← Book details Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 43

Sashe 42

Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Yi yayi kamar beji abinda take faɗa ba ,ya kalli Rufee yace " haba Rufaida me kikeyi haka ai zakisa yarinya ta rainaki , kinsani dai ni nace zan aure ki kuma kina raina yanzu haka ma ina zancen zuwa na ganki ne se gaki kin shigo " wai ya faɗa haka ne saboda Meerah taji haushi ,ita kuma da yake tana da wayo se ta matso wurin su da murmushi a fuskan ta tace " to kinji dai ke Amarya yanzu ki tafi idan ya gama da uwar gida ze zo ya sameki, ni bazan lamunci ku tsaya min a gida kuna zance da sunan soyayya ba da wannan rashin kunya ne , bayan jiya da kansa ya gama faɗar ji yakeyi kamar mu kasance mu biyu kawai shi zece ya fasa auren ki ni ce na ce ba'a haka saɓa alƙawari babu kyau tunda kin saka ma ranki wahalar auren mijin wata ya daure ya auro ki "wani lafiyayyan mari Rufee ta nufi fuskan Meerah ,da sauri tayi tsalle ta ƙankame Mu'aiseen ta kaucewa marin " cikin kuka Rufee tace " nayi nadamar sanin ki a rayuwa ta kuma kisani idan ma asiri kikayi ya aure ki wlh zan ƙaryasa , dan nasan haka kawai baze ce yana sonki ba yaushe ma ya sanki na tabbata Yaya baze so ki ba ,wato kinzo aiki a gidan mu shine ganin kudi kukakayi ƙulle² keda talakawan iyayen ki kuka aure mijina ko to wlh baze yiyu ba ,se kin bar gidan nan kijirani kuma " a fusace ta fita daga sa sashen wata iriyar dariya Amrah ta fashe da ita ,tsawa , Mu'aiseen ya daka mata yace ita ma ta fice ,sum-sum ta wuce zata fita seda ta kai bakin ƙofa ta jiyo hannu ta ɗagawa Meerah alamar jinjina ,tafi ce da gudu_

_Meerah na ganin _Amrah ta fita ya rage daga ita se shi ,ga ya ɗaure fuska ,se kawai ita ma ta ɗaure nata ,raɓa shi tayi ta shiga kitchen basket din da Amrah ta kawo ta duba kaɗan ta zuba irishi din da soyayyen ƙwai ,de tea da ta haɗa cikin ƙaramin cup ,komawa tayi tsakiyar falon ta miƙe ƙafa ta fara cin abincin ta kamar bata san dashi a wurin ba " ke wace irin yarinya ce da bakida kunya a gaban ƙannena ki tsaya kina furta banzayen kalamanki ƙara ma da ke har kisan wannan? Aje cup din da ke hannun ta tayi tace '' haba da ni ƙarama ce ai baxan kwana gidan miji ba rashin kunya kuma kadan a ghetto aka ɗaukoni" tana gama faɗar haka taci gaba da shan tean ta " ok ashe fa kin girma shiyasa aka kawoki gidan aure ,bara na gwada yanayin girman naki" batayi aune ba se jin ya dagata sama tayi ya nufi bedroom ɗinsu da ita ,wutsil² tafarayi amma yaƙi aje ta ,har se da ya shiga ɗakin da ita kan gado ya jefa ta ,yabita ya danne "yau zanga irin balagar da ke sakaki hayaƙin kai ba ke mara kunya ba? Ture shi ta fara yi daga jikinta amma ko motsi beyi ba ,sema kiciniyar zare belt din sa da ya fara " wayyo Allah me kakeyi haka dan haka Kayi haƙuri nifa wlh wasa nakeyi duk abinda nafaɗa " ƙarya kikeyi idan baki sani ba ai baxaki faɗa ba ,bansan cewar ai babbar yarinya na aura ba seda kika faɗa saboda haka haukar da kikace nayi a daren jiya itace zanyi yanzu " wayyo Allah na Ammi zeci amanar da kika bashi ni wlh ka ɗagani kaje can wurin wacce ke son ka ka nuna mata bani ba "zuuuu taji ya zuge zip din dake gaban rigarta ,wani irin ihu ta zabga tare da kai masa cizo a damtsen hannu ,wanda hakan ya saka shi sakinta babu shiri da sauri ta mirgina ta sauka daga gadon ta faɗa toilet ta danna key_

" _Ashe ƙaryar rashin kunya kikeyi ,wlh matukar baki saita bakin ki ba zakisha wuya ,yanzu zan fita naje na baiwa Babyna haƙuri da kika da ranta ya ɓaci a abanza ,kuma ki shirya duk hukuncin da ta yanke kanki ,ke kika so babu abinda zance mata " daga cikin toilet ɗin ta ja tsaki "mtswwww wannan kuma kai ya shafa ,ba ni ba daga kai har ita wacce kake kira masoyi yar ka bana tsoron ku wlh ,zanyi rayuwa ta cikin ƴanci dan baze yiyu ka hana me sona aure na ba kaikuma kazo nan kana ƙunta tani idan ka gadama yau katafi wurinta ka kwana duka ɗaya amma baze yiyu kuzo nan cikin gidana kuna min iskanci ba , salon ku ɓatamin tarbiyya "wato ke dai bakin ki baze mutu ba ko? Zanyi maganin ki ne kijira na dawo " ka dawo lafiya duk abinda kake tunani na wuce nan Ni ba kasarya bace ,katafi ka aure ta_ ban damu ba_

