta shigo tana ma ango da amarya liki sai Yarima ya juyo yace fita tace liki fa nake amarya da ango yace ibada ne ko kuwa tazo fita kawai wani ya biyota yana mata liki har wurin zaman ta ai kau ta tsorata ta juyo tace kai malam lafiya ni fa matar aure ce yayi murmushi yace nima ai mijin aure ne sai tayi banza dashi Yarima kau ashe ya ga abun da ya faru rai bace idanunsa har da canja kala kawai ya fita daga hall din billy.tayi sauri ta bishi amma ina tana zuwa har yayi reverse ya ja motar da wani matsiyacin gudu ta dawo wurin Mansu tace na shiga uku Mansu Yarima yayi fushi nasan kan na shawo kan sa sai naji jiki Mansu tace ki kwantar da hankalinki mu koma gida haka dai har aka tashi hankalin ta baya kwance suna isa gida Mansu tace taje wurinshi ta lallame shi tace nifa tsoro nake ji ko in bari dai sai ya huce
[8:36AM, 12/28/2016] �+234 814 912 1821�: 🏵MEKE FARUWA 78🏵
Chapter 47 · 0% Book details