← Book details Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 43

Sashe 36

Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Knocking Amrah ta fara seda ta dauki kusan minti biyar a tsaye ganin ko motsin sa bataji ba se ta tura ƙofar ta shiga ,duhune a falon kasancewar duka windows din a rufe suke ,seda ta laluba ta kunna switch kafin haske ya bayyana ,da ido ta bi falon kulolin abincin da aka kawo masa ,tun jiya suna ajiye da alama ko buɗewa beyi ba ,mamakine ya kamata " to ko dai be kwana a gidan bane ,Ammi ce bata sani ba? ganin batada tabbaci se ta nufi bedroom dinsa , shima babu haske seda ta kunna ,dube²ta fara yi can ta hango shi cikin bargo da sauri ta nufi gadon ta yaye bargon wani irin hucin zafi ne taji ya bugi fuskanta " Subhanallah Yaya bakada lafiya ne? me yake da mun ka kasha magani? duk da halin da yake ciki seda ya ɗan murmusa ,saboda ganin shirmen da Amrah keyi se jera masa tambayoyi takeyi bayan duk wanda ya ganshi yasan cewar beda lafiya amma ita tambaya ba adadi a lokaci ɗaya ,dama Rumaisa ce zata iya te makon sa dan tafi Amrah hankali ,ganin zata sauka daga kan gadon ya saka shi riƙo hannun ta ,cike da ƙarfin hali yace " don't inform Ammi just call me Rumaisa" bata ma gama sauraren shi ba tafincike hannun ta ta fita lokacin har hawaye sun fara bin fuskanta ,tana shiga falon Ammi mutane suka fara binta da ido ,ita ma kallon su takeyi ga hawaye a fuskanta sedai batayi magana ba " ke wane irin iskanci ne zaki shigo mana ido da hawaye kina binmu da kallo kamar wasu baƙin ki lafiya? Hajia Inno ta faɗa (yayar Dady) tana harar Amrah ,kasan cewar ta mace mafaɗa ciya ,turo baki Amrah tayi tace " Goggo ni Ammi nake nema "ai se kishiga ciki kiduba ba ki tsare mu da shegun idonki da kikayi gado ga dangin ubanki ,Duda ya rasu kinja masa zagi" dariya dai mutanen da ke wurin sukayi ,dan kowa yasan jarabar Inno ,ita dai Amrah batabi ta kanta ba ta tafi neman Ammi.

Waya ta sameta ta nayi ,ganin yanayin ta yasaka Ammi sallama da wacce take wayar ta maida hankalinta ga Amrah "Me ya faru keda na tura kidubamin Yayanku kindawo kina kuka har kinsani faduwar gaba me ya faru? "Ammi Yaya beda lafiya sosai kuma shine yace kar na faɗa miki wai na kira Rumaisa ,kuma nasan ita ta wuce school".

ko gama sauraren ta Ammi batayi ba tace " tashi mu tafi ,ganin fitowar su ne yasaka Umma magana tace wai me ke faruwa ne ta shigo tana kuka ke kuma kinfito hankali a tashe? Batare da Ammi ta tsaya ba tace " ina zuwa Yayansu ne babu lafiya "Umma najin haka ta koma ta zauna dan tasan yanzu haka ba wani ciwo bane kawai rundune irin na Ammi indai abu akan Mu'aiseen ne to fa babu zama ,sauran ƴan'uwanne sukayi masa fatan samun lafiya ,Inno kuwa taɓe baki tayi tace " shi keyiwa amaryar tasa jinya kenan dan ita naga har wa ni rawan ƙafa takeyi jiya na ga shigowar ta gidan nan amma da yake Saude batada mutunci tasan munzo shine takasa turo ƴarta ta gaishe mu ,Allah dai ya kyauta ,ni banso aka haɗa yaron nan da ƴarta ba naso nayi ƙorafi se ga naga ita Zainabu ma tayi murna da hakan shiyasa na kawo ba gani na saka musu dahuwar mutum dai me ƙwassai" babu dai wanda ya tanka ta har ta ƙarashi surutun ta.

Sosai halin da Ammi ta samu Mu'aiseen ya daga mata hankali , toilet ta shiga da kanta ta debo ruwa ta dauko towel ,ta fara goge masa jiki saboda zafin jikin sa yayi yawa ,yanajin duk abunda takeyi masa sedai yama kasa buɗe idon sa ,saboda saran da kansa keyi na azabar ciwo ,tura Amrah tayi ta haɗo mata tea ta kawo mata ,batayi masa magana ba dan ta san halinsa da shegen musun tsiya ,dan haka tafara kiciniyar tada shi ya zauna ,yunƙurawa yayi ya ɗan jingina bayansa da gadon ,bayajin shan tea amma saboda Ammi haka ya daure tama bashi ya ma karba seda yadan sha babu lefi ,kafin ta ajiye cup din ta duba side drower din ta ɗauko magani ta bashi yasha ,gyara masa kwanciya tayi tana rufa masa bedsheet din tace " kayi bacci idan ka tashi zamuyi magana " kai kawai ya iya ɗaga mata ,yana jinsu har suka fita ɗakin ta ja masa ƙofa .

Buɗe idon sa yayi a ransa yana jinjina soyayyar dake tsakanin shi da Ammi be taba jin cewar ba ita bace ta haifesa hasalima shakuwar da ke tsakaninsu babu ita tsakanin sa da Umma ,yanzu da wata uwar ce bazata kula da halin da yake ciki ba kawai tambayoyi zata fara yi masa akan me ya faru amma ita ta barshi har ya samu relief ,haka yayita tunani har bacci yayi nasarar ɗauke shi.