_Dama itace dai²da kai kaga se kuriƙa haifawa Hajia Sauda haja tana tallata muku_

_Shiru _Mu'aiseen yayi jin abinda ta faɗa ,tabbas akwai abinda yarinyar ta sani a game da Sauda ,dama shi tunda yafara ganinta gidan zuciyarsa ke zarginta idan hakane kuwa na babba da yaro xe yi mata har ya gane dalilin zuwanta gidansu_

Comments and share

#Real@Bazamfaria❤️
*MABARACIYA*

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى*  *ASSɷ📚✍**
  _{Onward Together}_

_STORY AND WRITTEN_
                  _BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////

🅿3️⃣7️⃣

_Kuyi haƙuri da typing errors zan iya yin typing amma baxan iya editing ba yana bani wuya_

Da kuka Rufee ta koma sashen su ,sosai hankalin " Mene ne Rufaida daga ina kike? Wani irin kallo tayiwa Hajia Sauda cike da baƙin cikin abun da suka aikata mata tace " Mama na fara shakka a kan ƙaunar da kike confessing cewar kina min wannan ita ce saka makon ƙaunar ,kinyi fatali da cikar burina burin ko wace uwa ta aurar da ƴarta amma me yasa ni tawa uwar ta nemi watse nawa auren? The worst pain ma abun da kikayi ya saka Mu'aiseen aurar Yarinyar da duk duniya babu wacce na tsana kamarta yarinyar da ta zauna a matsayin codmade ɗina yau ita ce ta auri wanda na daɗe ina mafalkin mallaka , yarinyar da nake zagi na sakata aiki a duk sadda na gadama yau ita ce ta zageni a gaban idona ta faɗa min maga yadda ta gadama kuma na kasa ɗaukar mataki ,me kika aikata min haka Mama?

" Rufaida ki natsu kimun bayani yadda zan fahimta ,me kike nufi Mu'aiseen ɗin wa aka aura masa? " Mama yarinyar da na ɗauka aiki a gidan nan shin kinsan dalilin kawota gidan nan da nayi? Saboda ta nemi ta haɗa kanta da ni ne shiyasa nace zan nuna mata tazarar da ke tsakanin talaka da me kuɗi se gashi da ga ƙarshe an aurawa Mu'aiseen ita saboda banzan dalilin ki " innalillahi wai wace yarinya kike nufi badai Aminatu ba? Banda lokacin rike sunan ta amma idan haka ta sanar dake to ita , Rumaisa ma tayi aure ,yanzu ni kaɗai ce a gidan nan ,taya zan yarda cewar kina sona?

"Ya akayi hakan ya faru? Tabbas ko ma menene ,Zainabu ce muna fuka tun ranar da aka sanar dani tafita tare da yarinyar jikina ya bani akwai abinda take ƙullawa " wayarta ta fitar ta kira Hajia Laura, dan ita ta bar gidan tun daga lokacin da Rufaida tayi bacci dan ta san dole ne Rufee zata zargeta ga kuma akwai shirin da take yi ta yadda Rufee zata zo hannun ta , ringing ɗaya ta ɗaga " Hajia ina zancen ki a raina se ga kiranki " kallon Rufee da ta tsure ta da ido Sauda tayi ,se ta nufi ɗaki saboda wannan wayar sirri ce ,seda ta rufe ɗakin tukuna tace " Hajia a kwai matsala fa anyi mana kutse ga jahar mu ,duk wani ƙudurina ya rushe "bangane ba Hajia wace hajar kike nufi ? Hajia ina yarinya Amina da muke ƙoƙarin tafiya Niger da ita? To muna fukar matar nan tayi amfani da damar da muka bari na fasa auren Rufaida ,ta aurawa Mu'aiseen ita"hajia Laura da ke a zaune bata san lokacin da ta tashi tsaye ba "Hajia ko ta san shirinmun ne game da yarinyar? " Kai ina bana tunanin haka ban bar kafar da wani xe iya zargina ba a kaf garin nan , nasan dai zatayi haka ne saboda huce takaici Kinga yarinyar ƴar talakawa ce dole zasu amince su bada auren ta a ganin su wani nauyin ne zasu rage , lallai kuwa a kwai matsala ya kamata mu kashe auren nan sedai ban san ta wane hanya bane " Hajiya zamu iya amfani da Rufaida a kashe auren yanzu dai na fita ne kijira ni zan dawo karkiyi magana da Rufaida har se na zo ni nadan abinda zan faɗa mata".

Rumaisa

Tun daga yanayin tarbar da matar Muhsin tayi musu ta san cewar da matsala ,ka san cewar gidan nasu upstairs ne ita matar itace a ƙasa ita kuma sama shi yasa da aka kawo ta seda aka ajiye ta sa shen uwar gidan domin a damƙa amanar ta a gareta ,budar bakin ta tace ,ita bazata iya ɗaukar amana ba domin wuya ne da ita abu ɗaya da ta sani shine kowa ya zauna da halin sa wannan abunne ya tabbatar musu da bazatayi kirki ba

Dan haka sosai su Hajia Inno suka bata shawara akan ta kama kanta tun da ma Allah yasa ba wani zama bane zasuyi tare ,idan sun daɗe ma befi suyi 2 weeks ba ,da ganan sukayi mata salla ma su ka barta daga ita se halinta , kifewa tayi ta ci gaba da risgar kukan ta ba su wani daɗe da fita ba angon ya shigo
Chapter 42 · 0% Book details