Ammi tana komawa sashen ta ta nemi ganawa da Umma ,su biyu suka keɓe a ɗakin ,ta kora wa Umma bayanin komai ,duk da Umma ta tausaya wa ɗan nata sedai bata goyi bayan shawarar da Ammi ta kawo a matsayin mafita ba " kiyi tunani da kyau Umma nasan Alh ze fahimce ni ,banason wani abu ya samu Mu'aiseen idan na bari hakan ya faru bazan taɓa yafewa kaina ba ,domin tun farko ya bayyana min ra'ayin sa game da ita " a'a Zainabu yin hakan kuma kamar mun so kanmu ne da yawa ita yarinyar tana son sa ne? bamuda wannan tabbacin " shi kansa wanda za'a batan ai ba son sa takeyi ba" duk da haka Zainab haramun ne neman auren cikin aure saboda farincin namu yaran be kamata mu tauye na wasu ba " wlh Umma duk wannan ba kawai saboda Mu'aiseen nakeyi ba har ita kanta yarinyar ,ina son ta kamar yadda nakeso Rumaisa kuma a shirye nake da na fanshe ta da Rumaisa" zare ido Umma tayi cike da mamakin abun da Ammi tace " taya zaki wannan gaskiya abun naki na neman zarta tunani taya zaki ƙuntata Amrah saboda shi ,a rayuwa kowa ya sani akwai nasara akwai faɗuwa saboda haka kibar wannan a matsayin ƙaddarar sa ko ba da haka ba ma bana tunanin ɗanki ze iya riƙe mata biyu kuma hakan kamar wani sabuwar fitinar ne zamu tono tsakanin mu da Saudah ,abar zancen auren nan kawai "

Ganin dai Umma bazata fahimce ta bane se kawai ta shareta kamar ta bar zancen

Sedai ta yi musu sallama cewar zata fita amma ba jimawa zatayi ba zata dawo ,tabarwa Amrah saƙon cewar tarikayi tana dubo Mu'aiseen idan ya tashi ta kai masa abinci ace yaci inji ta zata dawo masa da albishir din da ze saka shi farinciki

Ba ita ta dawo gidan ba se goshin Magrib ,duk da tana cikin damuwa amma bata bari su Hajia Inno sun gane hakan ba seda tayi sallar isha'i ta gama kafin ta ɗaga waya ta kira Rumaisa tace ta sameta ɗakinta yanzu kuma tazo ita kaɗai ,babu ɓata lokaci kuwa Rumaisa ta xo

Tashin hankalin da ta gani cikin idon Ammi yasaka nata hankalin tashi ita ma " Ammi wai me yake faruwa ne Yaya jikin sa yayi tsanani ko tashi baya iya yi kuma ya hana akaishi hospital ,sedai doctor yazo gida daƙyar ya bari aka saka masa drip"

Na sani Rumaisa ,shine dalilin kiranki da nayi yanzu , Rumaisa bansani ba ko zaki iya yimun wannan temakon ba duk da nasan cewar ke ɗin me biyayya ce kina son farincina idan har haka ne to ki amshi maganar da za faɗa miki ina me tabbatar Miki Allah ze duba sadaukarwar ki da biyayyar da kikayi min ,baxaki taɓa nadama ba ki temakeni Dan girman Allah"Ammi ta kara sa tana haɗa hannun ta ,rawa jikin Rumaisa ya fara ,duk da Ammi bata sanar da ita alfarmar da ta ke so tayi mata ba to ta tabbata al'amarin me girma ne ,fashewa tayi da kuka tana janye hannun Ammi daga rokon da takeyi mata ,cikin kuka tace " Ammi ni ce kike roƙo haka saboda wani buƙata kamar ba ƴar da kika haifa da cikin ki ba ,miye amfanin mu ƴaƴa idan bamu share muku hawaye ba a matsayin iyayenmu da su ka sha wahala akan mu ba , be kamata ki tsaya roƙon kafin ki zarta hukunci a kaina ba ,kamata yayi ki kirani kice ,kin yanke hukunci kaza akaina ,Ni kuma me biyayya ce a gare ki Ammi ,me kike so nayi Miki?

"Allah yayi miki albarka Rumaisa yabaki yaran da za su ji ƙanki kamar yadda kika amince zakiyi min biyayya ba tare da kinsan hukuncin da na zartar ba ,na bada auren ki ba tare da naji ra'ayin ki ba kuma za'a daura auren ne nan da kwana biyu rana ɗaya da na yayanki kenan " matukar girgiza Rumaisa ta girgiza da kalaman Ammi "innalillahi wa'inna ilaihiraji'un"take maimaita cikin ranta "wannann wace irin ƙaddara ce ta kusan to ta to wa Ammi ta baiwa auren ta? Baxaki amince ba ko Rumaisa? Maganar Ammi ta sake shiga kunnen ta ,da sauri ta girgiza kai " na amince Ammi "to baki tambaya waye mijin ba? Na tabbatar da mahaifiya irinki bazata taɓa yiwa ƴarta zaɓin tumin dare ba ,nasan cancantar sa yasa kika amince da zaki bashi ni ,a yanzu banason nasan ko waye Ammi na amince da auren sa ki tayani da addu'a hakan ya zamo Alkhairi a gareni" rungumeta Ammi tayi tana shi yi mata albarka ,nan take zazzaɓi ne zafi ya rufeta ita ma kwantar da ita Ammi tayi kan gado ta tofa mata addu'a tace ,ta yi bacci.
Chapter 36 · 0% Book details